Chapter 72
Chapter 72
nan cikin Nasarawa sai dai da d’an tafiya tsakaninsu da gida da estate.... Su Ummu da Mommy ne suka je suka yi mata jerenta tsaf! Wanda yanzu kawanchen Mama da Mommy ya dawo sabo fil! Dan har gida Mommy taje ta dubota, duk da Dad ba wani son yawan fitar tata yake yi ba amman indai abu ya shafi Maryam to ya kan bari saboda Mommyn tana yi musu campaign a lamarin Abba, sai ita kuwa Mama duk maganganu da Mommy take mata akan Abban amsa d’aya zuwa biyu take bata kullum ‘Allah ya zab’a mafi alkhairi’ ko kuma tace ‘ita fa ta riga ta hak’ura da Abba har abada! Ba akan dalili d’aya ba sai akan dalilai barkatai’. Amman duk hakan bai sanya Mommy ta hak’ura ba, haka nan suke fama kullum......... Yau sauran kwana uku d’aurin auren! Su Hudam basu samu komawa wajen Mama ba sai a yau d’in. Kafin su wuce Abba ya nemi ganinta.. Kamar ko wanne uba haka nan ya zaunar da ita yayi mata nasiha mai ratsa jiki! Yana hawaye tana kuka haka su Sudais suma da suka zo yi mata sallama… A haka dai ba dan suna so ba suka yi sallama Abba ya sanya mata albarka. Mommy da kanta ta kaita har gidan Shuwa gaban Mama Hudan tayi mamakin ganin baki y’an Maiduguri da suka zo dan gidan a cike tap! Suka tarar anata hada hada. A yau d’in zasu fara event! Dan haka suna isa suka tarar har mai kwalliya ta k’araso tana jiransu, waensu a cikin friends d’in su ma duk sun zo, da yake mai kwalliyar da tayi mata ita ce za tayi musu saboda Arshaad Maiduguri style yayi..duk shi ya biyawa friends d’inta kud’in makeup da anko. M T Tunda Mommy ta warke kullum itake ce take yiwa Aslam girki… Wani special kulawa take bashi amman ta rasa dalilin damuwarshi dan ko jiya ma sai da Doc ya zo ya dubashi kuma ya tabbatar musu jininshi ya k’i sauk’a instead ma k’ara hawa yayi! Sannan ga zazzab’insa shima ya dawo. Gaba d’aya hankalinsu duk a tashe yake, dan sun rasa gane kan Aslam kwata kwata. Arshaad tun yana kulashi, yana tambayarshi meke damunshi yana lallab’ashi, har ya zo ya hak’ura kawai ya watsa shi a kwandon shara Dan Arshaad d’in gani yayi kamar ma Aslam d’in haushinshi yake ji! Idan ma yana waje Arshaad d’in ya shigo kawai sai dai ya tashi ya fice ya bar mishi wajen, ko magana baya so ta had’asa da shi! Kamar ma wanda yake k’ok’arin yin gaba da shi ta k’arfi da yaji! Shiyasa Arshaad d’in kawai ya rabu da shi amman a chan k’asan zuciyarshi mamakin abubuwan da Aslam d’in yake mishi a wannan lokacin da ya kamata yafi kowa tayashi murna, yake yi. Hatta Dad Abba da Daddy sun lura da hakan, basa son shiga tsakaninsu tunda sun fi kusa shiyasa kawai suka zuba musu ido a ransu suna mamakin mai ya had’a best friends haka??……. Da yamma, Mommy na d’aki tana jera kaya a wardrobe Dad ya shigo.. A bayanta ya tsaya yayi hugging d’inta. A hankali tayi murmushi kafin ta juyo still yana rik’e da ita tace “ina wuni Dad” Murmushi shima yayi mata yana jin tsananin k’aunarta tana nunkuwa a cikin zuciyarshi, a hankali yace “Bayan waennan akwai wasu kuma da kike buk’ata??” A hankali ta girgiza mishi kai alamun ‘a’a’. Ajiyar zuciya ya sauk’e, kafin ya jawo hannunta suka nufi gadon dake d’akin. Sai da ya zaunar da ita shima ya zauna a daff da ita tukunna yace “Aisha, magana nake so muyi dake ta gaskiya da gaskiya” Da sauri ta mik’e tana k’ok’arin kawar da kanta daga gareshi kafin tace “Not again Dad, na gaya maka ban tuna komai ba, please Dad ka bar maganar nan.” Mik’ewa shima yayi ya sake rik’o hannunta kafin yace “Look at me kice mini ‘wallahi Dad ban tuna komai ba‘.” Hannunta ta fara k’ok’arin kwacewa a cikin nashi ta had rai sosai cikin fushi tace “Tunda baka yarda da ni ba, shikenan!” Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace “Jiya da yamma kin manta wayarki a d’akina kin tafi kitchen, naje kai miki wayar saboda a nata kira.. I didn’t mean to eavesdrop but i have no choice! Naji komai maganan ku da kuka yi ke da Asabe!.. Mai yasa kika b’oye min?”. Gabanta ne ya yanke ya fad’i! A hankali ta tsaya tayi tsit ta nutsu ba tare da tace komai ba, sannan ta kasa d’agowa ta kalleshi… Hannu yasa ya kamo hab’arta ya juyo da fuskarta ya d’ago fuskar, da sauri ta runtse idanuwanta. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa kafin a hankali yace “Maimaita min abinda ya faru that very day da kika fad’o, waye ya turoki?! Ina so inji daga bakinki, don’t lie, kin san naji komai.. Kawai i want you to tell me.” A hankali tace zan fad’a maka amman sai ka yi min rantsuwar ba zaka fad’awa kowa ba sannan ba zaka nuna ko da a fuskarka ne ba.” Cika fuskarta yayi cikin fad’a yace “Ba zan iya ba Aisha! Ya zama dole in fad’a sanann in nuna fushi kuma in d’auki mataki! Dole ne in hukunta mai laifi! Kin san irin ciwon da kika yi kuwa? Kin san irin wahalar..” Cikin katseshi tace “To kaga dalilin da ya sanya na b’oye maka ko?” Cikin karyewar zuciya taci gaba da cewa “I have lost a lot, shekaru sun jaa.. Na ci burin yiwa y’ay’ana tarbiyya especially ma Aaima da ta kasance mace amma kalli fa duk nayi missing Mai ya rage yanzu?. Ni za kayi wa abun nan ko? A kaina kake so ka hukunta me laifin ina? To ni d’in nace ‘na yafe har abada har gaban abada!’ Meye kuma na dawo da abunda ya riga ya wuce??. All i need to do now shine ibada dan kwata kwata ban gamsu da sallolina da kuka ce inayi ba, Nafilfili da ibada su kawai nake buk’atar inyi a halin yanzu, ba wai case da holding grudges ba! I want peace.” A hankali ganin ya d’an nutsu yana kallonta kawai, ta kamo dukkannin hannuwanshi biyu ta rik’e tace “Dad, duniyar ma duk nawa take? Idan fa mukayi hak’uri ma duk mutuwa za muyi! Yanzu idan kace zaka d’auki mataki wallahi square one zamu koma, mutane ba za su tab’a duba laifin da aka yi mini ba instead gani za suyi kamar ka fifita ni ne wanda fifita Aslam da Granpa yayi tun farko ni na tabbatar shiyasa aka zamo silar zabgemin kusan rabin rayuwata haka nan na yi ta a wahala! Please dan Allah let it go, for me..” Mommy ta dad’e tana kwantar mishi da hankali, da nuna mishi ita kwanciyar hankali kawai take buk’ata yanzu, tukunna da kyar da mugun kyar ya yarda da buk’atarta akan ba zai yi komai ba, kuma ba zai nuna ba ko a fuska! Tukunna a hankali ta hau fad’a mishi abunda yaji tana fad’awa Gwaggwo Asaben..... In banda ajiyar zuciya ba abunda Dad yake sauk’ewa a jejjere… Ji yake kamar ya mutu dan tashin hankali da takaici gashi ta saka shi yayi mata alk’awari. A haka Aslam ya shigo ya samesu.. Tabbas ya lura akwai abunda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96