Chapter 70
Chapter 70
lafiya! Ga Junaidu ya b’ata! Matsalalo gasu nan burjik sunyi mana yawa ke kuma kin matse bakin aljihu ya kike so inyi???. Ni kaina sai na mutu dan bak’in ciki in dai Huda ta auri Arshaad d’innan ba ke kad’ai ba! Haba dan Allah mana sai kace su kad’ai Allah yake so?? Baban ta mai kud’i sannan ta auri mai kud’i! Inaa, ba zai yiu ba gaskiya!” Umman ta k’arashe maganar cikin tsananin tashin hankali. Cikin kuka Jalila tace “Umma yanzu meye abun yi? Dan Allah karta aure min shi wallahi Umma ina son Ya Arshaad sosai.” Ajiyar zuciya Umman ta sauk’e kafin tace “Ki bani kud’i! Ki turo kud’i! Ki zuba mini ido kawai, shine abun yi.” A hankali Jalila ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Tam shikenan, Ta accnt d’inki ko?”. “Eh” Kawai Umman tace saboda tsantsar tashin hankalin da take ciki ba zai iya barinta tayi magana sosai ba. “Tam” kawai Jalila tace ta kashe wayar daganan ta tura mata ragowar kud’in accnt d’inta da ta ishi Auwal, ya tura mata da kyar.............. Bayan Arshaad ya tafi sun d’an tab’a hira tukunna Gwaggwo Asaben tace “itama bara taje ta bawa Mommy maganin nata ta sha ta shaafa dan yanzu ita take yi da kanta” Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tace “Ka zo muje kaga jikin nata mana”. Ahankali ya girgiza kai kafin yace “Gwaggo na san da sauk’i tunda gamu waje d’aya amman lafiya, kuma kin ce tayi garau yanzu to ai Alhamdulillah! Inaga ba sai na je ba, kar muje a samu matsala.” Shiruuu, Gwaggo tayi.. Ita har ga Allah so take Aslam d’in yaje ya ga Mommy watak’il In ya ga ta warke shima ya samu ya rage damuwar da ta hau kanshi. Amman tunda taga baya so bara kawai ta kyaleshi. Ganin dayayi kamar bata ji dad’in musun da yayi mata bane yasashi mik’ewa kafin yace “muje to” Murmushi ta saki tace “Yauwa d’an albarka, muje.” Itace a gaba shi a baya Haka suka nufi saman ba don ranshi yana soba gashi k’irjinsa In banda dukan uku uku ba abunda yake yi. Wutar parlourn a kashe suka tadda, suna k’ok’arin kunna flash d’in wayoyin su haske ya gauraye ko Ina! Bata lura da shi ba tace “Yanzun fa nake shirin kiranki na jiki yau duk shiru! Sai kuma nace bara in yi wanka kafin ki zo, kin ga banma ida shiga d’akin ba naji motsinki.” Tana maganar tana tahowa garesu. Aslam mutuwar tsaye yayi! Dukda a cikin zuciyarsa hamdala yake yi na ganinta a hakan, amma kuma bayaso suyi ido biyu dan bai san ya zata kaya ba! Hakan ne yasa shi fara ja da baya dan barin wajen Ita kuma kamar ance ta d’ago karaf! Suka yi ido biyu da ita...... Ta k’uraa mishi idanu ko kiftawa bata yi tana kallonshi kamar da mamaki akan fuskarta… Lura da hakan da Gwaggo Asabe tayi ne wadda itama ba k’aramin firgice ta shiga ba ya sanya ta daure taje ta fara jan hannunta tana “Muje ga tofin naki kisha In kin fito wankan sai ki shafa ko?” A hankali suka ji Mommy tace “Aslam!” Aslam wanda already ya juya da niyyar tafiya har ya d’aga k’afar shi jin ta kira sunanshi ya sanyashi dakatawa ba tare da ya sauk’e k’afar shi ko ya juyo ba! Sai da ta sake cewa “Aslam” Tukunna ya ajjiye k’afar ya juyo yana kallonta da idanuwanshi da suka rine lokaci guda!. Dafe kanta tayi da k’arfi, ta runtse idanuwanta kamar mai son tuno wani abun… Ganin haka yasa Gwaggo Asabe ta sake kamo ta kafin ta ce mata “Muje ki huta dan Allah” Sannnan ta baya ta yiwa Aslam d’in alamar ya tafi da hannunta. A hankali Mommy ta bud’e idanunta tana sake kallonshi kafin tace “Asabe me ya faru da ni? Kin ce nayi rashin lafiya meye ne ya sameni? Na shekara nawa?. Kinga fa Aslam kina ganin abunda nake gani kuwa? Shekara ta nawa a kwance? Dan Allah kimi.....” Gigitacciyar rungumar da Aslam wanda ba suba tahowarshiba yayi mata ne ya sanya ta kasa k’arasawa… Tana shirin yin magana taji Gwaggwo Asabe ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi cikin kukan banda kalmar “Alhamdulillah!” Ba abunda take ta nanatawa. Da kyar Mommy ta iya b’amb’aro Aslam daga jikinta, a hankali da hawaye sharkaf akan fuskarta ta shafa fuskarshi wadda ta koma jajir kafin tace “Loosing memory nayi ko?” Ta fad’i hakan tana mai fashewa da kuka. Rasa wanda zai rarrashi wani akayi tsakanin ita da Gwaggo Asabe.. Aslam kam banda ajiyar zuciya ba abunda yake sauk’ewa! Shi kanshi yau so yake hawaye ya zubo ta idanunsa amman abun ya gagara! A hankali ya cika mata hannunta dake cikin nashi ya dan jaa da baya kafin ya seseta gabas ya durk’usa yayi sujjada! Da sauri itama Gwaggwo Asabe tayi sujjjadar, ita kam Mommy tsayawa tayi tana kallonsu tana hawaye da mamakin abunda ya sameta haka… ….Wani abun mamakin still shine yanda ta kasa tambayar inda Aslam d’in yake har sai da ya baiyyana a gabanta! Wanne irin loosin memory tayi haka ita kam? Aslam wanda ta san shekarunshi basu wuce 12 ba shine yanzu haka wanda ta tabbatar yafi 30! Daman tun kwanaki 7 da suka wuce tayi noticing yanda Gwaggo Asabe tayi aging da kuma ita ma kanta! Mai ya faru? Wanne irin ciwo tayi haka? Innalillahi wa inna ilaihirrajiun Allahumma ajirni fi musibati… Take ta maimaitawa cike da rud’ani da alajabi gaba d’aya kwanyarta ta cunkushe............ A hankali Aslam ya mik’e ya kama hannunta suka shiga d’akinta ya zaunar da ita kafin yace “Ina yake miki ciwo, yanzun?” Murmushi tayi ta shafa fuskarshi a hankali tace “Ba ko ina” Sai kuma ta sake fashewa da kuka. Hugging d’inta kawai yayi yana tapping bayanta. A hankali ya d’auko wayarshi, ya hau kiran Dad video call, bai damu da time ba. D’auka Dad yayi suka gaisa yana tambayarshi “ya shirye shirye na bikin su Arshaad?” A hankali Aslam yace “Alhamdulillah” Sai kuma ya gyara zamanshi ya matsa kusa da Mommy ya kamo hannunta cikin nashi ya d’an kalleta yayi murmushi yana ganin yanda ta k’urawa Dad d’in ido, kafin ya juyo ya kalli Dad shima yace “Alhamdulillah Dad..” Bai ida rufe bakinshi ba, yaji Dad d’in ya saka kuka, cikin kukan shima yace “Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!” Sannan yace “Aslam ganinan zuwa yanzun nan, in shaa Allah” Da sauri Aslam d’in yace “No dad, kabari sai gobe yanzu dar....” Kit! Dad ya kashe wayar ba tare da ta tsaya jin maganar Aslam d’in ba. Anan aslam ya zauna, ya rik’e mata hannu gam kamar ance za a kwace mishi ita! Sai kallonta yake yana murmushi yana sauk’e ajiyar zuciya in yaji hakan bai mishi ba yasa hannu yai hugging d’inta. Ita ma Gwaggo Asabe a daren ta kira Yaranta duk biyun ta fad’a musu halinda ake ciki, murna a wajensu ba a magana, suka ce “in shaa Allah, za su tambaya. Za su taho suma in shaa Allah.” A haka Mommy ta sha addu’o’i ta shafa da hannu d’aya dan Aslam yak’i cikata, Gwaggo Asabe tana musu dariya tana kuka at the same time. Ko cikakkiyar awa biyu Dad bai yi ba, sukaji tsayawar mota.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96