Chapter 67
Chapter 67
nufi waje bayan sun gama gaisawa da su Arshaad d’in. Ganin ta biyo shi ne yasa ya d’an tsaya a y’ar varendar bakin main door d’in, tana k’arasowa Auwal shima yana isowa wajen! Ai kuwa ta had’e rai ta cuno baki ta d’auke kai. Shi kuwa Auwal gaba d’aya numfashinsa sama yaji yayi, da kyar ya samu ya seseta kanshi, ya shiga gaida Abba cikin nutsuwar da Abban bai tab’a saninshi da ita ba. Murmushi Abban yayi bayan sun gaisa yace “wuta da auduga” yana kallon Sakinar da ta d’an kalleshi kad’an, kunya ce ta rufeta dan haka tace “Ya auwal Ina wuni” Murmushi yayi wanda ya baiiyyana dimple da tsantsar kyawun fuskarshi, kafin yace “Lafiya, ya gida? Kwana biyu” Cikin takaici tace “Alhamdulillah” Abba ne ya katsesu ta hanyar cewa “You were saying?” yana kallon Sakina had’e da kallon agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunshi. Bataso yin maganar a gaban Auwal ba amman ba yadda ta iya, hakan yasa tace “Um daman Abba, wai pre wedding picture nake so inyi surprising su Hudan da shi, In ba damuwa, please.” Dan k’uraa mata ido yayi, kafin yace “Okay, banda shirme.” Sannan ya juya har zai wuce sai kuma ya juyo yace “Kina buk’atar cash ko?” Yayi maganar yana mai zura hannunshi a aljihu. Dasauri Auwal yace “No. Abba I’ll take care of it.” “Okay” kawai Abban yace, dan sauri yake yi, yayi gaba ya bar su a wajen. Murmushi Auwal yayi kafin ya dawo dai dai setin Sakina inda ta kawar da kai ta mayar da fuskarta ta, yace “For this surprises sake za a d’an kula ni ko? Na wuni d’aya tak dai?” Ya k’arashe maganar yana karyar da wuyanshi sannan ya maida fuskarshi kalar tausayi. Kallonshi tayi, bakinta na d’an motsi, tana son yin magana amman yanda idanuwanshi ya sarke da nata ne, ya sanya ta kasa cewa komai. A hankali ya lumshe idanunsa ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciyar da har sai da ta jiyo hucin numfashinsa mai d’umi wanda ya had’e da wani calm scent da kuma k’amshin turarenshi… tana shirin d’auke idanunta daga kan kyakkyawar fuskarshi, ya bud’e idanunshi cikin hikima ya sake yin nasarar sark’e kwayar idanuwan nasu waje d’aya, a hankali taji yace “I love you!”. Gabanta ne ya bada wani ‘Dumm!! Da masifar k’arfin da bata san dalili ba.... Da kyar ta aro jarumta ta yafa, da mugun k’ok’ari tayi nasarar zare kwayar idanunta a nashi k’irjinta na ci gaba da dukan uku uku. Harara ta zabga masa, ba tare da ta yarda ta sake kallon cikin idanunshiba had’e da yin tsaki sannan ta juya da mugun sauri zata shiga ciki..a ranta tana aiyyana ‘Tabbas Auwal tantirin shed’an ne!’ Dan gashi yana k’ok’arin rusa mata tsari cikin mintunan da basu gaza ashirin ba… Da kyar ya iya had’a kuzarin da ya bashi nasarar shan gabanta, ya tsaya a bakin k’ofar, dan ba k’adan ba jikinshi yayi mugun yin weak! Da sauri ya had’a hannuwanshi biyu waje d’aya kafin yace “I’m sorry? so sorry ba zan k’ara ba. Please lets just.. Bari in kira wanda na san zai yi, a Kano yake yanzu nan zai zo, professional ne, okay?” Ya k’arashe maganar da alamun serious a kan fuskanshi, yana mai d’aga mata gira duka biyu da d’an ware ido. “Unhm” Kawai tace sannan ta koma gefe tayi folding hannayenta tana kallon wani waje. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, ya fara k’ok’arin dialing number mai hoton…. A gabanta suka yi waya sukai fixing time @5:00 pm Zai k’araso, nan da 2 hours kenan. Suna gama wayar tace “thankyou” kawai sannan ta fara k’ok’arin wucewa. A hankali yace “Am, Sakina… i”. Da sauri ta d’aga mishi hannu d’aya, alamar (stop) Kafin tace “Ya Auwal please.. Ka kyale ni! Bana so!. I’m in a very serious relationship, besides ko ma bana dating d’in kowa I will never ever choose you! After what you did to Jalila kuma still ka ke dodging.. Kullum ko sunan ka naji an kira abunda nake tunowa kenan!. Ban shirya auren bazawari ba, ko da ace maza sun k’are ina rok’on Allah kar ya d’aura min k’addarar auren bazawari second hand.” Auwal bai san san ya akai ba, amman tabbas kamar hawaye yake ji suna shirin zubo mishi. Ita kanta Sakinar ta lura da yanda idanunshi suke kyallin hawaye. Jikinta ne ya d’anyi sanyi dan haka ta yi k’ok’ari ta danne ragowar maganganun da take ji suna taso mata. A hankali yace “Sakina na rantse miki da Allah a yanda nake jin ki a cikin zuciyata, ba abunda ba zan iya sacrificing akan ki ba, kuma babu abunda ba zan iya yi a kanki ba, zan iya chanja kaina in koma yadda kike so na zama, muddin zaki yarda da ni. I don’t know how why but ni kaina ina jin tsoron kalar k’aunar da nake yi miki! I just knew you but i have fallen head over heels… Na tabbatar ba wanda ya tab’a yiwa wata kalar pure love d’in da nake yi miki.. Ba wai wani abu daban ba kawai k’aunarki, yardarki, soul d’inki shi nake muradi.” Ya k’arashe maganar cikin karyewar zuciya. Shiruu, tayi kawai tayi k’asa da kanta, bata k’aunar abunda zai sa ta sake had’a ido da shi. A hankali tace “Ka rabu da ni! Dan Allah.” Yana shirin yin magana Arshaad ya bud’e k’ofa Hudan na a bayan sa. Juyawa Auwal d’in yayi aka hau kallon kallo..,, Arshaad ne ya katse shirun ta hanyar mik’awa Auwal hannu suka yi musabaha, a hankali Hudan ita kuma ta gaidashi. Yana amsawa ya wuce ya nufi part d’insu yana ji kamar zuciyarshi zata fashe! Tabbas ya san ba komai ke binshi ba sai hakki..Hakkin y’an matan da ya yaudara, da waenda ya wulak’anta, da waenda yayi mocking soyayyar da suke yi mishi! Duk hakkin su ne yake binshi. Yayi mocking soyayya, ya yaudari dayawa ta hanyar kalmar soyayya, ya wulak’anta dayawa dan sun nuna mishi zallar soyayya, shiyasa shi kuma yanzu Allah ya d’aura mishi tsantsar so mai mugun zafi da azabtar da zuciya wanda ya san wadda yake yi wa ba lalle ta soshi ba, gashi yanzu ma direct ta fad’a mishi ‘she’s in a very serious relationship’ wanda hakan sai da ya kusan kasheshi ba tare da ta lura ba. Daman haka so yake? Dama haka mutum yake ji? Tabbas shi kam ya san ajalinshi..dan muddin Sakina bata yarda dashi ba akwai matsala! Ranar kuwa da akace ta auri wanda take ik’irarin suna tare d’in ya san a ranar zai bar duniya…… Yana wannan lissafin da tunanin ya k’arasa b’angarensu, direct side nasa ya nufa, yana zuwa ya rufe ko Ina ya k’ara k’arfin ac ya zxube a kan kujera, ko d’aki kasa k’arasawa yayi.......... Hudan ta bud’e baki kenan zata yi magana Sakina tayi sauri ta wucesu ta shige ciki. Direct sama d’akin Hudan ta nufa, ta dad’e ta kusan awa d’aya tana juyi a kan gado ita kad’ai, daga baya ta hak’ura ta sauk’o. Suna zaune suna hira su Sudais suna gefe suna chess, tun da suka dawo daga karb’o gown d’in ta (Hudan) wadda delivery man ya kawo suke zuba idon ganinta amman bata sauk’o ba, Hudan taso zuwa amman Arshaad ya hanata…
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96