Chapter 21
Chapter 21
Auwal da Daddy suka iya gane Ummi, Mom itama ta wujigatu ba k’arya! Duk cikin su Mammy ce mai d’an kyan gani. Mom tanaganinsu ta fashe da kuka, da sauri Daddy yaje ya rumgume yayi ta lallashinta tukunna ta zauna. Ummi ma kukan take yi, Mammy kuwa suna gaisawa ta nemi waje ta zauna, dama tsaftataccen wuri take ta adduar samu don ta samu damar baje hanci ta shak’i tsaftatacciyar iska. Auwal gaba d’aya kanshi ya d’aure, dan haka yaje wajen Mammy ya hau tambayarta ba’asi, dan ya lura ita kad’ai ce ke a cikin hankalinta. Tiryan tiryan haka Mamyn ta zaiyyano mishi komai, tana gamawa ta fashe da kuka kafin tace “Na san mun yi laifi, amman wallahi hukuncin nan yayi mana tsauri! Ka ga inda aka ajjiye mu kuwa! Wallahi ko wajen tumaki ya fishi daraja,tsafta da kyan gani A wajen fa ake kashi ake fitsari, gashi ka san Adama da Zainab suna da allergy..kalli jikinsu kaga gaba d’aya borin jini ne,jiya ba wanda ya runtsa a cikinmu!! Ban san tayaya za muyi wata biyu a irin wajen nan ba, dan wallahi Auwal na tabbatar muna yin sati a nan to sai dai a kwashi gawarwakinmu.......” Tana gama fad’an haka ta sake rushewa da wani irin kuka mai cin rai. A fusace Auwal ya mik’e a wajen yayi hanyar fita, Daddy yana ganin yanayin mik’ewar tashi shima yayi saurin mik’ewa ya sha gabanshi yana cewa “ina zaka je?” Cikin d’acin zuciya yace “ba ruwan ka Daddy, this is between me and Abba!!” Yana gama fad’an haka ya sake yunk’urin fita, da sauri Mom wadda itama ta k’araso wajen tayi hanzarin rik’o hannunshi, yana juyowa yace “Mom dan Allah ki barni kawai, i need to teach him a lesson!! In banda tsabar rainin wayo a kan y’arsa zai yi muku haka? Y’ar gwal ce ita?” Cikin fad’a Daddy yace “Tou sannu sarkin marasa kunya!! Uncle d’in naka zaka koyawa hankali? Haukan naka ya tashi daga tsakaninku yana shirin haurawa kan y’an uwana kenan?? To wallahi a kul d’inka Auwal!! Raina a b’ace yake da kai tun d’azu shiru kawai nayi maka, kar ka yarda ka kaini mak’ura!!” Yana gama fad’an hakan ya koma wajen dpo ranshi a mugun b’ace… Da sauri Mom ta sake rik’o hannunshi duka biyun ta matse gagam sannan ta fara magana “Kayi hak’uri ka sauk’a daga kan wannan dokin zuciyar Auwal, dan babu inda zai kaimu, idan ma za a hukuntasu to bata haka za a yi ba, kaji?? Yanzu na tabbatar kana yin wani abun laifin ka za a gani, kuma nima kaga dai gani da nawa issue d’in, sannan ga matsalar ka da Granpa abun zai yi mana yawa.” Cikin yin k’asa da murya tace “Kana gani ai Arshaad da ya fika wayo tun jiya bai zo ba, kuma na tabbatar yana cikin gidan, shi kuma Aslam dayake babu uwar shi a ciki ta sama ya mak’ale yanata kallonmu bai ce ko yayi komaiba, bai san ba ganshiba. Don haka inaso kayi hak’uri ka danne zuciyar ka, tukunna sai mu san abun yi, kaji ko?”. Da k’arfi ya sauk’e ajiyar zuciya yana bin hannun Mahaifiyar tashi da yayi jajur ya kumbura ga borin jini kala kala, da ido. A haka har gara ita nata da d’an sauk’i akan Ummi, dan ita nata har fuska… “Kaji ko?” d’in da tace mishi ne ya sanya yayi mata nodding kai kawai sannan ya koma ya zauna, itama ta dawo ta zauna. A Chan teburin dpo kuwa Babu yadda Daddy bai yi da shi ba akan “zai biya ko nawa ne a ware musu office d’in wani d’an sandan a gyara musu toilet su dinga amfani da shi su uku kawai zuwa nan da 2 months d’in”! Amman furr!! Dpo d’in yak’i, yace “Jiya bayan na dawo sojoji Mahaifinta ya aiko suka kaini har gabanshi da daddare ya ja mini warning akan in tabbatar na basu horo mai tsanani, kuma ya shaidamin yana da cid’s da yawa, muddin na k’etare umarnin shi to a bakin aikina. Tsabar yanaso ya tabbatar min idanunsa suna kaina, yau da safe ya kirani, duk wani abinda ya faru a nan daga dawowata zuwa tafiya ta gida da zuwana nan yau da safen kaff! Babu abinda bai gayamin ba, har na cikin dare wanda bananan a bakin shi na ji. Hatta abinci yace sau biyu kawai za a dinga basu… So, dan haka dan Allah ka rufamin asiri ina son taimakonku tabbas amman ina jin tsoron rasa aiki na. Da kuma hukunci da yayi alk’awarin yanke min, wanda ban san meneneba.” Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e, sannan ya juyo ga su Ummi…. Idanuwa yaga sun zuba mishi alamun suna sauraron komaai. Tausayin su ne ya kamashi, hakan yaasa yayi saurin d’auke kanshi yana shirin yiwa dpo d’in magana Mom ta matso ta katsesu ta hanyar cewa “Tou dan Allah idan ba zaka iya komaiba, ka raba mana d’aki da matan nan, basu da mutunci kwata kwata, gara a kwashesu a zuba mana wasu” Jijjiga kai dpo d’in yayi sannan yace “zan gwada in gani.” Abinci Daddy ya bayar aka je aka siyo musu da alk’awarin zai dinga zuwa dubasu kullum sannan ya yiwa Mammy da Ummi sallama yace “Mom ta tsaya yana da magana da ita.” Suna fita ya cewa Auwal “ya matso”, ba tare da b’ata lokaci ba ya zayyano mata abinda ido da kunnuwanshi suka jiwo mishi daga Auwal d’in da Jalila yau da safen nan, kafin ya k’ara da cewa “Kina tausayin Yarinya kin d’auko ta zaki bata kud’in kayan d’aki! To ga d’anki nan zai lalata mata rayuwa gaba d’aya tun kafin ta samu kud’in da zata yi auren da shi. Ko kuma ma ince ya gama lalata mata rayuwar dan na kasa fahimtar inda zancen nasu ya dosa! Saboda haka it’s either kice mata ta koma wajen Inna ko kuma shi Auwal ya bar gidan, tunda na lura kamar ba kya son sallamar Jalilan. Duk lokacin data tafi shi sai ya dawo.” Hak’uri Mom tayi ta bashi da alk’awarin zata kira Innar taji, idan komawarta ba zai yiu ba, zata rok’i Gwaggo Asabe ta rik’eta a wajenta kafin ta dawo. Da kyar ta lallab’ashi ya hak’ura, akan sai zuwa wani d’an lokaci In ta tuntub‘I Innaa da Gwaggo Asabe amman da cewa yayi a yau zata bar gidan dan shima jibi tafiya zai yi, so ba za’a bar daga ita sai Auwal ba. Taso su d’an keb’e da Auwal d’in amman hakan bata faru ba, dan Daddy bai basu dama ba. A haka suka yi mata sallama suka tafi, zuciyarta a cunshewa gashi babu daman yin waya don an karb’e tun jiya, gaba d’aya hnkalinta kuma sai ya koma kan yadda zata ci uban Jalila! Dan ta kaita mak’ura, so itace target d’inta in the next two months tana fita a cell zata yi maganin shegiya, tukunna Abba sai Aslam sai Maryam sannan Huda da Ummi…. Kmr yadda wannan Likita ya fad’a, da yamma sai gashi e da results ya bawa Granpa da duk wasu bayanai tukunna ya tafi. Sai bayan sallar isha, tukunna Granpa ya nemi ganin Huda Abba Gramma Daddy da Dad wanda dawowarshi kenan ya tarar ana sallah dan haka ya kira Gwaggwo Asabe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96