Chapter 41
Chapter 41
rintsa dan ni ba anan zan kwana ba Baba nake jira yazo ya d’auke ni sai gobe tukun zan dawo. Amman na san yau rikici zata yi tayi, Mama ta zama mai fad’a sosai!. Maganar da zan fad’a mata kuwa, gaskiya ce zan fad’a kawai ba wani abun ba.” Rau rau Huda tayi da idanu. A hankali Sakina tayi murmushi tace “Kije ku tafi, tabbas Mama za taji ba dad’i amman kije kawai kin ji?” A hankali ta share hawayenta ta matso ta rungume Sakina, dai dai nan Baban su Sakina shima ya k’araso wajen. Abba ma haka wanda tun fitowarta ya gansu ganin da yayi kamar bata ganshiba ne yasa ya fito ya k’araso inda suke tsaye. Kusan a tare suka k’araso wajen, Baban su Sakina yana ganinshi ya gane shi ne baban Hudan dan haka yayi saurin mik’a masa hannu (wani aiki ya tab’a had’ashi da Abban kuma ya samu alkhairi sosai! Har gidansa ma sukaje suka yi mishi godiya. Yanata yaba alkhairin mutumin, shiyasa da Arshaad ya rok’esa akan ‘ya rufa mishi asiri kar ya fad’awa kowa daga family d’in daya fito yet saboda gudun matsala’ Shi kuma ya yarda yayi shiru bai fad’a d’in ba Don yaga sun san mutunci kuma shi kanshi yana so Hudan ta had’u da Mahaifinta a samu a dedeta komai! Amma Arshaad yace baya nan yanzu ya tafi wani aiki kuma akwai issue har yanzu a k’asa, but a hankali a hankali za suyi settling in shaa Allah, komai ya dawo normal . Shi kanshi a lokacin ya yarda da hakan saboda ya san wani part na case d’in su Madu da family d’in Abban… To kuma suna k’ok’arin ganin komai ya koma normal d’in tukun a samu a daidai sai shi kuma Aslam yazo yayi musu mai gaba d’aya!).... Shima Abban kallon sani yake yi masa, sai da Baban su Sakinan ya tuna mishi ‘ya tab’a basu wani contract kwanakin baya’ Tukunna Abba ya tuna shi, Hudan kuma ta gabatar masa dashi a matsayin Baban su Sakina mijin anty d’inta. Sake gaisawa suka yi sakina itama ta gaidashi cikin girmamawa… kallon Abban take yi tana sake maimaitawa! Tanaji Ummu tana cewa ‘Baba kishi yake da Abba shiyasa yake yin wasu abubuwan’ tabbas kam dole Baba yayi kishi da wannan mutumin! Dukda cewa shima Baban ba mummuna bane kuma fari ne shima amman ko makaho In ya shafa yaji ya san babu had’i kwata kwata tsakanin Abba da Baba, Abba ya tsere mishi a komai da komai.. Gashi wani abun mamaki ba zaka tab’a cewa ma ya haifi Hudan ba dan kamar wani d’an 33 haka yake, jikinsa san bai nuna tsufa ba kamar dai Mama, Ita kam tunda take a rayuwarta bata tab’a ganin perfect match irin na Abba da Mama ba…… Da kulawa ya amsa gaisuwar tata yana tambayarta “ya school” a hankali tace “muna jiran results ne har yanzu”. Sun d’an tab’a hira da Baban Sakina daga nan sukayi exchanging numbers suka yiwa juna sallama. Abba ya lura da yadda Huda ta shak’u sosai da Sakina dan har suka isa mota tana waigawa tana waving d’inta kamar wata Yarinya itama Sakinan haka dan ita kam har sai da taga fitarsu tukunna suka shige ciki don su d’auko kayanta. Tun kafin Mama ta gama gaisawa da Babansu Sakinan ta san yanda tayi ta zulle ta gudu, daman itama k’arfin haline kawai zata yi wajen yiwa Maman bayani kuma yanzu ga mafita Allah ya kawo mata. Tunda suka kama hanya Hudan take tunanin abunda tayi sam bata kyauta ba! But ya kamata shima Mahaifinta ta d’an kwantar mishi da hankali tunda ga halin da yake ciki da family d’inshi…. Ya lura da ita sosai, don k’arshema har da y’ar kwalla yaga tana gogewa. Shiru yayi mata kawai…..har sun kama hanyar gida sai kuma ya juya yayi hanyar dominos. Suna zuwa yayi parking ya shiga bai dad’e ba ya fito da Ledoji nik’i nik’i dangin su ice cream da milk shake da pizza….. A baya ya saka ya zagayo ya zauna yace “gashi ita da su Shuraim, in kuma sun yi bacci by the time da suka gidan sai ta sa musu nasu a fridge.” Godiya tayi masa, daga nan suka kama hanya, yana ta d’an janta da hira kad’an kad’an, yace if “she’s bored gobe ta shirya Arshaad ya kaisu munjibir park” Kamat zata ce masa a’a sai kuma tace “to” kawai. A haka suka karasa gida. Shi ya taya ta d’aukar kayan sai da suka isa chan sama tukunna ya ajjiye a parlour yayi hanyar d’akin shi bayan ya rarrage fitulu yana ce mata “ta duba su ta shafa musu addua idan sun yi baccin, itama tayi kafin ta kwanta.” Kamar yanda tayi tunani, ko da taje su Shuraim d’in har sun yi bacci dan haka tasa a fridge d’in sama dan ita tsoro take ji ba zata iya sauk’a k’asa ba, a Iyaka saman ma itakam duk a tsorace take!. Tana jera kayan tana mamakin uban yawansu…. Ice cream d’aya ta Iya d’auka, dan gaba d’aya bata da laka a jikinta tunanin Mama take tayi..duk jikinta a sanyaye yake, ta san tayi laifi babba a Mama, bata san ma ta ya zata sake facing d’inta ba! Cokali biyu kawai ta iya yiwa ice cream d’in duk dad’in shi amman sai ta kasa sha, da kyar ma ta iya had’iye biyun a mak’oshinta don haka ta rufe ta saka a d’an mitsitsin fridge d’in gefen gadonta ta mik’e tayi wanka. Tana fitowa ta rarumo waya ta danna kiran Sakina Ita kuwa Sakina tunda suka fita tana zama a mota ta kashe wayarta ma gaba d’aya dan wallahi ta gaji dayawa tana buk’atar isheshen bacci, in yaso duk fad’an da za ayi mata ayishi gobe!. Shiyasa Hudan tayita kiranta amma taji a kashe…. daga k’arshe ta hak’ura tayi cilli da wayar, ta kwanta, gaba d’aya ranta ba dad’i, bata san ya Mama zata kwana ba yau! Kuka ta fara yi, ta dad’e tanayi kuma daga baya ta share hawayenta…. Wayarta taji tana k’ara dan haka ta lallab’a ta d’auka, gabanta ne yayi wani irin mugun fad’uwa ganin sunan Ummu, sai da wayar ta kusan tsinkewa tukunna ta iya d’auka tana karawa a kunnenta Ummu tace “kina gida ne?” “Eh” ta bata amsa. “Waye ya mayar da ke?” “Abba” ta sake bata amsa. “Daman tare kuka zo?” “Eh!” “Tam! Sai da safe.” Hudan tana shirin yin magana taji kit!! A yanke kiran. A daren ta kira layin Ummu yafi sau ashirin amman bata d’aga ba! K’arshema dena shiga tayi. Gaba d’aya hankalinta sai ya sake tashi, sai wajajen 2 tukunna ta samu tayi d’an baccin ta rabi da rabi, kiran sallar farko ta farka. Tashi tayi tayi Nafila ta jira aka kira tayi sallar Asubah… Bata kwantaba sai da tayi azkar d’inta ta fara karatu. Sai bayan gari ya d’anyi haske tukunnna ta d’an iya yin bacci shima nisanshi iya awa d’aya! Wayar Sakina ta sake gwadawa tana tashi but still a kashe. Tana zaune taji kamar ana knocking chan waje k’ofar falo, mik’ewa tayi ta fita taje ta bud’e… Tana bud’ewa taga ashe ragowar kayantane na jiya aka kawo/ Cikin girmamawa maid d’in ta gaidata sanann ta hau shigo mata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96