Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Mama ko wani zai yi mishi maganan Arshaad amman yaji shiru shiyasa shima yana yiwa Maman ‘ya jiki’ ya fita, dan baya so suyi mishi d’in, but ya tsara a ranshi zai gayawa matarshi, duk abinda ya sani, da kuma dalilin yin shirun da yai, saboda kar ayi mishi kallon munafuki. Sai da suka biya duk wani bill sannan suka tafi a lokacin an tafi da mama yi mata eco. Su Kaka ma shirin tafiya gidan su Abba suka yi, aka bar Baaba Talatu. Sai a sannan ne Baba yazo, ganin Maman bata nan yasa suka gaisa da Baaba Talatu ya wuce kasuwa akan zai dawo da azahar in shaa Allah. Su Kaka basu samu damar zuwa gidan su Abba ba, sai la’asar, a sakamokon kiran da aka yi musu akan results d’in da ya fito, dangane da case d’in Junaidu......... Yadda Hudan taga rana haka taga dare, Gwaggo Asabe har mamakinta take yi dan duk juyi in tayi sai taga idonta biyu! Gaba d’aya ta kasa bacci ta k’agu Safiya tayi taje taga jikin Maama, da taga safiya ta k’i yi k’arshe kawai mik’ewa tayi taje ta d’auro alwalla, tazo ta fara jero nafilfili. Tana idar da sallar asuba kuwa bayan ta gama Azkar ta d’anyi karatu, ta shiga tayi wanka. Tana fitowa ta tarar Gwaggo Asabe bata d’akin, hatta sallayar data barta akai ta nad’e. Doguwar rigar da Gwaggo Asaben ta bata jiya had’e da Maclean da brush sabbi ta d’auka ta sanya, luckily ta samu comb a d’akin cikin drawer, dan haka ta goge shi da tissue sannan ta sa hannu ta zare ribbom d’inta ta hau ware tufkar da ta yiwa dogon gashinta wanda yanzu har ya kai tsakiyar bayanta….ita kanta tana mamakin yadda ya tofo a cikin shekara uku! Bayan askin dolen da Ya Jalila tayi mata… Tunawa tayi da Jalila wadda Sakina tayi mata k’us k’us d’in Khadija tace mata ‘kamar ciki ne da ita( Jalilan)’ amman Umma tayi k’arya tace ‘ta tafi jinyar Hansai’. A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya a ranta tana adduar ‘Allah yasa ba cikin ne da ita da gaske ba’ ….abunka da zuciya mai kyau! gaba d’aya duk sai taji tausayin Yayar tata ya lullub’eta, don haka ta hau yi mata addua da fatan alkhairi, tanayi tana taje kanta. Sai da ta gama tsaf, ta d’auko ribbon d’in ta tufke gashin a d’an k’asan tsakiyar kanta kad’an! Ganin yadda jelar take reto ne ya sanya ta kanannad’e gashin waje guda ta tura ta had’e da ribbon d’in, d’ankwalin doguwar rigar ta d’auko tayi style d’in V da d’aurin very simple amman ba karamin kyau tayi ba, ga gashin data duk’unk’une ana iya hango santsi da kyallin shi da uban yawa dan d’ankwalin k’aramine sosai so bai gama rufewa ba. Ta d’auko wayarta kenan zata kira su Mama ta ganta a kashe, ba chargi. Ajiyar zuciya ta sauk’e, daman ta san za ai haka, dan tun jiya chrgin ta yayi low sosai. Zama tayintana jiran Gwaggwo Asabe ta dawo ta ari wayarta ta kira su Mama don duk ta haddace nambobin su. Kusan minti arbain taji shiru.. ga anxiety yana neman kashe ta! Shiyasa ta yanke shawarar mik’ewa, ta hau nemanta. Bata wani sha wahalan neman nata ba, dan tana fitowa daga d’akin taji k’amshi ya cika ko Ina a gidan wanda hakan ne ya tabbatar mata da inda take(Gwaggwo Asaben), dan haka ta nufi k’asa. A k’ofar kitchen d’in suka had’u da Gwaggon, da tray a hannun ta, da kuma tea flask da ta rik’e da kyar. Sai da Hudan da d’an rissinar da kai tukunna ta gaisheta. Da kulawa Gwaggo Asabe ta amsa… Har ga Allah ta dad’e bata had’u da Yarinya mai hankali da nutsuwa irin Huda ba, ga kyau tubarkallah…shiyasa lokaci guda suka saba, taji ta shiga ranta sosai! Har k’asan zuciyarta take yiwa Aslam d’insu kwad’ayin auren Yarinyar saboda ta had’a komai ga kyau ga hankali ga nutsuwa gata y’ar uwarshi! Sai dai kuma yadda taga Arshaad yana shige mata sosai, watak’il shi ne zai fara cewa yana sonta, dan jiya ta lura har wata y’ar hira suka tsaya yi a parlour, sai wani nan nan yake yi da ita….. Hannu Huda ta saka tana k’ok’arin karb’ar tea flask d’in dake hannunta wanda hakan ne ya katse mata tunanin ta! Ba musu ta sakar mata , dan itama tana jin yadda ya kusan fad’uwa. A tare suka nufi hanyar sama, tana gaba Hudan na biye mata baya, wata hanya suka kuma d’auka bayan sun shanye stairs d’in, nan ta sake hango wani bene, benen suka bi suka hau, suna kaiwa k’arshe suka tarar ta wata y’ar k’ofa A bud’e k’ofar take hakan yasa suka shige, dogon corridor ne sosai, sai k’ofofi biyu, d’aya a farko farko hanyar dama, d’ayar kuma a kusan k’arshen dogon corridor d’in ta hannun hagu, Wadda itan taga Gwaggwon ta nufa, sai da suka iso bakin k’ofar, tukun suka tsaya! Rik’on tray d’in Gwaggwo Asabe ta gyara sosai a hannu d’aya sanna tasa hannu tayi knocking, tukun taja ta tsaya, ta gyara ruk’on tray d’in. Kusan minti biyu tukunna suka ji ance “come in” Hudan ta kalla tace “tayi amfani da empty hand d’inta ta bud’e musu.” Hakan tayi, bayan ta murd’a handle d’in a hankali ta d’an tura sai kuma ta matsawa Gwaggo Asabe don ta fara shiga.. Murmushi Gwaggon Asabe tayi sannan ta shige Itama Hudan ta bita a baya. Sai da ta rufe k’ofar tukun ta juyo ta fara kallon d’akin…. “Ma shaa Allah” tace, a ranta. Ba zaka kirashi d’aki ba kuma ba zaka kirashi da parlour ba, ga set d’in kujeru har da k’aramin dining, da makekiyar tv d’in da bata tab’a ganin irin ta ba, ga kuma set d’in gado shima komai akwai, royal, light blue da fari haka colour d’in kujeru da gadon suke, hatta pentin d’akin haka yake. Ga kuma wani glass door, wanda kana iya hango swimming pool da shuke shuke da kujerun shak’atawa. K’auyanci ta fara, don a ranta ta hau rayawa “daman ana pool a sama? saman ma ta biyu! Ita tunda take bata tab’a ganin d’aki mai girma sosai da kyau irin wannan ba!”…… Tunanin ta ne ya katse jin Dad yana cewa “Hudan k’araso mana ya kika tsaya a k’ofa?”. Sai a lokacin hankalin ta ya kai kan Dad, da wata mata a zaune a gefen shi yana rik’e da hannunta. Ji tayi kamar ta rusa kuka!! Da ta san gurinshi Gwaggo Asabe zata zo da bata biyo ta ba, kenan ita duk b’uyab da takeyi ma a banza, tunda gashi a gidanshi ma ta kwana ba tare data sani ba, kuma yadda ya nuna it’s like ya san tana nan d’in, shikenan ta san yanzu zai kira Abba shi kuma ya hanata zuwa taga Mama. Gwaggo Asabe ce ta katsemata tunani jin ta sake cewa “Huda k’araso mana.” A hankali take takawa izuwa bakin gadon inda suke… Taji Dad yana cewa “Ashe da gaskiyar Abba, daman ya ce tana wajensu Aslam ni ban yarda ba, sune suka kawota jiyan ko?” D’an murmushi Gwaggo Asabe tayi kafin tace “Eh jiya lokacin da ka kira ni, Arshaad bai dad’e da kawota ba, shi ya rakota.” Hudan dake jin su

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});