Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 79

Chapter 79

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Ta fad’a a k’asan ranta! Bata san dalili ba amman taji zafin yanda yayi mata, taso ta koma sama kawai abunta amman sai ta tsinci kanta da kwad’ayin bin bayanshi, dan haka ta rufe k’ofar ta nufi side d’in Arshaad. Direct main bedroom d’in dake side d’in Auwal ya nufa. Yana shiga ya ganshi yashe a k’asa da jikakkun kaya. Da sauri ya k’arasa wajen ya durk’usa ya hau jijjigashi yana kiran sunanshi…. Dai dai nan Aaima ta shigo, duk da fushin da take yi dashi hakan bai hanata fashewa da kuka ba da ganin halin da yayan nata ke ciki. Da sauri Auwal ya juya gareta yace “Yi maza Aaima d’ebo ruwa a toilet yi sauri plss..” Ya fad’a cikin gigita da kid’ima. Da gudu ta nufi toilet d’in ta d’ebo ruwan ta fito ta na zuwa Auwal ya amsa ya hau yayyafa mishi…. Sai da suka fidda ran ma zai farfad’o tukunna yayi wata wawiyar ajiyar zuciya wadda ta taho mishi tare da tari! Auwal ne ya d’an d’ago shi kad’an yahau bubbuga mishi baya yana jera mishi sannu. Da kyar ya samu tarin ya tsaya ya shiga jejjera ajiyar zuciya.... Sai da Auwal ya kamashi ya kaishi kan gadonshi, tukun ya zaro waya ya fara k’ok’arin kiran family doctor d’insu…. Kamar Arshaad d’in ya san me yake shirin yi, yace nasa “Kar ka kira kowa Auwal, i’m fine. Please.” Kallonshi Auwal d’in yayi kafin shima yace “Dan Allah kar ka gwada yin wannan taurin kan! Ka bari a kirashi ya duba ka kawai.” Cikin d’an fushi Arshaad yace “Auwal zamewa nayi na fad’i na buga kaina! Yanzu kuma na farfad’o… Ka gaya min in akwai abinda Doc zai yimin idan ya zo d’in bayan wanda kukai min.” D’an k’uraa mishi ido Auwal d’in yayi kawai ya tsaya yana kallonshi. A hankali Arshaad d’in ya koma ya jinjina a jikin gadon sannan yace “sorry” Ajiyar zuciya Auwal ya sauk’e kafin yace “Are you sure that’s all?” Jinjina kai kawai Arshaad d’in yayi. Auwal bai wani gamsu da maganan shi ba but yaga kamar he wants to be alone shiyasa yace “Shikenan, Allah ya kare gaba, ka kira su Hudan hankalinsu ya tashi sosai. And dan Allah ka sauya kayan jikin nan naka, sai da safe.” “Ok” shine abunda Arshaad yace sannan ya k’ara da cewa “Thanks a lot” Murmushi yayi kawai yace mishi “Good night” Daganan ya nufi hanyar fita. Kallonshi (Arshaad) itama Aaima tayi tace “Ka kira wayana if you need anything” Jinjina mata kai kawai yayi sannan ya fara k’ok’arin mik’ewa dan chanja kayan jikinshi. Ganin haka yasa Aaiman yi mishi sai da safe itama ta juya tabi bayan Auwal wanda har ya kusan ficewa… Sai da ya kusan isa k’ofar fita ta main parlour tukun ta samu ta cin mishi ta wuce ta isa bakin k’ofar ta sa hannu ta bud’e. Ba tare da ya kalletaba dan shi har ga Allah ta fara k’ular dashi Ya sa kai zai fice. Daurewa tayi tace “Mun gode sai da safe” “Allah ya kaimu” yace daga nan ya fice. Ta jima a parlourn bayan ya fita.. Daga k’arshe ta nufi side d’in Arshaad har bedroom ta lek’a ganin yayi bacci yasa ta fito ta nufi sama ta koma d’aki. Da kyar ta samu bacci ya d’auketa. Shi kuwa Arshaad yanda yaga rana haka ya ga dare! Yana jinta lokacin da ta shigo, baya san ganin kowa shiyasa yayi baccin k’arya, ko Hudan text kawai ya iya tura mata cewar ‘he’s okay’. Kafin safiya ya gama deciding yanda zai yi da abunda zai cewa Mammy amman still yana d’an d’arr! Ga fargaba ga tunani barkatai shiyasa zazzab’i yace salama alaikom........... Zazzab’in da ya rufar masa ne yaasa da kyar ya iya mik’ewa yayi sallah a daddafe! Kafin 7 kuwa zazzab’in yayi masa rufdugu…. Ganin yana shirin mutuwa ya sanya shi kiran family Doctor d’in da baya so, dole! Ya kira fad’amshi yana zazzab’i mai k’arfi. Ba a rufe 30 minutes ba Doctor d’in ya iso.. Allurai yayi mishi bayan ya duddubashi dan ya san Arshaad ya tsani magani, daga nan ya jona mishi drip yayi mishi sallama… Sai wajajen 11 drip d’in ya k’are da kansa ya zare ya danne, bayan some minutes ya mik’e ya fad’a wanka. Yaji dad’in jikinshi ba kad’an ba kuwa. Yana fitowa ya d’an shafa mai da turaruka ya zura wata cream jallabiya mai gajeran hannu… A hankali ya k’arasa bakin gadon ya d’au wayarshi ya fara kiran Hudan dan tun da safe yaga message d’inta. Bata wani dad’e tana ringin ba ta d’auka! Bayan sun gaisa ya tabbatar mata da ‘he’s okay daman kawai dan zazzab’i ne’. Tace mishi “Anjima around 1 ana buk’atar shi za suyi traditional event d’insu na yaren Shuwa kuma dole sai yana wajen! Inda hali ya turo driver kafin nan, yazo ya karb’a mishi kayan tradition d’in da aka tanada domin shi (wanda zai saka a event d’in) Kayan ba su iso ba sai d’azu shiyasa bata bashi da wuri ba.” Da “to” ya amsa ta daga nan suka hau hirarsu dan yaga kamar hankalinta still a d’an tashe yake. Sun jima suna hira dan sun fi 30 minutes kafin suyi sallama. A hankali yayi shiruuu, yana y’an tunane tunane.. Chaaan! Ya turawa driver d’in da zai karb’o mishi kayan nashi message daga nan ya mik’e yayi kalmar shahada ya fita ya nufi sama wajen Mammy. A stairs suka had’u da ita tana k’ok’arin sauk’owa! Kamar bata ganshiba haka tazo ta wuceshi. Hannunta yayi saurin rik’ewa ya juyo a hankali yace “Haba Mammy.. Ki saurareni please mana.” Ya fad’i hakan kamar mai shirim fashewa da kuka. Ba tare da ta kalle shi ba tace “Ka bari idan Allah ya kaimu gobe naga kayi abunda nace sai in saurareka” “Meye abunda kike so yayi miki goben??” Suka ji muryar Dad a bayan su!. Da sauri Arshaad ya juya yana kallonshi gabanshi na tsananta fad’uwa! Ba tare data juyo ko ta damu da Dad d’inba tace “Ai gaka ga shi nan! Kana iya tambayarshi.” Tana gama fad’in haka ta nufi k’asa wajen bakinsa da take expecting dan sune ma suka ce mata sun kusan shigowa ba daban su ba da babu abinda zai sauk’o da ita k’asan! Tana buk’atar time ita kad’ai, dan ita kanta bata san daliliba amman komai ya kunce mata.. Kame kame Arshaad ya fara bayan ta sauk’a… Babu yadda Dad bai yi da shi ba amman yace mishi “ba komai! Kawai sun d’an samu issue ne shi da ita lokacin tana cell shine yake so suyi settling”. Sam Dad bai yarda da shi ba dan kwata kwata babu kamanceceniya a cikin maganar shi da tata!. Fahimtar da Dad yayi Arshaad d’in ba zai gaya mishi komai ba ne yasa kawai yace “to, shikenan ka samu ku shirya d’in kafin ka bar gidan nan.” Yana gama fad’in haka ya wuce shi shima yayi k’asan. Sai a sannan Arshaad ya sauk’e ajiyar zuciya He needs to talk to Mammy! Idan tak’i ta lallashi tabbas zai b’ullo mata ta hanyar da bata zata ba! Akwai abubuwa da dama waenda ya sani amma yayi shiru kuma ta san ya sani but it’s like kamar ta manta, so he has to

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});