Chapter 83
Chapter 83
zuciya Mom ta sauk’e tana ji kamar ta shak’e Mommy ! ‘Wato irin ita har ta jone da Maryam d’innan’. Mammy na shirin yin magana Arshaad wanda ya ga b’oye b’oye shi ba inda zai kaisa dan kwata kwata ya kasa shawo kan Mammy kuma yana ganin in dai ya gayawa Mommy maybe a samu sauk’i ta hanyar Dad da Gramma ne, yace “Mommy cewa tayi ko a fasa auren ko ta tsine min” Da sauri Mommy tace “Whatt!!” Cikin firgici kafin ta juya kan Mammy tace “Rukayya wanne aure kike so a fasa?” Ba tare da b’ata lokaci ba cikin b’acin rai da tarar numfashin ta tace “Auren Huda da Arshaad, Aisha! Shi nake so a fasa Idan kuma kina da ja to sai in ji...” Sai a sannan Aslam ya d’ago ya kalleta, bata san mai ya faru ba amman sai Yaron yayi mata kwarjini ta kasa ci gaba da magana. Mommy ta yunk’uro za tayi magana kenan taji Aslam d’in ya rik’e hannunta, ba tare da yace mata uffan ba kawai ya juya da ita suka fara tafiya. Har suka fice a parlourn bai ce uffan ba ita kuma bata yi mishi tirjiya ba, sai da suka isa tsakiyar compound d’in tukunna ya zaro waya ya danna kiran Dad! Ba tare da b’ata lokaci na ya gaya mishi halin da ake ciki… Suna gama wayar, ya ga tana k’ok’arin komawa A hankali yace “Mommy please kar ki koma ciki, kina jin fa yanda take yi miki magana ba respect. Please dan Allah kar ki je.” Za tayi magana yace “Please Mommy, i can’t take it” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin a hankali tace “To kaini gidansu Huda. I have to be there, suna ta expecting d’inmu.” Da k’arfi yaji zuciyarshi ta buga ! Sai kuma yaji zafi kamar an soka mishi wuk’a… Sai da ta sake maimaita maganar tata tukun yace “Tam” Daga nan suka fara tafiya suka wuce inda motarsa take a chan wajen gidan, suka shiga suka wuce. A chan parlourn kuwa Zuwa wannan lokacin gaba d’aya hankalin matan parlourn ya koma kan su Mammy. Su Mommy suna fita Ummi ta hau lallab’a Mammy tana bata baki, basu kulata ba sam daga ita har Mom dan tun a cell daman sun fita harkarta saboda ta zama wata salaha doluwa wawiya! kamar ba ita ba. Arshaad kuwa ji yake kamar ya chaka wa kanshi wuk’a! Babu abunda yafi d’aga mishi hankali kamar kalmar ‘sai ta tsine mishi’ da taketa faman ambata, hakan yasa kawai ya juya zai bar wajen suka yi karo da Dad! Fuskarshi sam babu alamun annuri dan hatta Arshaad d’in sai da ya d’an tsorata da yanayin shi. Ganin yana shirin fara zuba musu tujara a gaban jama’a ne ya sanya Mom tace “Dad da mun d’an shiga daga ciki ko mu hau sama Kalla kowa ya zubo ido mu yake kallo” Juyowa yayi yana kallonta wanda hakan yasanya ta sha jinin jikinta. Da kakkausar murya yace “Granpa ya san kina nan?” A hankali jikin a mace ta girgiza kai, Snapping fingers d’inshi yayi kafin ya nuna mata hanyar main door straight! Ba k’aramin sanyi jikin Mom yayi ba! Kunya da takaici kuwa kamar su kashe ta, a hankali tace “Sai anjiman ku” daga nan ta fara k’ok’arin wucewa taji Ummi tace “Adama d’an jirani in je in d’auko wayata a side d’in Granpa In zo mu wuce. Ya sallameni tun jiya.” Ba tare da Dad ya kalleta ba yace “Ki jirani zan maidake anjima, ina son ganinku tare, ke da Abba.” “Ok” kawai tace Mom kuma ta wuce ta fita. Sai a sannan Dad ya kalli Mammy yace “Magana d’aya zuwa biyu nake son gaya miki… Na farko shawarace Na biyu kuma zan iya kiranshi as treat.. Ki kwantar da hankalinki ayi auren Hudan da Arshaad cikin lafiya da kwanciyar hankali Ko kuma wallahi idan kika yi wani abun da ya b’ata auren nan tou ki tabbatar sai na sauk’e igiyoyin aure na da suka yi saura a kanki.” Yana gama fad’in haka ya juya ya wuce. A rikice Aaima da sisters d’in Mammy suka hau cewa “Kawai ta hak’ura dan Allah kar ta b’ata aurenta” Bata bi ta kansu ba, cikin b’acin rai ta kalli Arshaad tace “Arshaad kaje ka cire waennan kayan na gaya maka babu inda zaka je! Wallahi idan ka fita a gidannan yau ni da kai ne.” Daga haka ta juya ta wuce sama. Sai a sannan Hajiya Binta ta k’araso tanajin abinda tayi tace “Suje kawai a sallami y’an wuni suma su zo su wuce gida tunda ba za a je kaulun ba!” Nan take gayamusu ma sak’on Mahaifiyarsu da tace a fad’a musu… Jiki a mace haka duk suka bar gurin aka je aka rarraba souvenirs d’in k’atuwar jaka an rubutu sunan Amarya da Ango a jiki a cikin jakar an zuzzuba turaruka da atamfofi guda biyu da vail da jaka da takalmi, a each bag.......... Mom, bata tab’a tunanin Dad zai iya yi mata hakaba! Wai me ya shigi mazan estate d’in nasu ne da duk suka bi suka rainasu suka tsanesu haka? Daddy ne kawai yake musu mutunci yake tausayinsu amma hatta Auwal da Arshaad sun renasu Aslam kanshi tana gani d’azu yanda yayi musu sannan ya wani ja hannun uwarshi suka fita Ala dole shi mai zuciya! Inaa, gaskiya rayuwa fa ba zata yiu a haka ba, dole su gyarawa mazan MT zama dan yanzun taga wani tashen rashin mutunci suke yi especially Abba, ta kanshi zata fara wallahi! Wannan shine damuwar da ya kamata su tsaya su magance ba wai shirmen Mammy na hana auren Arshaad ba! Abunda sai sun so ma tukun Hudan zata zauna a gidan Arshaad d’in! Bata san me yake damun Mammy data kasa fahimtar simple abu ba....... Ji tayi kawai an yi hugging d’inta A d’an razane ta zare wadda tayi hugging d’in nata tana shirin cewa wani abun suka yi ido biyu da Jalila.. B’ata rai tayi tamau ta tamke fuskarta. Jalila ta lura da hakan sarai amman ta manna mata hauka cike da shak’iyanci tace “Oyoyo Mom d’inmu ashe kin dawo ni banma sani ba. Dama wallahi zaman gidan su Gwaggo Asaben chan ya dameni, girkin kuku fa nake ci baki ga har na rame ba? Yanzu kuwa tunda Allah ya dawo dake na san k’ibata zata dawo. Taho muje, ko kayana ba zan d’auka ba wallahi Auwal yaa zo ya d’auka anijima, k’afata k’afar ki, mu tafi. Ashe alkhairin ganin ki ne yasa naji ina kwad’ayin lek’owa nan dan tunda naji Gwaggwo Asabe tace ana biki anan na kasa sukuni.” Lumshe ido kawai Mom tayi, sai da ta tabbatar da zuciyar ta ta dedeta tukunna ta bud’e idanuwanta da sukai ja ta zubasu akan Jalila wadda tayi mata k’urr! da ido. “Muje” Shine kawai abunda Mom d’in tace, ba tare data sake bi ta kanta ba tayi gaba Jalilan ta bita a baaya daman neman wanda zata k’untatawa take yi ta san watak’il ta samu tashin hankalin da take ciki ya d’an ragu! Duk da Umma ta bata assurance d’in ‘ba matsala an tabbatar mata da babu aure tsakanin Huda da Arshaad dan haka kar ta damu da wani bikin da suke ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96