Chapter 11
Chapter 11
Dan shi kanshi Aslam d’in abun a jiye mishi ne, saboda gaba d’aya rayuwarshi ya yita ne cikin fargaba, k’unci da damuwa. Yanzu haka ko Abokanai baya iya tarawa shi kad’ai d’insa yake komai sai dai a d’an dinga zumunci sama sama, Abokin shi na k’ut da k’ut guda d’aya tak a duniya wato Arshaad, da Arshaad ne kawai za kiji suna waya suna d’an raha amma ko mu y’an gida wani lokacin idan ka kirashi sai yak’i d’auka. Tsoronma shiga mutane yake yi balle yayi huld’a dasu.. Naji su Abba suna cewa ‘Kana ganinshi in dai ka fahimci yanayin shi tou tashi d’aya zaka fahimci he’s depressed! Kuma hakan ba a so a mutum especially mai k’arancin shekaru kamar nashi, zai hanashi yin farin ciki a rayuwa ne kwata kwata, har abada!.” Ahankali tace “To amman ya za ayi? Magani in dai sunanshi magani tou ba kalar wanda ba ayi ba amman har yanzu shiru............” Ta k’arshe maganar tana share d’an hawayen daya biyo idanunta a karo na ba adadi. Hudan, itama hawayenta ta goge, a ranta tace “Allah sarki bawan Allah, ashe shiyasa kullum yake cikin fushi, da har nake jin haushinshi.. In shaa Allah daga yau na daina jin haushinshi, Allah ya bawa Mahaifiyarta lafiya.” Maganar Gwaggo Asabe ce ta katseta jin tana cewa “Kema dan Allah idan kin yi sallah ki dinga sakamu a addua Allah ya kawo k’arshen wannan abu.” A hankali Hudan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “In shaa Allah” Sai kuma ta gyara zamanta ta ci gaba “Amman Gwaggo a duk cikin bayaninki banji inda aka yi mata Sauk’ar Alqur’ani ba!” Cikin katseta Gwaggo Asabe tace “anyi sauk’a Huda, Granpa da Dad da kansu suka je suka raba kud’i lokacin da suka dawo farko farko a islamiyoyi da tsangayar almajurai aka yi ta sauk’a!.” Murmushi Hudan tayi sannan tace “Gwaggo Asabe, idan zan bada shawara a d’auka inaga daa mu da kanmu ya kamata muyi mata sauk’ar bayan an raba a islamiyoyin, kuma in na fahimceki kamar sau d’aya aka tab’a yin sauk’ar ko?” Bata jira jin mai Gwaggo Asaben zata ce ba ta ci gaba “Ni a lokutan baya, idan bamu da lafiya ko wani alamari mara dad’i ya afku Tou bayan Mama ta bamu magani sai ta kammala mana sauk’a, ko lokacin da nake k’arama akwai Yayanmu da yake shaye shaye sai da Mama tayi mishi sauk’ar AlQur’ani sau bakwai!! Ta fara tayi sau hud’u ya warke ya daina amman dake tayi niyyar bakwai d’in zata yi sai da ta k’arasa. Da kuma muka yi wayo haka zata rarraba mana muna tayata da ni dasu Ya Jalila koda izu d’ai d’ai ne mu kan taimaka. Ko yanzu haka In wani abun ya faru rabawa muke yi ni da ita da Sakina wani lokacin da Sumayya, bama wata d’aya muke k’arasawa, in kuma mun kwallafa to a sati muke idawa. Balle nan gidan munada d’an yawa.. Yanzu for example ace mutum shidda kowa ya d’auki izu goma, duk bayan sallar Farilla kayi izu d’aya a kwana biyu fa za mu dinga kammalawa, In kuma izu biyu za ana yi a cikin kwana 1 mun kammala, inda hali kowa in ya kammala sai yayi mata addua dafatan waraka bayan an tofa aruwa a bata tana sha, Daganan ayita yi, kuma akai akai. In Allah ya yarda sai kiga an dace. Dan dai gaskiya kamar yadda kika fad’a abun sam kamar bana asibiti bane ba! Koda ace ma na asibitin ne Sauk’ar Alqur’ani fa shine k’arshen waraka Especially idan mune muka yi da kanmu, saboda waennan na islamiyya ba mu da tabbas, yanzu duniya ta chanja ba lalle In sun karb’i kud’in suna sakawa anayi ba…..” Maganarta ce ta katse jin mutum a tsaye a bayanta ya dafa kanta, tana juyowa sukai ido hud’u da Dad da Abba a bayanshi suna murmushi, waenda shigowarsu kenan suna d’an tatauna wata magani suka ji bayanin Hudan. Dad ne yace “y’ar albarka, naji dad’in wannan shawarar taki sosai. Kuma daga yanzu in shaa Allah zata fara aiki. Kafin masu kwashe kaya su gama na san mun kammala in shaa Allah, na yau.” Yana gama fad’in haka ya d’au waya ya kira Arshaad da Aslam yace “su sameshi.” Sai da ya gama wayar, Hudan ta d’an zame daga kan kujera inda take ta shiga gaida Abba. Shima Dad d’in ta sake gaidashi. Cikin kulawa suka amsa mata sannan suka cigaba ta tattaunawarsu da alamun magana mai muhummanci suke yi. Hudan sai d’ar d’ar takeyi a tunaninta kar Abba yai mata fad’an abunda tayi mishi jiya, shima ya lura da yanayin ta shiyasama ya fasa zuwa inda take, amman da yayi niyyar jin yadda ta kwana da kuma jin ko akwai abunda takeso dan harga Allah shikam yana so ya zama tare da y’arsa ya jaa ta a jiki ko sa samu su saba da juna sosai. Arshaad ne ya fara shigowa… Tsayawa Hudan tayi tana kallonshi dan ta manta rabon da ta ganshi da k’ananan kaya, yafi ta’ammali da shaddodi da yadi, sab’anin yau da yake sanye da wata shirt army green dark an rubuta ‘KING’ a jikin gaban rigar da zanen crown d’in king d’in ata k’asa. Rigar irin mai d’an kama jiki ce, hakan ya taimaka wajen fito da ainahin surar jikinshi dan kana iya hango packs d’inshi na sama sama ta cikin rigar da yadda dantsen hannunshi yake a mummurd’e! Wandon nashi shima ba jeans bane yana yin rigar ne black in colour bai kamashi ba kwata kwata ta sama amman roba ne, kasancewar ya d’an matse daga guiwar wandon zuwa k’asa yasa ya zama kamar pencil trouser ta k’asan… Kayan yayi matuk’ar fito da asalin surarshi ta giant! Ga wani fitinannen k’amshi mai tsayawa a rai da yake zubawa dan tunda ya shigo parlourn ya karad’e da k’amshin shi, tun bai iso inda suke ba…. Hudan bata gama k’are mishi kallo ba suka had’a ido da shi, gira d’aya ya d’aga mata yana d’an murmushin gefen baki, da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa kunya duk ta lullub’eta ganin ya kamata tana kallonshi . Ganin yadda tayi ne ya sanyashi sakin wani lallausan murmushi, kafin ya k’arasa inda su Dad suke ya shiga gaidasu cikin girmamawa. Ya so ya k’arasa wajen Hudan dan shima ba k’aramin kyau tayi mishi cikin rigar abaya blueblack mai stones, d’aurin da ta yiwa kanta da d’ankwalin abayan ya yi matuk’ar burgeshi! Amman sai Dad ya tsareshi ta hanyar fara yi mishi bayani abunda za suyi ba tare da b’ata lokaci ba, 100%ya amince da kuma jinjina ga wanda ya kawo shawarar dan abunda ya kamata ayi kenan, cikin jin dad’i Dad yace “ai Hudan ce” da d’an murmushi ya juyo yana kallonta, yanzun ma sauri tayi tai k’asa da kanta, don still satar kallonshi take yi, harga Allah Ya Arshaad yayi kyau yau sosai…… Tana wannan tunanin hancinta ya fara jiyo mata wani k’amshi na daban, wanda a take ya cika mata hanci, kuma ta fahimci wanene Kasancewar a kan kujerar dake gaban side d’inshi take ne yasanya ta fara jin k’amshin kafin kowa, bata san daliliba ba kuma tasan mai ya faru ba, amman ko lokacin idan anyi laifi a islamiyyarsu za a dakesu tabbas zuciyarta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96