Chapter 64
Chapter 64
da rejecting shi kuma baya gajiya da kira! Sai dare Abba ya zo d’aukar su, tun safe daman da ta san zasu tafi taketa nuk’u nuk’u Da suka zo tafiya kuwa sai da tayi kwalla! Ummu ce ta rakasu har mota (Sakina Hudan da mai gyaran jikinsu ) ta dawo. Tana shigowa d’akin ta tarar da shuwa tana lallab’a Mama Abun yayi matuk’ar burgeta dan haka ta zauna a gefe tana jin Shuwan tana cewa “Duk abunda hak’uri bai bada ba fushi da zuciya ba zasu kawo ba! kwanaki da kika d’aga hankalinki akan sai Hudan ta dawo hannunki, waye waye aka yi ta rikice dai kina kukan ya rabaki da y’arki hankalin kowa a tashe!. Yanzu ki gaya min a cikin wata d’aya da sati d’ayan nan da wa Hudan tafi zama tsakanin ke da shi? Ai ita y’a mace da Mahaifiyarta aka santa, ki ci gaba da bin komai a hankali wata rana sai labari! Kuma in dai za kiyi wa Abba adalci shima ya kamata ace ya d’an zauna da y’arsa kafin aurenta, kuma kinaji da kansa yace ‘In bikin ya rage saura kwana biyar nan zai dawo da ita a hannunki za a d’auketa!’ Wanne kalar adalci kuma kike buk’atar yayi miki sama da wannan??”….. Shuwa bata barta ba sai da ta tabbatar ta gwada mata gaskiya sannan ta d’an sauk’o tukunna tayi musu sallama ta tafi d’akinta. Ummu da Sumayya su suka ci gaba da zama da ita saboda Baban Sakina yayi tafiya tun wanchan satin. Arshaad ma yayi tafiya zuwa Uk da kuma garin da za suyi honeymoon d’insu… Yaje domin ya d’an yi settling accomodation da sauran harkar karatun su shi da Amaryarsa kafin su tarkata su yi chan gaba d’aya. Satinshi biyu, sai yau ya dawo shima (Washegarin ranar da su Huda suka koma GRA). Aslam ne yaje ya d’auko shi. Ba yadda Arshaad bai yi da Aslam ba akan ya kaishi ya fara ganin Hudan amman furr!! Aslam d’in ya k’i! Yace “ai shi ce mishi yayi yazo ya d’auko shi ya kaishi gida ba golden G Avenue ba.” B’ata rai Arshaad yayi, yana ji yana gani Aslam ya kaishi MT estate. Ko thankyou bai che mishi ba ya bud’e k’ofar fito ya bud’e baya ya d’au kayanshi yana ta b’ata fuska.. Yana shirin rufe murfin motar Aslam yace masa “Amm, by the way you are welcome” Yana d’an dariya k’asa k’asa. Rufe murfin motar Arshaad yayi ya juya shima yana d’an murmushi sama sama har ya isa gida. Yana shiga ya tarar da jakankuna, bai gama tantance na waye ba! Yaji anyi tsalle anyi hugging d’inshi ta baya. Yadda tayi masa ya riga ya san wacece dan haka ya fad’ad’a fara’ar shi ya sa hannu ya zare ta a jikinshi ya juyo da ita kafin yace “Wai ni sai yaushe za ki girma ne?” Turo baki gaba tayi, kafin tace “Ya Arshaad oyoyo d’in kenan? Da fad’a za a yi min sannu da zuwa?” Ta fad’i maganar tana hard’e hannunta a k’irji, sannan ta juya mishi baya alamun tayi fushi. Dai dai nan Aslam ya shigo, d’an murmushi yayi da ganinsu a hakan kafin yace “Har an fara ko? Oya! In kin gama fushin, wuce kitchen ki had’a min black tea. Yau duk kun gajiyar da ni da zirga zirgar airport wallahi, ga drivers a gida kamar me amman kowa In ya dawo daga yawon sa sai yace Ni!”. Sake turo baki Aaima tayi kafin tace “Ya Arshaad makarantar ne yawo? Shikenan naji ba komai duk na lura bakwa murna da ganina. Ina Mammy ne? Na duba ko ina bata nan! Ka ce mini bata da lafiya shiyasa ta kashe wayoyinta, meyene ya sameta tana ina ? Wallah duk hankalina a tashe yake, bafa ayi hutu ba ma na dawo! Dad shima same yadda kuke yi haka yayi min.” Ganin duk sun yi shiru sun kauda kai yasa ta k’arashe maganar tata a hankali tana mai cewa “kuyi min magana please”. Aslam ne yayi k’arfin halin cewa “Aaima, kawo min tea, ki huta kici abinci daganan sai mu yi magana ko?” Gani suka yi kawai ta fashe da kuka, cikin kukan tace “Ya Aslam dan Allah in mutuwa Mammy tayi ku fad’a min dan Allah.” Da sauri Arshaad ya toshe mata baki da hannunshi kafin yace “Mammy tana nan, kinji!! Babu abunda ya sameta, in fact zuwa anjima ma zan kaiki ki ganta, kin ji? Yanzu ki huta tukunna nima bara inyi freshening up, sai muzo ayi magana ko?” Cikin tashin hankali tace “Ba dai rabuwa sukayi da Dad ba, ko? Ya a....” Cikin tsawa Aslam yace mata “Idan kika bari na k’araso wajen nan sai na tattakaki wallahi!! Ba za ki wuce kiyi abunda akace ba?” Ta tsorata sosai da tsawar shiyasa ta zo ta wuce sum sum ta shige kitchen d’in jikinta na karkarwa, tana matsar hawaye. Sai da ta wuce kuma sai Aslam d’in yaga rashin kyautawarshi “Damn it!” Ya furta hakan chan k’asan mak’oshi, kafin a hankali ya rintse idanunsa… Shi kad’ai ya san me yake going through those days! Abun har tsoro yake bashi, shekaran jiya fa Gwaggo Asabe ya yiwa tsawa! Abunda bai tab’a tunanin zai kwananta yi ba ko da kuwa da wasa ne. Abunda ya kai yaji haushi da wanda bai kai ba gaba d’aya hassalashi suke yi! Haushin kowa yake ji! Ya tsani kowa ya tsani komai! Baya son shiga mutane, shiyasa shi kuma yake tilastawa kanshi ya dinga shiga mutanen saboda yayi fighting abunda ke shirin hargitsa rayuwarshi! But ko hirar minti uku ba a yi dashi ta kirki, zai fara fad’a. A hankali yace “Ya Allah ka yaye mini abunda yake shirin k’arasa tarwatsa rayuwata, Ya Allah ka ji k’aina.” Kallonshi kawai Arshaad yake yi, ya dai san magana yake yi amman baya iya jiyo abinda yake fad’a. Ya kusan minti uku a tsaye yana kallonsa, kamar zai k’arasa wajenshi sai kuma ya sunkuya ya d’auki suite case d’in shi da ta fad’i garin oyoyo d’in Aaima, ya jaa trolley d’inshi ya nufi side d’insa. Yana wucewa Aaima ta fito da tea d’in akan d’an karamin tray, ta ajjiye mishi tace “Gashi” Bata jira jin mai zai ce ba ta wuce sama itama don yin wanka. Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e, kafin yasa hannu ya d’auki cup d’in wanda yake ta uban tururi yayi sipping a hankali.. Da kyar ya iya had’iyewa sakamokon wani tururi da yake ji yana taso mishi daga k’irjinsa yana yowa sama.. He hates this! Yana disturbing peace d’inshi, kamar ya sa hannu ya kwakule heart d’inshi ya jefar haka yake ji… Takaici da ya isheshi ya sanya shi d’aga cup d’in ya kafa a baki ya hau kwankwad’a yana had’iyewa da k’arfi! Ko zafin tea d’in ba ya ji saboda wanda yake ji a k’irjinsa ya ninnika na tea d’in. Sai da yaga bayan tea d’in tukun ya hak’ura ya ajjiye cup d’in yana uban gumi, had’i da sauk’e ajiyar zuciya a jejjere. A hankali ya jinginar da kanshi da bayanshi a jikin kujerar yana sauk’e ajjiyar zuciya still kafin ya lumshe idanuwanshi… Sai bayan kusan minti talatin tukun Arshaad ya fito wanda kana ganin sa ka san zance zai je. Sanye yake cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96