Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 85

Chapter 85

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya maida hankalinshi a direction d’in Ummi, ya ganta zube a k’asa. Dan haka ya mik’e a mugun firgice ransa na k’arasa dagulewa. Abba kuwa ko gezau bai yi ba Yana nan zaune a yanda yake ko motsi ma ba shi da niyyar yi. A gigice Dad ya mik’e cikin sassarfa ya k’arasa inda suke yana cewa “Subahanallah, Abba suma tayi ko me? Duba ta mana, tashi mana, ya kamar baka ga abunda ya faru ba ne?” Ya fad’i hakan yana mai durk’usawa a inda Ummin take. Cikin nuna halin ko In kula ya mik’e tsaye ya karkad’e farar jallabiyar dake jikinshi, kafin yace “At least na sakata tayi mai dalili ai yanzu ba fake ba.” Yana gama fad’in haka ya juya zai hau sama.. Da sauri Dad ya mik’e ya sa hannu ya juyo da shi, bai yi wata wata ba ya d’auke shi da wani mahaukacin mari dan tun lokacin daya durk’usa akan Ummi idanuwanshi suka sauk’a kan takardar saki biyun da Abba yayi mata. Da sauri Auwal wanda ya shigo yanzun ya k’araso inda suke yana cewa “Subahanallah, mai ya faru? Dad wace..?” Maganarsa ce ta katse sakamakon Idanunshi da suka kai kan fuskar Ummi, da sauri ya durk’usa ya hau tattab’ata yana tambayar mai ya same ta?. Cikin b’acin rai Dad yace “Maida ita yanzunnan ko ka fuskanci fushina Yakubu!” Da mamaki Abba yake kallonshi jin yana yin yanda Dad d’in yayi mishi magana da kuma yanda ya kira sunanshi haka! Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “I can’t Dad, I’m really sorry Wallahi baz..” Wani marin ya kuma sakar mishi kafin yace “Kar ma ka rantse! Dan ko ka rantse sai kayi azumi saboda Ummi sai ta koma d’akinta a yau wallahi! Kaji dai na rantse.” Bai ankara ba yaji hawaye yana zuba ta idanunshi.. Cikin kuka yace “Dad bana son ganin fuskar matar nan, tayi ruining komai nawa saboda selfish reason d’inta! Ba zan b’oye maka ba wallahi Ina having second thoughts akan auren Hudan da Arshaad saboda kwata kwata bana son yin nesa da y’ata because i just knew her, all because of ummi. Ka san irin azabar da Hudan ta sha a hannun Usman kuwa? All because of Ummi. Ka san yadda nake jin Maryam a cikin zuciyata? Amma ba yadda na iya dole haka inaji Ina gani ta auri wani ta rayu da shi for almost 20 years!! All because of ummi Komai fa Yaya ita ce sila! Itace silar ciwon zuciyana! Itace silar bak’in cikina! Itace silar lalacewar soyayya ta! Haba haba dan Allah.. sannan yanzu kace In maida ita? Gaskiya kayi hak’uri Yaya, ban tab’a maka gardama ba amman kam yau zan yi maka!. Wallahi ko sunanta ba na son ji kwata kwata..” Ya k’arashe maganar cikin d’acin zuciya sannan yana gama fad’in hakan ya wuce sama ya barsu shi da Auwal wanda yake ta yayyafa wa Ummin ruwa yana son yaga ta farka. Da kyar Dad ya iya juyowa ya kalli Auwal d’in, sannan yace “Kamata mu kaita asibiti, Allah yasa ba wani babban abun bane ya sameta......” Gandun albasa (2:30 pm) A tsakar gidan Madu, akayi decoration na traditional kaulu! Wajen yayi masifar yin kyau. Taken wak’e wak’en Shuwa Arab ne ke tashi in a very low tone. Su Sudais da wasu Yaran sai y’an tsofaffi tsilla tsilla ne a zazzaune a kan kujerun da aka k’awata tsakar gidan da su. Gaba d’aya y’an mata da manyan matan suna ciki, wasu suna had’a takeaway da souvenirs wasu kuma suna shiryawa dayake mostly family ne sai na jiki sosai suka zo dan Mama ba wani taro tayi ba Ita dama ba wani sanin jama a ma tayi sosai ba, sai y’an unguwa da suke ta zirya tun safe waenda rabinsu duk munafurci ne yake kawosu dan an san yau za a kawo lefe. Umma bata da lafiya tana fama da hawan jini amman tun sassafe suka zo ita da Baaba Laraba da yayarta Hansai, kuma wani abun mamaki tunda tazo d’in tak’i kula Mama dan wani mugun zafinta take ji, sun dai gaisa da Shuwa da Ummu Ita kuma Mama sun gaisa da Hansai da Baabaa Laraba amman Umma kam tama k’i bari su had’u dan tana hango ta zata kauce hanya ko ta fad’a d’aki ta shige band’aki. Da Mama ta fahimci hakan kawai sai ta tattarata ta watsar ta shiga sabgar gabanta dan ita mamaki ma Sadiyar take bata duk tabi da d’aurawa kanta wahala gaba d’aya a takure ma kamar ta ganta ga kuma rashin lafiyar Bp da take ta fama. Sai da Anty Zainab ta zo tukunna ta d’an samu ta ware. Itama Anty Zainab d’in da kyar ta iya daurewa suka gaisa da Maman wadda tayi wani irin fresh! Sannan idan ka kalleta ba zaka tab’a cewa sa’ar su bace ita da Sadiyar Sai dai kace Antys d’inta ne dan ba za ma ka ajjiyesu a matsayin yayunta ba! Musammam ma Sadiya wadda ta zama kamar wata mahaukaciya kwana biyun nan! Tun lokacin da taji labarin maganar auren Huda har yau bata san inda nutsuwarta take ba……… Mama na gama gaisawa da Anty Zainab ta juya ta wuce abunta. Anty Zainab kuma ta nufi wajen Umma! Nan kuwa suka hau hassada da zagin Mama har da suna cewa wai “bazawari take nema shiyasa taci wannan uwar kwalliyar”. Laffaya Maman ta nad’a itada Ummu, kalar laffayar ja sai blue d’in flowers, sun yi kyau sosai dan har d’an light makeup sai da Sakina ta tirsasa su suka tsaya aka yi musu. Itama Sakina laffayar ce a jikinta, amma bata nad’a ta har ka ba, instead sai tayi d’aurin Zahra Buhari da mandil a kan nata shi kuma mayafin layyafar ta nad’a a kafad’ar ta. Amarya kuwa ta sha traditional kaya abunta! Hatta hair style d’inta ma irin nasu aka yi mata, daga sama ta nad’a wata had’add’iyar blue black d’in laffaya, aka yafa mata mandil akai. Tun daga kan sark’ok’in k’afarta har na wuya da y’an kunneta da wanda ta sa a kanta na sisin gold duk na asalin gold ne! Wanda Madu ya bata kyauta jiya da daddare, yace “tun na mahaifiyar mahaifinsa ne! Maryam yaso bawa Allah bai yi ba. Ashe rabon ta ne..” D’akin isu isu ne ita da k’awaye ta, anata d’aukar hotuna amman kallo d’aya za kayi mata ka san hankalinta baya ma gidan gaba d’aya! Tun da gari ya waye take jin fad’uwar gaba, gashi yanzu kuma sai kiran Arshaad take yi baya d’auka….. Shuwa ce ta shigo ita da Baabaa Talatu sanye cikin wata rantsatsiyar milk laffaya sun yi anko su biyu suma abun su ita da Baabaa Talatun. Basu dad’e ba wasu mata suka shigo su biyu, daga nan suka umarci Hudan da ‘ta mike a fita da ita’ Aranta ji take kamar ta tambayesu ‘Ya arshaad ne ya zo? Sai kuma taga rashin kunya da zak’ewarta Kuma ta tuna jiya Sakina tace mata ‘Ta bar nuna mishi ta damu sosai fa, idan ba haka ba tabar ganin wai yana sonta Wallahi wahala zata sha....’. Lumshe idanuwanta tayi ta dedeta nusuwarta sannan ta bawa Sakina wayarta ta mik’e, ta jaa mandil d’inta ta rufe kaf fuskarta, su kuma suka tik’eta sukayi waje. Suma su

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});