Chapter 81
Chapter 81
wajen ingije Arshaad d’in sannan kafin yayi nasarar tsaidata ta tafi gaban Dad ta tsaya! Tana mai jin wani tuk’uk’in bak’in ciki yana taso mata, babu abunda idan ta tuna yake k’ona mata rai irin yanda taga Daddy yana ziryar zuwa wajen Adama last zuwanshi da yayi har kusan kuka taga yayi daga nan ma yace ‘ba zai iya sake ganinta a haka ba’ Tun daga ranar kuwa idan bai kirata sau d’aya ba tou zai kira sau biyu! Amman ita ko lek’enta ko waya Dad bai tab’a yi yace a bata ba, ita tana chan tana tunanin sa ashe shi yana nan Aisha ta d’auke masa hankali! Kalli fa sarai ya san ta dawo amman ko lek’enta bai yi ba kuma suna cikin gida d’aya, sai yanzu dan rashin kunya da tsaurin ido ya buk’aci ganinta kuma ko alamar tambayarta ya take bai yi ba instead ya hau wani tsattsare ido yana hucin banza.. Waennan takaicin ne suka sanya ta kasa cewa komai kawai ta zube a wajen ta fashe da wani mugun kukan bak’in ciki. Cikin son kawar da lamarin Arshaad yace “Dad, dan Allah ka bar maganar nan, na fad’a maka ba komai fa”. Banza Dad yayi da shi kawai ya juya ya fice! Yaso ace Mammy tayi mishi wani shirmen yau wallahi da sai ya yi mata abunda bata tab’a tsammani ba! Ya san at least zai samu peace of mind at last. Yana fita Mammy ta mik’e! Tunda take a rayuwar ta bata tab’a jin kishi da takaici da tashin hankali da bak’in ciki irin na yau ba! Ta rasa dalili amma ko y’ar kissar da ta saba yiwa y’ay’an nata da Dad d’in ta kasa kuma bata jin zata iya, babu abunda take so kuma take buri irin taga ta b’atawa Dad rai ko ta samu zuciyarta ta d’anyi sanyi. Tayi imani yanzu haka wajen Aisha zai tafi yaje ya ganta yad’an samu nutsuwa hankalinshi ya d’an kwanta alhalin ita kuma gashi ya k’unsa mata bak’in cikin da bata jin zata iya mantawa da shi har abada! Taya zai yi mata haka? Taya zai banzantar da ita har haka saboda Allah kamar wata dabba? ‘Inaaa!! Ba zai yiu ba Wallahi’ Shine abunda ta fad’a ta gyara tsayuwarta tana k’ok’arin yin hanyar waje….. Da sauri Hajiya Binta ta tareta tace “Meye haka ne wai Mammy? Ba a isa a fad’a miki kiji bane? Ina za ki ji yanzun?” Cikin kukan Mammy tace “Kina ganin fa abubuwan da Yahaya yake yi mini Ya gama b’ata min rai ya fice ya tafi wajen uwar gidan shi ya bar ni ni anan zuciyata ta kama da wuta kenan ko me? Ki cikani kawai, wallahi bai isa yayi farin ciki ba, ba inda zai je yau, kullle k’ofar gidan nan zan yi sai dai mu kashe juna ni da shi a cikin gidan nan!” Da sauri Arshaad ya matso kusa da su ya rik’eta, wani tsananin takaicin sa take ji hakan yasa ta juyo da sauri ta kifa masa Mari! Sai kuma ta fashe da kuka, cikin kukan tace “Ai kaima baka kishina Arshaad, a tunanina ko Hudan y’ar gwal ce wallahi ba za ka so auren ta b. Taya za ka had’ani da ita mu zama surukai!? Ko kasan cin mutuncin nan da aka yi min shine abu mafi muni a rayuwata?. Na fad’a na k’ara fad’a yanzu ma zan maimaita maka ‘Wallahi idan ka aureta sai na tsine maka!’.” Arshaad bai san lokacin da ya tsugunna a wajen ba ya fashe da wani mugun kuka. Cikin b’acin rai da kafiya Mammy tace “Kuma ko event d’in yau da suka gaiyyaceka ban yarda ka je ba! In kaje kuma wallahi Allah ya isa ban yafe ba! Zan ga wa zaka zab’a tsakanin ni da ita.” Da sauri ya mik’e yace “Haba Mammy ya kike so inyi ne? Ki tsaya ki saurareni kuma kin k’i.. Dad ne ya nema min aurenta Abba kuma ya bani, idan nayi miki biyayya su kuma bijire musu kike so in yi?” Da sauri cikin katsesu Hajiya Binta tace “Rukayya ban tab’a tunanin baki da hankali ba sai yau wallahi! Ni, na fad’a miki! Mahaifiyarmu, itama ta fad’a miki! Amma ba za ki ji ba? Waye a cikinmu zai fad’a miki abunda zai cutar da ke? Munce kiyi hak’uri ko? Waennan irin y’an iskan aljanu masu shegan taurin kai kika kwaso a cell d’in ne wai?” In banda gunjin kuka babu abunda Mammy take yi. Cikin son su kad’aita iyaka su biyu dan ta samu damar lallashinta da fahimtar da ita Hajiya Binta ta cewa Arshaad “wuce ka tafi ka shirya ku je ku yi event d’in, idan ka dawo sai mu k’arasa” Ai kuwa Mammy na jin haka ta tafi da gudu hanyar k’ofar fita ta tsaya tayi stretching hannunwanta sideways ta kare k’ofar tace “wallahi idan ka fita sai na tsine maka!!” Da sauri Hajiya Binta tazo ta kama hannun tana k’ok’arin janyeta tana cewa “Arshaad zo ka wuce” a ranta tana aiyyanawa ‘Tabbas akwai abu a kan Mammy’ “Zo ka wuce nace kar ka bari tayi maka spoiling day d’inka!” Hajiya Binta ta sake maimaitawa ganin Arshaad d’in ya k’ame a waje d’aya abun tausayi. A hankali ya k’araso ya shiga lallab’ata, Hajiya Binta itama tana yi, amman fur!! Mammy ta yi kane kane a hanyar tana ta faman maimaita kalma d’aya ‘Idan ka fita sai na tsine maka!!’ Basu ji lokacin da akai sliding k’ofar aka shigowa ba sai dai kawai suka ga an juyo da Mammy an wanke ta da mari! Diff!! haka parlourn yayi tsit! Cikin b’acin rai Maman Mammyn tace “Yi maza kaje ga Aaima chan driver ya bata kayan da zaka saka ta kawo. Jeka ka shirya yanzun nan za muzo mu rakaka.” Har ya d’anyi gaba sai kuma ya juyo yace “Tace fa In na fita sai ta tsi..” Cikin katseshi Maman Mammyn tace “Nace ka fita ko! Ta tsine makan in gani.” A hankali yad’an kalli Mammyn yaga ta d’auke kai daga kallonshi, cikin nutsuwa yayi sliding door d’in ya bud’e ya fice, yana mai share ragowar kwallar dake kwance akan fuskarshi. Yana fita ta fashe da kuka, cikin kukan tace “Da wanne kuke so inji ne wai? Ya kuke son inyi? Wallahi ko sunan Yarinyar bana so a kira! Ji nake yi kamar zan mutu, ku duba fa kuga yanda yake kuka shab’e shab’e dan kawai nace ba zai aureta ba! Idan ya aureta kuma ya kuke tunani??” Hugging d’inta Mahaifiyar tata tayi tana d’an bubbuga bayanta… Sai da ta tabbatar tayi shiru tukun cikin sigar lallashi tace “Kiyi hak’uri Rukayya, ke fa da kanki kikace Mijinki yana share ki! Ki duba fa ko wajen ki baya zuwa kuma da kika dawo bai nemeki ba, ko ya yi miki magana bayaga yanzun?” Cikin sheshshekar kuka Mammy ta hau girgiza kai alamun ‘a’a’. Ajiyar zuciya Maman nata ta sauk’e kafin tace “Kinga ko! Wannan ma kad’ai abu ne wanda ya kamata a tsaya a duba da kyau. Yanda kikace Matar nan tasa ta warke, da kuma dalilin da ya sanya yake ta faman jin haushin ki wanda bamu san daliliba yanzu shine abun a tsaya a duba a gyara bawai wannan k’aramin alhakin ba.”
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96