Chapter 14
Chapter 14
Hudan take yi mishi da kuma yanayin fuskantar, ne ya sanya gabanshi yayi mugun fad’uwa sannan wata zazzafar zufa ta hau keto mishi, tabbas ya san taji shirmen da Auwal ya gama fad’a yanzu. Auwal kam tsayawa yayi yana kallonta yana mamakin tsananin kamanninta da Abba da Aslam! “Who’s she!?” Ya fad’a a hankali ba tare da kowa ya jishi ba. Chan kuma sai ya tuno da case din y’ar gidan Abba da har ta kaiga kulle su Mom d’inshi a cell! Antake kwakwalwarshi ta d’au chaji, don haka a zafafe ya nufeta, daman neman ta yake yi ya kora mata warning!! Jalila kuwa tsorone ya rufeta ganin Huda, a tunanin ta Umma ce ta fad’i inda take, su kuma suka zo har da su Kaka tafiya da ita, dan haka karkarwar jikinta ya tsananta ba abunda take tunawa irin auren ta da Mati mai wanki ta san yanzu kam babu fashi!. Cikin zafin nama Auwal yana karasawa inda Huda take tsaye yace “Hey! Couz… You must be Huda right? Inaso kije ki samu uban ki kice mishi......” Cikin katseshi Arshaad wanda shima ya k’araso inda take yanzun yace “Huda lets go don’t mind him, he’s crazy!! Muje kawai za mu yi magana a waje.” Ya k’arashe maganar yana durk’usawa don k’ok’arin d’aukar wayarshi data jifar a k’asa. Hudan ita kanta bata san tana da kishi irin haka ba, sai yau. Wato ba zai ma iya fuskantanta a gaban Jalilan ba?! Gashi yadda duk ya rikice jikinshi yana d’an karkarwa yasa ta d’aura ayar tambaya akanshi… Ita Arshaad zai yiwa haka? Why? Of all people kuma yayarta!!! Bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba!. Ai kuwa a rikice, Arshaad yace “Oh nooo, Huda dan Allah kar muyi haka dake mana, na rantse miki da girman Allah ban san wacece waccar ba! Ban tab’a ganinta ba a rayuwata, wallahi! Muje waje we ‘ll talk outside.” Yai maganan yana k’ok’arin kama hannunta.. Da sauri ta fisge cikin kuka tace “Don’t touch me! Ai dole kace baka santa ba mana, Ya Jalilan ce baka sani ba? Daman Mama tace min rannan kaje kana nemanta, kuma nima naji Umma ma rannan suna wani magana da Anty Zainab dana kasa fahimta a kanka kaida Ya Jalila. And if baka santa ba mai take yi a nan ya akayi ta san gidanku da ni kaina ban saniba? Ana tunanin tana gidan Anty d’inta a gida ashe tana wajen ka! I trusted you,I tot.....” Arshaad kam zuwa yanzu ranshi yayi mugun b’aci dan a tunaninshi ko Sakina ce zata fad’awa Hudan wannan maganar a kanshi bai ci ache ta yarda ba, balle a bakin mutumin da bata tab’a gani ba sai yau! Dan haka cikin katseta yace “Ba kiyi trusting d’ina ba Huda! Tunda gashi har kin d’auki maganan da aka fad’a miki a kaina… Rantsuwa ta k’arshe da zan yi miki shine ‘wallahi ban san Yarinyar nan ba!’ Mutum d’aya na sani a gidanku age mate d’inki itace Sakina. Kuma ban san wanne Arshaad d’inne yaje nemanta gida ba rannan d’in da kikace, amman bani bane ba!. Maganar su Umman shima i don’t know anything about it, wallahi!. Anyways Na gode da irin shaidar da kika yi mini.. Hudan aure za muyi ya kamata ace kinyi trusting d’ina tunda as far as i know inda ace ni d’an iskane da tuni ke zaki fara fad’a ba wai ita ko shi ba.” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita dan in ya ci gaba da tsayawa a wajen zai iya yin abunda zai yi ending up yana regretting… A hankali Hudan ta k’arasa ciki wajen Jalila ta kama hannun ta kafin tace “Ya Jalila” Cikin kukan makirci Jalila ta fashe da kuka ta rungune Hudan kafin tace “Hudan Allah da gaske ne abunda Auwal ya fad’a yanzu, gashi na kasa fad’awa kowa, ban san ya zanyi ba! Arshaad ya cuceni.” Ta k’arashe maganar da wani mugun kuka, don ta lura Hudan ta yarda da ita,,dukda kuwa har yanzu tana cikin rud’u akan ‘’me Hudan take yi a gidan’ Dan kalaman Auwal da yadda yace mata cousin ya sake dilmiyar da tunanin ta… Amman yanzu ba wannan ne a gabantaba, raba Hudan da Arshaad shine first! Ga kuma zancen miliyan biyar! Don haka dole ta ajjiye komai a gefe ta duk’ufa ta cimma burinta. Da kyar Hudan ta lallasheta, ta samu tayi shiru.. Rasa abunyi yasa Huda tace mata “bara taje ta dawo” da taso ta tafi da ita, amman tak’i, dan haka ta mik’e tace “tana zuwa, tukunna sai su san me za suyi” Cikin share ragowan hawayenta ta d’agawa Hudan kai, Hudan kuma ta fita a zuciyarta tana rayawa yanzu zata kira su Ummu dan ba zata iya wannan abun ita kad’ai ba! dole a kwatarma Jalila hakk’inta, tana tafe zuciyarta na tafarfasa, ita kawai idonta ya rufe da kishi har ya kaita ga kasa yin lisaafi mai kyau a kwakwalwarta. Jalila na ganin fitar Huda ta share hawayenta ranta fess! Sannan ta mik’e ta k’arasa inda Auwal ya daskare yake k’ok’arin hada 1+1 akan alamarin da ya gudana yanzun nan dan in dai shi ba dak’ik’i bane ba tou abu na farko daya fara fahimta shine ‘Arshaad Huda yake dating!’ And tabbas bai san Jalila ba, to who….. Muryar Jalila wadda ta k’araso yanzu ne ta katseshi jin tana cewa “Nayi duk abunda kace, yanzu abunda nakeso da kai shine ka kawo miliyan d’aya, ragowar kuma in aiki ya kusan kammaluwa, dan..” Shak’ar!! Da yayi mata ce ta katse mata maganar tata, cikin d’acin zuciya da k’arfi yace “Who are you?”. BULAMA ✍️ Cikin fushi tace “kafi kowa sanin me kayi! Kuma ina so ka sani Allah sai ya bi ma Hudan hakkinta dan wallahi kaji na rantse ita d’in son gaskiya da tsakani da Allah take yi maka! Amman duk da hakan zan yi k’ok’ari inga na cire mata kai a ranta!. Sannan ga sak’o ka gayawa Abba! ‘ in duk duniya ce zata taru a kaina to ba zan yarda ba!! Nima ina nan zuwa karb’arta, daganan in Mahaifinsa yaga dama ya kulle kaf jinsina ba wai iya danginaba!!”. Tana gama fad’in haka ta wuce ta barshi nan, a daskare!! Da kyar ya iya tattaro ragowar kuzarinsa ya fice shima a d’akin, saboda iya yadda yaga ta fita tana layi ya tabbatar mishi ba zata iya kai kanta ko da nan da gate ba! Sai dai kuma, ko da ya fita d’in sai bai ganta ba bai ga alamartaba kamar wadda tayi layar zana ta b’ace! Duddubawa ya hau yi har buildings d’in gefen emergency amman babu ita babu alamar ta! Abun ba k’aramin sake d’aga mishi hankali yayi ba dan babu inda bai duba Mama ba amman bai ganta ba har unguwar su yaje a tunanin shi ko ta koma amma tun kafin ya k’arasa gidan ya hango ana (Baba) datsa datsa kwad’o a gidan, ya fitar da machine da alamun fita zai yi. Sanin da yayi in dai napep ta hau to ba lalle ta rigashi isowa gidan ba ne, ya sanyashi zaman jiranta, anan cikin mota! Sai dai almost 2 hours amman bata dawoba. Zuwa yanzu kam hankalinshi ya kai k’ololuwar tashi!….. …….Tun farkon had’uwar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96