Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 44

Chapter 44

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba?” “Abun mamaki ko? Suna tare amman basu gane junan su ba!” Daddyn ya fad’a, kafin ya ci gaba da cewa “Ya yiwa Dad ma maganar! Wallahi baka ji yadda lamarinnan yayi mana dad’i ba! Ni kam na riga ma na bashi ita.” Ya k’arashe maganar yana murmushi mai kama da dariya wanda ke baiyyana tsantsar farin cikin da yake ciki. A hankali Abba yayi k’arfin hali ya d’an k’ak’alo guntun murmushi kafin yace “Tou Allah ya zab’a mana mafi alkhairi” Ameen Daddy yace sannan ya juyo ya kalli Aslam wanda ya runtse idanunsa ya kwantar da kansa da bayansa a jikin kujerar! Cikin zolaya Daddyn yace “wannan azumin da kaina zan buga maka wak’ar gauro!! Arshaad yayi maka wayo..” D’an murmushi kawai yayi ba tare da ya bud’e idanunsa ba. Abba baya son maganan shiyasa ya sako wata maganar daban dan haka suka hau tattaunawa…… Shi kam Aslam mik’ewa yayi yayi musu sallama ya kama gabanshi. A b’angaren Hudan kuwa bayan sun gama dabdalar assignment d’insu dasu Sudais ta tafi d’akinta, tana kwanciya bacci mai nauyi yayi gaba da ita. Sai wajen 1:30 ta samu ta farka. Alwalla tayi tayi sallah, sanin da tayi ba a gida za tayi sallar laasar ba ya sa ta karanta izu hud’u, tayi doguwar addua ta tofa, itama ta shafa. Tana idarwa Shuraim yazo ya kirata yace “taje inji Abba, yana parlour” Jikinta ba kwari ta fito, dan still ta sake gwada number Ummu tana shiga amman tak’i d’auka! Gashi har yanzu Sakina itama bata kunna wayarta ba, ba kuma ta k’araso ba, Allah yasa ba hanata aka yi ba!. Tana wannan tunanin tana tafiya domin amsa kiran Abban nata. A parlourn saman inda sides d’insu yake ta sameshi. Tun daga yanayin ta ya fahimci tana cikin damuwa.. Ajiyar zuciya ya sauk’e bayan ya amsa gaisuwar ta kafin yace “Zauna, i want to talk to you” Zama tayi, a one seater d’in parlour da yayi mata nuni da. Ba tare da b’ata lokaci ba , ya fara magana “D’azu Daddy yake cewa wai Arshaad ya sameshi akan maganar ku!” Da sauri ta d’ago ta kalleshi, a zuciyarta ta hau mamakin Arshaad da kalar nerve d’inshi! Despite abunda yayi da kuma fushin da suke yi da juna amman shine yaje ya samesu da maganan! Me kenan yake so? Auren yakeso ayi ko tanaso ko bataso kenan ko me!?…. A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa, jin Abban ya sake cewa “Yace wai you two knew each other for a while ko?” Sai da ta taushi zuciyarta, tukunna ta iya d’agawa Abba kai alamar ‘eh’ sannan ta bashi labarin yadda Arshaad d’in ya kaisu makaranta… Hatta wayoyin daya siya musu sai da ta fad’a mishi bata b’oye komai ba a labari da tarin alkahairan da yayi musu tun daga had’uwar su har kawo yanzu. Dan ita bata kasance mai manta alkhairi ba kwata kwata. Tanaso ta fad’a mishi issue d’inshi da Jalila amman sai ta kasa. Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e bayan ya gama jin bayaninta ya na k’ok’arin fassara lamarin Arshaad amman ya kasa! Tabbas akwai abinda Arshaad ya sani tun farko kuma yayi shiru wanda shi kad’ai ya san dalilin yin shirun da yayi! Dan a cikin labarin da Huda ta bashi yanzun yaji inda Arshaad ya had’u da Mama ba so d’aya ba, and in dai Arshaad ne ya tattare mishi d’akinsa kwanakin baya da za suyi parking ya kai personal kayayyakinshi gidanshi na kwandila, tou tabbas ya san wacece Huda! Ahankali yaji tace “Amman Abba yanzu bama tare mun yi fad’a sosai..” Ta k’arashe maganar ta na kuma yin k’asa da kanta. Murmushi Abban yayi kafin yace “Ai kuwa ke kad’ai kike fad’anki! Don shi gashi yazo yana binmu one by one yana expressing how much he loves you.” Da sauri tasa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta… Tashi d’aya Maryam ce ta fad’o mishi arai, yanayin kunyarsu iri d’aya ce, kalli fa fad’a tace sunayi amman kuma anyi magana ta hau jin kunya…. Murmushi yayi kafin yace “Kije ki shirya dan na san yanzu Auwal zai zo, Shuraim yace min “zai bada hadda yau a islamiyyarsu da suke zuwa duk asabar da lahadi so nan zai je shi ba zai samu daman binku ba. Sai kuje da ke da Sudais kawai.” “To” tace, sannan ta mik’e, har tayi gaba sai kuma ta juyo Tace “Abba Allah da gaske nake yi munyi fad’a dashi, fad’an gaske!” Dariya ta bashi ganin yanda ta dage akan ita fa sun yi fad’a, amman ko a cikin bayaninta, yadda take yabon Arshaad d’in, ya sanya ya fahimci still tana son abunta. Murmushi kawai ya sake yi yace “Tam na yarda kun yi fad’a, shikenan.” Ahankali ta juya ta wuce don taje ta shirya. Lumshe idanunsa yayi ya kwantar da bayanshi da kanshi jikin kujerar... .....Zai fara yin magana da Arshaad first! He just hope yanada kwakkwaran reason ba munafuntar su yayi ba all this time.. Saboda in dai hakane tou gaskiya zai murzawa idanunsa toka, ya hanashi Huda! Dan ba zai bari y’arsa ta rayu da Namiji mai b’oye b’oye ba. Ya lura da tana sonshi, so yana adduar Allah yasa Arshaad d’in ya zamana yanada reason d’in da zai kare kanshi kwakkwara! Zai yi farin ciki da hakan domin kuwa ya san that’s wat she wants.. Dukda kuwa yana da wani buri da ya d’aura akanta tun lokacin da ya fahimci yanada y’a mace mai shekarunta amman tunda he’s late ta riga ta zab’i Arshaad, shikenan ba komai, yana yi mata fatan alkhairi….. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 43. Cikin nutsuwa ta shirya ta d’auki y’ar k’aramar jaka da wayarta ta fito. Bata samu Abba a wanann parlourn ba! Dan haka ta sauk’a chan k’asa cikin nutsuwarta… Tun kafin ta k’arasa ta hangoshi shi da Sudais wanda shima har ya shirya da alamun ita yake jira. Har ta sauk’o Abba bai lura ba, yana nan ya dulmiya duniyar tunani….surutun Sudais ne ya d’an dawo da hankalinshi parlourn, dai dai nan kamar had’in baki Auwal ya shigo.. Riga da wando ne a jikinshi, rigar maroon mai dogon hannu da black jeans asalin crazy! Ga wani had’add’en takalmi sau ciki mai mugun kyau black! D’azu uban gashi ne a kanshi amman yanzu yayi sabon aski an aske gefe da gefe da k’eyar an bar tsakiyan (saman kan) lallausar sumar ta taru a kanannad’e iya tsakiya sai shek’i take yi, gefe wajen kunnenshi na dama ta sama inda aka aske an sake bi anyi wani style kamar zigzag, asalin farar fatar kan nashi ta baiyyana ta fito da design d’in radau!! Ga wani bracelet kamar sark’a a hannun daman shi, sannan ya maka wani arnen bak’in glass mai shek’i wanda kana gani kasan mai mugun tsada ne…… Yana shigowa k’amshin turarenshi ya gauraye ko ina. Tafe yake yana danna waya, har ya k’araso cikin parlourn bai ma lura da su Abban ba. Da Hudan ya fara lura kasancewar ta a tsaye sai kuma sudais wanda ya k’arasa wajenshi da sauri yace “Ya Auwal har da wannan wajen nan zaka kaimu ko? Wanda ake sa glass ayi game..” Dariya yayi ya d’an sa hannunshi akanshi ya hautsina y’ar sumar data d’an tarar mishi ba sosai ba sannan

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});