Chapter 20
Chapter 20
bud’e baki zata yi magana kenan Granpa ya shigo, kallonsu yayi kafin yace “ku biyo ni” sannan ya juya ya fita. A zaune suka sameshi a parlourn da wani da suke da tabbacin Likita ne saboda ga lap coat a jikinshi. A k’asa Hudan ta nemi waje ta zauna kan kafet, gramma kuma ta zauna a kan d’aya daga cikin kujerun parlourn. Nuna mishi ita kawai taga Granpa yayi, daganan taga mutumin ya nufuto…..setin ta ya zauna sannan ya bud’e d’an k’aramin akwatin da ya shigo da shi. Sirinji ya d’auko da wani abu kamar cutting bud sai reza guda d’aya! Sai da aka sha fama sannan aka d’auki jikin, daganan ya bata rezar yace “ta yanko farcenta” cuttonbud d’in kuma a bakinta kawai ta saka ta cire ta bashi, daganan ya d’an sa hannu ya ciri gashinta dake kwance akan goshinta wanda har sai da tasa k’ara dan ba kad’an ba taji zafi! Daga nan ya mik’e ya cewa Granpa “nanda 24 hours in shaa Allah zai dawo” Sannan yasa kai ya fice. Gramma taso tayi mishi magana amman ganin yadda ya had’e rai ne yasa kawai ta kyaleshi suka koma d’aki ita da Hudan bayan ya sallamesu. Iya gata Huda taga gata a wajen Gramma, amman dukda hakka Hudan zancenta d’aya ne “zata je wajen Mama” Da kyar ta samu ta lallab’ata akan zuwa gobe za suje su duba Maman nata, sannan ta yarda tayi bacci mai cike da mafarkin Mama kala kala..... Sai bayan isha tukunna Auwal ya dawo, daman saboda aikin da ya d’orawa kanshi kwana biyun nan sometimes har kusan kwana yake yi a office. Aikin da ba nashi ba da wanda yake nashi duk yi yake…ya kuwa ci sa’a dan Granpa har ya d’an fara sauk’owa da kuma tunanin maidashi kujerarshi. Bai tashi fahimtar babu Mom a gidan ba sai da safe da ya fito zai tafi office!! Cikin nutsuwa yake break fast d’inshi, tun sauk’owarshi Jalila dake kitchen ta had’a uban milo da mdara tana sha ta jiyoshi, tana lek’awa kuwa ta ganshi.. Don haka da sauri ta koma ta hau danna kwab’etar a bakinta har tana kwarewa, cikin minti kad’an ta shanye sannan ta goge bakinta ta nufi k’ofa dan bata so ya fita ba tare data karbi uban kud’ad’en data k’udira a ranta zata amsa ba! Dan bazata iya jira sati biyu ya cika ba kamar yadda Umma ta fad’a ba.. Sannan inta karb’i kud’in ma ba bata zata ke yi ba Dan ita ba sakarya bace ba tana gani sati hudu da suka wuce Kaff kud’in hannunsu sai da suka Kare aka dinga cewa ‘Auwal zai dawo gareta a rikice kuma da maganar auren ganga ganga!’ Ga shi har ita tazo gidan shi bai je ba k’arshentama da tazo d’in da mari yayi mata sannu da zuwa… Sannan bataga alamar rabuwa tsakanin Huda da Arshaad ba dan haka kud’inta kawai zata amsa taje ta yi fafa na kwana biyu ta sayi kayan kwalliya da turarurruka tazo ta yak’i Arshaad tunda gasu a gida d’aya!….. Da wannan tunanin ta fice daga kitchen d’in Ya gama breakfast ya mik’e kenan ita kuma tana fitowa. Sarai ya ganta amman sai ya basar kawai, ya juya ya d’auka jakar shi kafin ya fara k’ok’arin barin wajen, dasauri ta shiga gabanshi ta tsaya sannan tasa hannu ta rik’e jakar, bata damu ta gaisheshi ko ta tambayi ya yake ba tace “Muna biki, inaso zan je, kuma ni wannan mai girkin gaskiya bana iya cin abincin ta tayar min da zuciya yake yi, tun jiya da Adama ta tafi nake fama da yunwa, so anjima ka taho da wata sabuwar mai abincin ta gwada inga ko zan iya ci!” Yayi mamaki da yaji tace ‘Mom bata nan’, a ransa yace “to Ina ta tafi kenan??” Sai kuma ya raya “anyways zai kira ta yana fita yaji mai ya faru! Dan kwata kwata he can’t stand Jalila, shiyasa cikin k’aguwa da son ta rabu da shi yace mata “tou” kawai, sannan ya fara k’ok’arin barin wajen. Da mamaki yake kallon ta ganin tak’i sakin mishi jaka, da d’an fad’a yace “dalla Malama cikani kar In yin latti!” Itama cikin tsantsar rashin kunya tace “sai aikin zuwa office kullum amman kwakwalwa kamar ta kifi, simple abu idan an fad’a maka ba zaka d’auka ba ni ina mamakin ma ta yadda kake yin aikin wallahi!! Da kaji nace maka za muyi biki Ina so zan je kenan! sannan ina nufin yau nake son zuwa maybe kuma kwana zan yi maybe ko kwana biyu dan an riga an fara bikin! Dan haka ka saka driver ya kaini idan na gama kuma yaje ya d’auko ni, in kuma ka bari na dawo da kaina to ka san mai zai faru ba sai na tsaya yi maka bayani ba!. Sannan kuma inaso a cika min jaka ta!” Ta k’arashe maganar tana hard’e hannayenta a kan k’irji, sannan ta fara jijjiga irin ina sauraronka d’innan. Shiru Auwal yayi, ji yake kamar ya shak’eta ta mutu kowa ma ya huta! Cike da gajiya da ita yace “Nawa kike buk’ata??” Ba tare da b’ata lokaci ba tace “Dubu d’ari shidda!!”. kallon tsana ya fara jifanta da shi, chaan! Kuma sai ya d’an yi murmushi kana ya matso kusa da ita ya mik’o mata hannunshi kamar wanda zai karb’i wani abun, cikin yin k’asa da murya ahankali yace “Ban gishiri in baki manda!” Yana murmushi tare da d’age mata girarshi d’aya. Tsaki Jalila taja, Dan sarai ta fahimci me yake nufi hakan yasa ta fara k’ok’arin barin wajen…. Zagayeshi tayi da sauri ganin yana shirin ruk’ota, amman bata tsira ba dan tana wuce shi shima ya juyo kafin ta ankara taji ya ruk’o hannunta sannan cikin sanyin jiki yace “Ko har kin hak’ura da kud’in yanzu kuma bakya so? Na San fa kema kinyi missin….” Maganarshi ce ta mak’ale sakamokon idanuwanshi da suka sauk’a a kan Daddy wanda ya hard’e hannuwanshi kawai ya zuba musu ido, kana ganin fuskarshi ka san yana cikin tsananin b’acin rai!. Da sauri Auwal ya cika hannun Jalila sannan yayi saurin yin k’asa da kanshi.. Daddy yana k’arasowa ya jaa hannunshi kawai ba tare da ya ce mishi k’ala ba suka fice. Mukullin mota ya bashi sannan ya fad’a mishi inda zai kai su. Auwal yana son tambayarshi ‘me zai kai su police station’ amman sai kawai yaja bakinshi yayi shiru sakamokon ganin yadda Daddyn ya had’e fuskarsa tamau!! Suna shiga ciki Auwal ya fara yatsina yana toshe hanci sannan a hankali ya cewa Daddyn “pls, zan jira ka a waje.” Banza Daddy yayi da shi bai ce mishi komai ba.. Suna a haka dpo d’in ya fito, yana ganin Daddy ya ganeshi dan haka ya shiga gaidashi cikin girmamawa.. Amsawa Daddy yayi sannan yace mishi “yana son ganin su Mom” Sai a lokacin Auwal ya d’ago a razane yana kallonshi fuskarsa na nuna buk’atar son jin k’arin bayani. Babu wanda yace mishi komai, dpo d’inne yace “To dan Allah yaje office d’inshi zai kawo mishi su” Daddy bai so hakan ba amman yadda dpo d’in ya nace ne yasa kawai suka nufi office d’in nashi shi da Auwal. Ko minti biyar ba a yi ba aka shigo da su! Dakyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96