Chapter 97
Chapter 97
da ta ingizo Bukatarsa tace. "Ohhh sorry Ya Haroon meya faru gaya min me yasameka". Cikin sakaliyar murya yace. "Haroon yunwa yakeji". Sam bata fahimci inda batunshi ya dosaba haka yasa cikin haɗa fuska tace, "Ya Haroon ka dawo gida, shi Hamma Jabeer ba matace dashi ba, bare ya kula da cikinku, na kuma san in kuna Side ɗinsa ba wani zuwa wurin Aunty Juwairiyya zakuyiba, kuma itama fama takeyi da mijinta. Ni gsky ka dawo Tsinako nasan Umaymah zata kular min da kai da kyau, ko kuma kazo Masarautarmu Leddi julɓe, nida Sitti mu kula da kai". Murmushi yayi tare da cewa. "Masarauta Joɗo fa masarautace mai daraja, da karrama baƙo baki san asalin tarihin inda masarautar tasamu suna Joɗa bako. Baby kada ki damu kular da muke samu ko sarki mai mata huɗu da kwarkawara biyar baya samu. Tako wani sashi na gidan abinci hadimai ke kawowa Side ɗin Sheykh a ƙalla wani lokacin kusan abinci kala goma muke riska, kinsan fulani ba marowata bane. Kawai matsalar wannan yunwar rashinki ne, a kusa yasa nake jina ina tashi sama kamar doki". Cikin kunya da kauda zancen tace. "Ya jikin Hamma Jabeer shugaban tuzuran ƙasar mu?". A hankali ya juyo kanshi ya kalli bisa makeken gadon da Jabeer ke kai. Da sauri ya katse kiran bayan yace mata. "Ina zuwa". Kan gadon ya nufa, jabeer ɗin yana ƙoƙarin tashi zaune. Hannunshi daya miƙa zai taimaka mishi, ya buge cikin haɗe fuska yace. "Yanzu ƙarfe nawa?". Wayarshi dake hannunshi ya duba cikin zuba mishi ido yace. "Ƙarfe ɗaya dai-dai". Cikin tsuke fuskarsa tamkar zaiyi kuka yace. "Shine ka barni ina bacci kamar kafurin da bashi da addini. Anyi sallan bamgrib baka tasheniba, anyi Isha'i baka tasheniba, daga wannan masifeffen bacci mara daɗi mai cike da mafarkai marasa daɗin da nasan rashin yin salla a lokacin sane ya jazamin su. Iya wunin yau duk so kuke kuyi min asarar lokuta masu muhimmanci da daraja, kun sani na makara la'asar da magriba hakama isha." Ya ƙarishe mgnar yana miƙewa tsaye, Tare daci gaba da cewa. "Da fari ansa ni na tsaya gaban jama'a da baiyana surata, Aka ɗora min da duka kana, akasa na makara sallan la'asar, Yanzu kuma mangriba da isha'inma kun barni ina baccin asara na makara, sabida baka san darajar yin salla a cikin jam'i da kuma yin ta cikin lokacin ta ba ko?". Cikin taɓe baki Haroon yace. "Kasan ai ni ba musulmi bane, ban san komaiba". Harara ya dannawa Haroon tare da cewa. "Kai ka gayawa kanka, Ni bana kafurta mutum, abinda na sani dai kai tsarin yahudu da nasarane, To bari kaji, Ni bani da laifin komai sabida bacci nakeyi, mai bacci kuma al'ƙalami ya sauƙa kansa har sai ya farka. Kai dake ganina ina bacci lokacin salla yayi idonka biyu baka tasheniba haƙƙin a kanka ya rataya." Ya ƙarishe mgnar yana shiga bathroom tare da cewa. "Ka cire idonka a kaina banza mai kallo kamar mayun wancan garin mugayen". Murmushi Haroon yayi tare da komawa ya zauna bisa kujerar. Shi kuwa Sheykh Jabeer wonka ya kumayi da ruwan ɗumi, kana ya kimtsa cikin irin suturun da yake ta'ammali dasu, in yana gida. kana ya ɗaura wata farar jallabiya kai. Sannan ya fito bayan ya shafa mai ya fesa turare. Yana fita ya fara ramuwar sallan daya wuceshi yana bacci. Haroon kuwa falo ya fita abincin da yasan zai iya ci ya kawo mishin A ƙalla awa ɗaya yayi kafin ya tashi kan sallayan Gaban gadonshin ya dawo ya zauna bisa tattausan carpet ɗin da ke shimfiɗe a wurin mai kalar Sky blue and white. Sosai yaji daɗin jikinshi, sai dai har yanzu yana jin raɗaɗin bulalin. Tea kawai ya iya sha. Kana a hankali yace wa Haroon. "Canza min beshit ɗin nan da blanket ɗin." Hararanshi Haroon yayi tare da cewa. "Zan koma, yaseen na gaji da mulkinka da sarautar da kake ji dashi. Ji yadda ka medani tamkar wani bawanka ko hadimin gidanku, kuma duk abinda zanyi maka sai ka cini gyara, mutum ba'a iya mishi sai masifa kake min kamar dai nine nace a zaneka". Ya ƙarishe mgnar yana miƙewa tsaye tare da gimtse dariyarshi, sabida ganin kallon da Jabeer ke mishi. A haka dai ya sauya komai na gadon kafin suka, hau suka konta. Tsaki Jabeer yaja tare da cewa. "Ni dama ka tafi wancan ɗakin sabida zancen gsky kasan ni bana son takura. Sabida zaka hanani sakewa yadda nakeso". Cikin gajiya Haroon yace. "Allah babu inda zan fita inje". Da haka dai Haroon yayi bacci. Shi kuwa Sheykh Jabeer karatu yayi tayi har biyu da rabi tayi kana, ya buɗe tafin hannunshi yayi addu'o'in bacci. Falaƙi 3 Nasi 3 ƙulhuwa 3 Ayatulkursi'u 1 kana amarrasulu 1 tofa a tafin hannunshi ya shafa a jikinshi. Kana ya kuma yi. Haka ya tofa a tafin hannunshi ya shafa a jikin Haroon Wanda tuni ya ɓingire, Shi kuwa Jabeer wannan al'adar rayuwarsa ce daya saba, kan Jalal da Jamil sabida suma haka suke bingirewa, shikeyi tofi ya shafa musu. Washe gari Lamiɗo baiyi zaton Jabeer zai samu fitowa masallaci ba, Shiyasa limamin dake jansu salla in baya nan ya fito ya jasu salla, yayinda Jabeer ke cikin sahun forko. Wannan yasa mutane sukayi zaton ciwon ne yayi tsamari bai samu ya fitoba. Ana idar da salla kuma ya fito yayi cikin gida sabida. Fushi yakeyi da wannan tsohon ya sani in ya tsaya kuma zai dameshi da wata falsafarshi da zaici karo da addini. Ƙarfe takwas dai-dai. Barrister Kamal da Ya Jafar, da kuma Baba Basiru ne zaune dashi a falon shi. Suna zaune anan Jalal ya shigo cikin yanayin damuwa yace. "Hamma Jabeer, Umma na falo tazo dubaka da jiki." Cikin yamutsa fuska yace. "Wacece hakan?". Cikin fusata Baba Basiru yace. "Ashe uwarka ma bazaka santa ba, ina dai baka san wacece Umma ba". Wani irin kallon ido cikin ido Sheykh yayiwa Baba Basiru, sai kuma ya ɗora ƙafarshi ɗaya kan ɗaya, cikin ƙasaita ya kalli Jalal tare da cewa. "Mene Umman!?". Ya sani sarari Gimbiya Saudatu ake cewa Ummu . Gyara tsayuwa Jalal yayi tare da gyara zaman belt ɗin ƙugunshi yace. "Matar tsohon Galadima marigayi, Baba Muhammad ce Ummar Gimbiya Saudatu." Da sauri Baba Basiru yayiwa Jalal daƙuwa tare da cewa. "Kan uwarka hegen yaro ɗan shila". Shi kuwa Jabeer ƙafarshi ya fara kaɗawa. Barrister Kamal kuwa ido ya zubawa Fuskarta Jabeer da Jalal. Cikin sanyi da tausasan laffuza yace. "Jabeer tashi muje ka gaisa da ita tunda ta taso tazo har nan dubaka da jiki". Kanshi ya gyaɗawa Barrister Kamal ɗin wanda suke cewa Baba Kamal wanda yake mahaifin Sulaiman, sa'an Jabeer. Da hannu yayiwa Jalal alamun yaje yace, yana zuwa. Shi kam Baba Basiru bayan Jalal yabi. A babban falon suka zauna shida Gimbiya Saudatu da Laminu da kuma Baba Nasiru. Jalal, Jamil, Haroon, Jafar, kuwa duk suna can Dinning area kan dinning table sunayin breakfast. A jere suka fito falon shida Barrister Kamal. Suna isowa tsakiyar falon. Cikin wani irin taku mai cike da ƙasaita da rashin tsoro. Ya kalli Gimbiya Saudatu dake zaune bisa kujerar zamanshi. Yatsunshi biyu ya haɗa ya kaɗa mata tare da mata alamun tashi min kan kujera. Cikin wani irin kallo mai nuna
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185