Chapter 45
Chapter 45
yace “Ashe yau za asha ihu kenan” Dariya dukkansu suka yi, sannan ya dago ya kalli Huda.. Three quarter riga mai fad’i ce a jikinta wadda ta wuce mata har gaba da guiwowinta peach colour, sai pencil trouser white, ta yi mopling da white vail, sai y’ar k’aramar white bag d’inta. Kwalli kad’ai ne a idonta sai d’an pink d’in jam baki data shafa amman tayi masifar kyau! A ranshi yace “Yarinyar akwai kyau kamar aljana” sai dai shi ko sau d’aya bata tab’a burgeshi ba, asalima shi haushin ta yake ji! Ko dan ita tayi sanadiyyar zuwan su Mom da Mammy cell ne, oho! Duk da ba wani shiri yake yi da Mom d’in tashi ba amman yayi mugun jin zafin abunda aka yi musu ata dalilin y’ar k’aramar Yarinya. Gyaran muryar da Abba yayi ne ya katse mishi tunani.. Bai ma lura da shi ba, sai yanzun. “Abba ashe kana nan.” Ya fad’a yana d’an murmushi. A b’angaren Abba kuwa yanda yaga ya kafe mishi y’a da ido ne ya sanya yaji kamar yace su fasa fitar! Ajiyar zuciya ya sauk’e yayi saurin kawar da tunanin daga zuciyarshi, sannan ya sake kallon Auwal d’in yace “Kallo d’aya tak! Duk wani mai isheshen hankali zai yi maka ya fara yi maka zargin gudowa kayi daga gidan mahaukata!!Kalli wandon ka kamar wanda aka yi maka gorin kaya, kalla nan” Abban ya mik’e yana nuna mishi wandon da hannunsa kafin yace “har cinyarka ana iya hangowa! Wannan d’an iskan askin shi kuma an hanaka amman naga abun naka gaba yake yi dan na yau ma yafi na kullum! Sai kace wani zakara. Harda sark’a a hannu!! Wai ni auwal mai kake son ka zama ne? Eh??” Yayi mishi tambayar cikin b’acin rai, bai jira jin amsar shi ba yace “Wallahi ka tabbar ka seseta wannan d’an iskan askin kafin ku dawo gidannan inba hakaba kowa sai ya ji kanmu!” Yana gama fad’in haka yayi hanyar sama ranshi a b’ace… Gaba d’aya In ka kalli Auwal ba zaka tab’a kiranshi da musulmi ba, ba abunda yafi b’ata mishi rai kamar sark’ar hannunshi ya lura harda wata sark’a a wuyanshi wadda ta b’uya a cikin rigar kawai shiru yayi masa dan in yaci gaba da kulashi zuciya zata jashi ya fella mishi mari!! Anyi maganan anyi har an gaji amman saboda ya raina mutane sam bai fasa ba. Auwal kuwa kamar ya had’iye zuciya… Tunda Abba ya fara fad’a ya had’e rai! Ba abunda yafi b’ata mishi rai irin tijarar da Abban yayi mishi a gaban Yara, don haka ya ja hannun Sudais suka fice ba tare da yabi ta kan Hudan ba. Ganin da tayi ranshine a b’ace yasa kawai ta bishi wajen, bata biye sa ba. Sudais yasa a gaba, amman dake Yaron ya fishi hankali yana ganin Hudan ta taho ya bud’e mata motar shi yayi saurin tsallakawa baya. Kamar zai yi magana sai kuma kawai yayi shiru. Ko ida rufe murfin motar bata yi ba ya fige ta da azabar gudu.. Daman masu gadin tun da suka hangoshi ya tada mota suka wangale gate, gudun kar garin saurin bud’ewa idan ya taho yayi gaba da wani! In kuma kayi jinkiri a balbaleka da zage zage! Komin tsufan mutum. Gudu yake shatatawa kamar zai tashi sama.. Hudan duk ta tsure, ta rik’e kujeran da take kai gam! Ta k’ame, yana lura da ita wanda hakan ne ma ya sa ya sake k’arfin gudun nashi. Ikon Allah ne kawai ya kaisu inda za suje, Ita ba sanin munjibur park d’in tayi ba, shiyasa bata gane inda suke ba! “Fito” Yace, yana k’ok’arin bud’e motar ya fita. Sudais ma ya fito daga baya. Tana fitowa tun kafin ta rufe motar gabanta yayi mugun fad’uwa ganin su a police station. Juyowa tayi tana kallonshi wanda zagayowarshi kenan kafin tayi magana yace “Su Mom zan nuna miki, halinda suke ciki all because of you!” Ganin ya tsareta da ido ne yasa ta wucewa jikinta sai karkarwa yake yi. Direct wajen da suke ya nufa, bayan ya amsa gaisuwar police d’in da suka tarar a reception, sannan ya zaunar da Sudais a kan kujerun wajen yace mishi “kar ya kuskura ya tashi, ya jirasu a nan” Da kyar ta iya k’arasawa wajen! Tun daga lokacin jikinta ya mutu, yayi wani irin sanyi… Da kyar ta iya bud’e baki ta gaishesu amman ba wadda ta amsa mata tsakanin Mammy da Mom, Ummi ce wadda take mugun jin jiki ta d’ago da ta kalle ta a hankali tace “Lafiya Alhamdulillah.” Sannan ta komar da kanta k’asa ta kwantar. Wata jakar leda wadda ya shigo da ita yayi saurin mik’a musu, ganin wani police ya taho yasa Mammy tayi saurin b’oyewa a cikin mayafinta , sannan tace “Ka cewa Arshaad inata jiranshi akan maganar mu naji shiru!! Shekaran jiya dana samu waya nayi mishi more than 20 miss calls amman bai d’auka ba k’arshema kashe wayar yayi! Kace nace Dan ubanshi shi nake jira in kuma ba zai iya ba to ya daina kashe mini waya kawai ya fito fili ya fad’a min!!” Hudan kamar tace mata ‘ba kashe wayar yayi ba’ Don tana gani kamar wannan number da tayita kira ranar nan da wayar tana a hannunta ne Mammy take magana akai! Sanann sub’ucewa wayar tayi a hannunta ta fashe…. Amman kuma kawai sai tayi shiru ganin yanda ko inda take Mammyn bata kalla ba. “Muje” taji muryan Auwal. A hankali tace musu “Sai anjima’ Nan ma ba wanda ya kulata sau Ummi dake kwance taga ta d’an d’aga mata kai alamun ok. Suna fita Mom tacewa Mammy “Nifa gaskiya ko Arshaad ya kawo kud’ad’en nan ba inda zan biki mu fita, maybe ma yaudararki police d’in nan yake shirin yi, dan ba miliyan uku ba gani nake ko miliyan arba’in zaki bashi ba lalle ya iya k’etare umarnin Granpa ba! And in ma ya yarda, bakya tunanin irin mummunan hukuncin da shi Granpa d’in zai yanke mana muddin yaji labari?” Murmushin takaici Mammy tayi kafin tace “Adama na gaji da halin mutanen nan! Na kawo wuya! Ke dai kawai kamar yadda na fad’a miki ‘ki zuba min ido’ wuyarta kawai mu fita daga nan, dakanshi shi Granpa d’in zai kira mu mu koma gidajenmu… Shi kuma Yahaya wallahi kinji rantsuwar d’an musulmi ko? Sai na gasa mishi aya a hannu! Wai ace mutumin nan ya dawo amman ban isa yazo ya ganni ba? Hak’uri na ya k’are Adama!Maganar gaskiya na gaji da cin kashin da ake min na gaji!!!” Ta k’arashe maganar tana share kwallar data zubo mata. Matsowa daff da ita Mom tayi tana magana k’asa k’asa gudun kar Ummi taji, tana cewa “To ki kira maman ki mana, ai kina nan ma ita d’in zata iya yi mana komai” Ajiyar zuciya Mammy ta sauk’e kafin tace “Tace babu ruwan ta, ranar dana ari wayar ai har ita na kira kin tafi fitsari lokacin, tace in yi hak’uri har lokacin daya yanke yayi, ita ba ruwan ta waye waye….. Ni k’arshe ma kashe wayar nayi dan tsabar bak’in ciki. Adama ba abunda yake d’aga min hankali irin maganar nan ta fita wasu suji, dukda shima Granpa d’in na san k’ok’arin b’oyewa yake tayi dan Inajin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96