Chapter 53
Chapter 53
can cause problems for you daga Granpa dan na lura maganar kad’ai idan akayi ran kowa sai ya b’aci a estate d’in. Shiyasa na rok’i Baban Sakina akan ya b’oye identity d’ina har iya lokacin da za a d’aura mana aure, daga nan zan san yanda zan yi In shirya ku kaida su Madu, tunda kuma ga auratayya a tsakani, dole a na san za a hak’ura a sauk’o a yafewa juna… Na san nan ne side d’in Mahaifinta mun fisu k’arfin da iko da ita amma da nayi lissafi tabbas naga akwai possibility d’in suci galaba a kanmu, ni kuma issue ko case ne kwata kwata bana so har in samu cikar buri na shiyasa nayi k’ok’ari wajen ganin na danne duk wani abu da ka iya zama mini matsala wajen ganin na mallaki Huda a matsayin matata. I know I was wrong! Ban san taya zan fara baka hak’uri ba, but I did everything out of love! Dan to be honest a yanda nake jin k’aunar Huda a raina Abba wallahi I don’t think I can go on living idan aka yi tunanin raba ni da ita! Please try to understand and forgive me.” Ya k’arashe maganar cikin tsananin kalar tausayi kamar wanda zai fashe da kuka. Shiruuu, Abba yayi yana nazari kafin yace “Arshaad na san menene so, tbh a lokacin da nake tare da Maryam, ake k’ok’arin rabamu! Hakan nima nayi na zama selfish har naga mun mallaki juna… Amman abunda kai kayi is morethan selfish, Arshaad banji dad’i ba, ka k’i ka baiyanar mini da y’a ta.” Shiruu, Abba ya d’anyi kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yaci gaba da magana “But, zan iya yafemaka! Zan yi k’ok’ari In manta da abunda kayi after all everyone deserves a second chance sannan naji reason d’inka and its not all bad. But Arshaad don’t ever try something like this again saboda i as selfish back then just like you and abun bai yi ending well ba! Although I was happy for good 10 years, but har yau Maryam is not in good shape with her parents because of my decision.” A hankali Abba ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “And another thing thankyou so much! Hudan ta fad’amin yadda ka dinga d’awainiya da su har makaranta, Allah ya saka maka da alkhairi.” A hankali Arshaad yayi murmushi kafin yace “Ba komai Abba, thankyou” Murmushi Abban yayi kafin yace “A matsayina na Mahaifin Hudan! Na baka ita Halak Malak! Allah ya nunamin ranar da zan aura maka ita. Dan Allah Arshaad ka kula min da ita.” Ya k’arashe maganar, cikin nauyi da karyewar zuciya. Zamowa Arshaad yayi daga kan kujerar da yake kai kawai ya hau godiya, yana yi masa alk’awarin in shaa Allah zai bata dukkanin kulawar data kamata….. Sai godiya yake yi, har sai da Abban ya sallameshi tukun ya mik’e ya fita still yana godiya. Murmushi Abba yayi bayan fitar Arshaad d’in, ba abunda ya zo kanshi sai lokacin dasu Kaka suka bashi Maryam! Yanda Arshaad yayi exactly shima hakan yayi….. A hankali yayi murmushin da har sai da y’ar kwalla ta zubo daga idanunshi! Yana tuno ta (Maryam) da moments d’insu…. Chaan, ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, a hankali yasa hannu ya sharce kwallar shi, sannan yace “Astaghfirullah”. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 45 Kiran sallah aka fara, dan haka ya mik’e ya wuce toilet ya d’auro alwalla ya sauk’a don zuwa masallaci. Arshaad yana zuwa k’asan, ya tarar da Aslam a tsaye jikin dispenser yana shan ruwa.. wanda jin sauk’k’owar tasa ne yasanya shi ya juyo. Fara’ar da ya ga yana yi ne ya sanya Aslam d’in fahimtar wani abu dan haka yad’an matsoshi yana shirin yin magana yaga yayi hugging d’inshi yana wani murmushin da yake baiyyana tsantsar farin cikin da yake a ciki! Cikin farinciki ya cika shi still yana murmushi ya d’ago ya kalleshi sannan yace “Call me Ango! An bani mata”. Ya fad’i hakan yana dariya. Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e, sannan yace “Congrats bro, i’m very happy for you.” Cikin zolaya Arshaad yace “na yi maka wayo! Kai ma kayi sauri ka nemo..” Murmushi Aslam d’in yayi kafin yace “ka yi mini wayo kam!” Shigowar da Auwal yayi cikin parlourn ne ya katse su. Bai kalli kowa ba ya wuce yaje ya zauna akan d’aya daga cikin kujeraun parlourn… Aslam ne yace masa “Auwal ya gida” D’an d’agowa Auwal d’in yayi ya kalleshi, har zai ce wani abu kuma sai ya d’auke kai kawai yace “Fine” yana mai kallon hanyar staircase…. Bayan kamar 2 minutes Abba ya sauk’o. Cikin girmamawa ya gaida Abban har da d’an rissinawa! Da d’an mamaki Abba ya kalleshi ya amsa sannan ya wuce, su Aslam suma suka nufi hanyar wajen ganin zasu fita yasa shima ya mik’e suka nufi mosque gaba d’ayansu....... A dining d’in suka tarar da Hudan, Sakina Sudais da Shuraim don haka suka yi joinin d’insu su uku, banda Aslam wanda ya wuce gida daga mosque d’in don kanshi yana d’an ciwo! Shiyasa kawai ya wuce bayan ya cewa Arshaad “ya karb’a tofin ya taho dashi in sun gama”. Babu kunya haka nan Auwal ya samu guri ya zauna dai dai gefen Sakina! Da mugun sauri tayi zumbur! Zata mik’e Hudan tayi saurin rik’ota tana nuna mata Abba da ido. Suna shirin farawa Daddy ya shigo, yana ganinsu gaba d’aya ya cewa Abba “Wato ka had’a kan y’ay’anka ni kuma ka manta da ni, ko?” Dukkansu dariya suka yi kafin su shiga gaidashi one by one.. Cikin kulawa ya amsa musu yana mai cewa “Na gaji da cin abinci ni kad’ai daga yanzu kawai a dunga yin dinner a chan side d’ina, breakfast da lunch ku dinga yin abunku a nan, in ba haka ba shirun ai sai yayi min yawa, daga ni fa sai Auwal shima kuma in yaga dama ma sai ya kwana biyu bai yi dinner d’inba, yau kuma kalleshi ja’iri ya gudo ya barni!”. Duk dariya aka sa sannan suka fara cin abincin cikin nishad’i….. A zaman su Auwal ya cewa Sakina ‘Hi’ Yafi sau ashirin amman har aka tashi bata amsashi ko d’aya ba! Ko arzik’in kallo ma bai samu daga gareta ba k’arshema juyar da kujerar tata ta yi kad’an ta karkatar da hankalinta a Huda gaba d’aya! Wanda hakan ya sanya duk jikinshi yin sanyi dan tunda yake a rayuwarshi tun yana secondary school mace bata tab’a yi mishi haka ba, wasu ma sune suke cewa suna sanshi, dan ko a yanzu haka kafin yace yana so sau d’aya sai ance ana sonshi sau goma!!. Daddy ne ya fara mik’ewa sai Abba…. Auwal yana shirin yi mata (Sakina) magana tayi sauri ta mik’e ta haye sama Hudan kuma ita da Arshaad suka koma cikin parlourn suka zauna, su Sudais ma suka yi mishi sai da safe suka tafi. Kasa mik’ewa Auwal yayi a wajen, dan haka har Abba ya dawo ya taddashi yana nan bai tafi ba!. Hudan daman a shirye take dan haka ta kira Sakina a waya tace “tazo su je” Arshaad yaso yace zai je amman kunyar Abba sai ta hanashi yin maganar, dan haka ya yi musu sai da safe ya tafi bayan ya karb’i ruwan Addu’an
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96