Chapter 89
Chapter 89
family d’in MT haka suke lefe duk matan gidan da aka tashi aurar su ko wacce sai da aka yi mata kit d’in gold! Yanzu kuma wannan kinga shine jika na farko da yayi aure. Kaii ammanfa wannan Yarinyar ta tako, gaskiya tayi goshi Allah yasa y’ay’anmu a danshinta. Zata sha gata ba kad’an ba! Naji ma kamar ance wai k’asar zai bari ma da ita gaba d’aya!”. Tabbas zuwa wannan lokacin Umma ta daina ganin komai in banda duhu! Maganar ma sama sama ta dawo ji daga nan kuma jinta da ganinta suka d’auke d’iff!! Mutanen wajen kowa hankalinshi yana kan kallon lefe mai abun mamaki da alaajabi Saboda kaff cikin su babu wadda zata ce ta tab’a ganin lefe kwatan kwacin wannan.... Dimmm!!! K’arar fad’uwar Umma ta sa jamar dake kurkusa da ita zabura suka jujjuyo….. “Subahanallah! Mai ya sameta!! D’in da aketa maimaitawa ne ya janyo hankalin mutanen gurin kaff kowa akayi kanta akai mata rumfa...... A zaune Auwal ya tadda shi, a d’akinsa. Ya jinginar da kanshi a jikin gadon ya lumshe idanuwanshi fuskar shi tayi jajawur! Kana ganinshi ka san yana cikin tashin hankali. Auwal bai damu da yanayinshi ba dan shi ganinsa ma da yayi a zaune ko shirin tafiya bayayi shi yafi komai b’ata masa rai! Cikin muryar b’acin rai yace “Haba Arshaad! Ka sa mutane sun tara jama’a kai kawai ake jira kazo ka wani zauna anan, me kake jira? Gaka nan dai a shirye tsaf! Mai kuma ya hana ka tafiya tun d’azun? Nace maka ina zan taho karka jira ni. Ka san yanda hankalinsu ya tashi kuwa? Dagajin muryar Sakina ka san ba lafiya ba! Taso mu tafi da sauri dallah” Wata nannauyar ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin a hankali ya samu ya d’an bud’e lumsassun dogayen idanuwanshi, sai da Auwal ya d’an zabura sakamokon had’a ido da suka yi da Arshaad d’in! Da kyar ake iya hango maroon eye balls d’inshi da suka b’uya cikin jajawur d’in idanun nasa. Sai a lokacin Auwal ya lura da yanda jijiyoyin kanshi suka fito sukai rud’u rud’u! Da sauri ya k’arasa ya zxauna a gefen shi kafin yace “Lafiya kake?? Me ya sameka haka?” Ya jera mishi tambayoyin duk ya rikice. Banda ajiyar zuciya ba abunda Arshaad yake ta faman sauk’ewa yama kasa yi mishi magana Da kyar ya samu yace “Mammy ce ta….” Sai kuma yayi shiru. Cikin firgici da tsoro Auwal yace “Ta hana ka zuwa?? Lumshe ido Arshaad yayi kafin a hankali yace “Har ma auren! Tace idan aka d’aura sai ta tsine min!” A zabure Auwal ya mik’e kafin yace “Innalillahi wa innailaihirrajiun! Shine kuma ka zauna za ka kashe kanka haka? Zama ai bai ganmu ba! Bara in je in samu su Dad in yi musu bayani, idan ta kama har Granpa sai a sa a case d’in. Mai yasa Mammy zata yi mana haka?” Ya k’arashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka. A hankali Arshaad d’in yace “Ba wanda bai sani ba. Kowa ya san da case d’innan. Har mamanta da sisters d’inta duk an bata hak’uri amman tak’i hak’ura.” Wata kakkausar ajiyar zuciya Auwal d’in ya sauk’e kafin yace “Ya aka yi Mammyn ta sani? Last time da naje na dubasu naga kamar duk basu san da zancen ba.. Na san dama suna iya causing problems shiyasa nima ban yi gigin fad’a musu komai ba! Ko maybe Ummi da aka kawo ce ta kirasu ta gaya musu?” Da d’an mamaki Arshaad d’in yake kallon shi kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Baka had’u da Mom ba hala? Sun dawo jiya. All of them” Da mamamki shima Auwal d’in yake kallonshi ya ma kasa cewa komai. A hankali Arshaad ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “Auwal do me a favour.. Ka kira Sakina, inaso kayi mata bayanin komai amman kace kar ta fad’awa kowa kawai a san yanda zaai a gudanar da event d’in ba tare da an jira ni ba! Yanzu na san Mammy idonta a kaina yake dan tun d’azu nake lura tanata turo Aaima tana mata patrol so ba zan iya fita ba. Sakina is smart she’ll know what to do yanzun In shaa Allah ni kuma anjima da daddare za mu je Ina son ganin Hudan na san abunda zan yi. For now amman kawai ka lallab’a mun Sakina tayi handling komai, kafin nan da anjima.” Cike da gamsuwa Auwal d’in ya d’aga kai alamar to sannan ya zaro waya ya fara kiran Sakina. Tun lokacin da aka fara rangad’a gud’a taji dan haka ta mik’e ta lek’a ta windown d’akin Shuwa.. Ji tayi kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha sakamokon hango su su biyu a zaune da ta yi! Bata ganin fuskar su especially Huda da har yanzu tata fuskar a lullub’e take sannan windown a rufe ne kuma sun yi mata nesa.. Bata san lokacin da hawayen farin ciki suka zubo mata ba! Tana gani yanda mata suke zuwa suna d’an d’aga mayafin kad’an suna shafa mata da hannuwanta shi kuma a tafukan hannunshi da goshinsa ake shafawa sannan su ajjiye musu gift a cikin d’an kwanon da aka ajjiye wasu kuma kud’i. Ba k’aramin burgeta suka yi ba, banda kalmar ‘Alhamdulillah’ ba abunda taketa nanata a ranta tana mamakin dalilin da ya sanya Aaima karkacewa ta gilla mata wannan uwar k’aryar haka Wata zuciyar kuma tace maybe an gyara abunne Mammyn ta sauk’o cikin kawar da tunanin a ranta tace “Chan ta matse musu” Sannan ta hau raya yanda zata yiwa Arshaad in sun had’u na k’in d’aukar wayarta da yayi. K’arar wayarta dake kan gado ce ta katse mata tunani dan haka ta isa ta d’auki wayar.. Kamar ba zata d’auka ba ganin sunan Auwal ne sai kuma ta d’anyi murmushi a ranta tace ‘Kar In zama kaza mana’ dan haka ta d’auka ta kara a kunnenta kafin yace komai tace “Gashi chan Ya Arshaad d’in yazo suna zaune ana saka su a lalle. Thanks for your time” Tana gama fad’in haka ta katse kiran. Da mamaki suka kalli juna shi da Arshaad dan a hands free wayar take Shiruu, d’akin ya d’auka chan kuma Auwal yace “Bara inje wajen maybe ko fushi suka yi shiyasa tayi min gatse” Cikin katseshi Arshaad yace “Kaje wajen Mom mana. Kace bama ka san ta dawo ba bayan a gida d’aya kuka kwana. Kaje wajenta daga nan ka d’an lallab’ata may be in tasa baki Mammy ta hak’ura.” Har ya d’anyi gaba sai kuma ya juyo yace “Su kuma fa?” “Kar ka damu na gama tsara komai, zuwa anjima da daddare za muje in shaa Allah. Zan sameka a gida.” Cewar Arshaad yana mai maida kanshi da lumshe ido dan kanshi ba k’aramin ciwo yake yi ba amma kuma har ga Allah y’ar maganar da ya samu suka yi da Auwal ya d’an ji sassauci a ranshi. “Allah ya kaimu” Shine kawai abunda Auwal yace yana me fita daga d’akin da waya kare a kunnen shi still yana sake kiran Sakina sai dai har ya tsinke bata d’auka ba. A tsakiyar main parlourn suka kusa yin karo da Aaima, kasancewar hankalinshi naga wayarshi yana turawa Sakina message. D’agowa yayi yana kallonta itam ma shi take kallo kafin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96