Chapter 34
Chapter 34
wuƙan a cikinsa wani irin ƙara isa ya sake, sai dai babu mai jinsa bare ya kawo masa agaji domin. Dai-dai wannan lokacin duk wani musulmin wannan yankin yana masallacin jumma'a, Da wannan damar suka samu suka kashe isa, wanda suka daddatseshi da wuƙa. Daga nan suka kira Ba'ana a waya, nan take ya kaɗa shanayen yace. "Yauwa aikinku yayi kyau, yanzu kuyi maza kuyi gaba da shanayen kasar Cameroon, zaku nufa birnin Yahunde kuna isa bakin boda yarana na kasar zasu amshi shanayen ku kuma sai ku dawo, kafin nan ma komai ya lafa baza'a zargekuba". Haka kuwa sukayi, suka kaɗa kan shanu suka fasa daji, suka nufi hanya, shi kuma ya dawo cikin gari ya wuce ɗakinsa bayan ya bawa uwarsa lbri. Koda aka taso sallan jumma'a, anyi mmkin ganin isa bai dawoba, shiru-shiru dai har akayi sallan la'asar babushi, tofa daga nanne hankali ya ƙara tashi. Cikin kiɗima suka fara shiga daji a duba ko lfy bai dawoba. Ai kuwa nan maza matasan Fulani suka watse cikin daji, Bayan sun gama bulayin nemane babushi babu shanunshi, suna cikin zagayawan ne Sale yayi arba da gawar Isa dake malale cikin jini. Nan suka ɗauki gawa suka koma cikin gari dashin. Wannan rana hankali Fulanin Rugar Bani yayi masifar tashi, gaba ɗaya ma sai ba'amaida hankali kam ɓatan shanunba, Hankali ya tashi, ɗauki ɗai-ɗai da akeyi musu ya fara hautsuna musu tunanin, Gashi kisane da babu wanda za'a iya kamawa, koda aka sanarwa hukar cikin Numan sai suka korasu da case ɗin, sabida a lokacin da suka zo shigar da report babu musulmi a police cikin officers ɗin shiyasa suka korasu da batun. Salmanu wanda shine ɗan bokon da kan iya jagorantan lamarinsu, yana gadon asibiti, bisa ƙarƙashin kulawar abokinshi badon hakaba da tuni Ba'ana ya kasheshi. Koda fulani suka hatsala kamar kullum haka Arɗo Yabani ya tarasu ya taushi zuciyarsu, da kuma shawarar, su kai kukanmu ga sarkin Numan ɗin, tunda ya hanasu samun damar ganin sarkin Nuruddeen Bubayero. Koda sukaje masarautar Numan ɗinma abin da akayi musu a police station, fiye dashi akayi musu. Dole suka dawo suka nade hannun suka kai kukansu ga, Allah, sai dai sun ɗauki mataken kare kai da kai, bisa shawarar daddatawa cewa kada makiyayan ko manoma su yarda su rinƙa rabuwa a daji ya zama suje tare su dawo tare da hakane zasu gane mai ke musu ɗauki ɗai-ɗai ɗin. Yau la'hadi tunda safe, Aysha keta shirin komawa makaranta. Sabida hutunsu ya ƙare. Tafiyan safe takeso tayi shiyasa ta gama shirinta da wuri. gaba ɗaya suna tsakiyar gida Yayunta maza sune zasu rakata bakin hanya. Haka nan taji bata son tafiya ta barsu, tsoro mai yawa ya rufeta Especially in tayi tunani da yadda ake kashe makiyayan. Durƙushe take gaban Bappa yana yi mata masiha mai ratsa jiki da zuciya ya kare nasihar tashi da cewa. "Allah ya miki al'barka Shatu, Allah ya kaiki lfy." cikin sanyin murya tace. "Amin Amin Bappa ngd matuƙa". Sai kuma ta kalli Ya Giɗinta da ya zuba mata ido tamkar bai taɓa ganintaba, cikin sanyin murya yace. "Yanzu shike nan zaki tafi ki barmu, ki tafi can ke ɗaya ki zama baki da kowa naki a kusa". Haka nan kalamanshi ya karyar mata zuciya, sai kuma taji hawaye nason zubo mata. A hankali tace. "Ya Giɗi bazan daɗe ba zanzo". Cikin sanyi Seyo yace. "Allah yasa ki samemu in kinzo ɗin". Da karfi ƙrjinta ya bada wani sauti mai karfi, ta buɗi baki zatayi mgna kenan Ya Lado ya ɗanyi murmushi cikin sanyi yace. "To Shatu Ni zan tafi inje in kunce dabobbin, bazan samu daman rakakiba, Allah ya kaiki lfy, ya ƙaddara saduwarmu kan al'khairi, ki yafe". Kawai sai taji hawaye na zubo mata, cikin dariya ya Gaini yace. "To kunga kun sata kuka, Shatu ko dai bakya son komawane?". Cikin rawan murya tace. "Inaji bana son rabuwa daku". Murmushi inna tayi tare da cewa. "Ai kuwa dole ki rabu damu, domin lokaci yazo". Ummey dai ido ta zuba musu. Shi kuwa Ya Lado da murmushi a fuskarshi ya fita yana ɗaga mata hannu. Bappa ne ya ɗanyi murmushi cikin sanyi jiki yace. "Maza tashi ki tafi, ki gaida Aminiyarki Rafi'a, Seyo Giɗi Gaini ku rakata har bakin titi". Da sauri suka miƙa. Ita kuwa Aysha kamo hannun Junainah tayi wacce tayi kasake tana kallonta cikin sanyi tace. "Ƙanwaliya, sai na dawo". Kai ta gyaɗa mata cikin sanyin da sam ba ɗabi'arta bane a hankali tace. "Addana, bana son ki tafi". Shafa kan Junainah tayi, kana ta faɗa jikin Inna, tana zubda hawaye, sake Inna tayi sannan ta faɗa jikin Ummey, murya can ƙasa Ummey tace. "Tashi ku tafi, Allah ya sadamu da al'khairi, Shatu". Da kuka ta fita, ta barsu jiki a mace. A hankali suke tafiya tafiya, suna hira, kayan lambu da suka cika mata bakko dashi na hannun Giɗi, jarkan nonon kuma na hannun Seyo, ya Gaini kuma, jakar kayantane a hannunshi, da kwaryan kwan zabbi, kamar dai yadda suka saba, suna tafe suna, hira suna gab da bakin hanya. Ba'ana ya isosu aka ci gaba da tafiyar, suna isa motar da zata wuce cikin Yola (Ɓadamaya) na isa, saida suka samata kayanta, kafin, tazo har zata shiga taji Giɗi na riƙe da hannunta juyowa tayi ta kalleshi cikin murmushi yace. "Kinsan abinda zamu iya aikatawa a duniya da abinda bazamu iya aikatawaba". Kai ta gyaɗa mishi alamar eh, murmushi yayi kana yace. "To ki ƙara yarda zamu zamu zama GARKUWA'nki muddin muna raye." Murmushi tayi cikin ɗan jin daɗi tasan akan mgmar auren Ba'ana yake nufi. Ido ta zubawa Ya Seyo shi kuma sai murmushin shi nan yake mata, Ya Gaini kuwa hawayene ya cika masa ido shiyasa ya juya ya bata baya. Cikin sanyi Seyo ya matsota kana a hankali yace. "Ki sanarwa duniya halinda muka ciki in kin samu dama Aysha, ki sanarwa duniya Fulani ba ƴan ta'adda bane ba ƴan bindiga daɗi bane ba kuma ƴan Garkuwa da mutane bane, wasu kesa rigar Fulani ke wanzar da ɓarna da wasu ƙalilan na mugayen daji." Cikin rauni ta zuba mishi ido tana kallon kekyawar fuskarsa, da gyaɗa mishi kai. Ba'ana ne ya ɗan kalleta tare da miƙo mata damin kuɗi yace. "Mata zanyi kewarki, amman ba matsala duk ƙarshen mako zan ke zuwa." Drivern ne ya katse su da cewa ta shigo su tafi, haka yasa ta juya da sauri ta shiga, yaja suka tafi tana ɗaga musu hannu, suma basu tafiba saida sukaga motar ta ɓace musu. Juyawa sukayi suka nufi cikin gari. Shi kuwa Ba'ana da ido ya rakasu a a baiyane yace. "Zanga ta yaya zaku zama GARKUWA'nnata, dan na fahimci duk bakwa son aurena da ita, toko zanyi mgninku." Su kuwa basuma juyo sun kalleshi ba. Ita kuwa Aysha tana komawa ta samu, Rafi'a ta dawo ta gyara musu komai na ɗakinsu, to samun Rafi'a da tayine yasa ta ɗan samu nitsuwa, ranar kam wuni sukayi suna hira, darema haka sukayi ta hirar yaushe gamo. A Rugar Bani ( Rugar kikan) kenan nake nufi. kuwa, su Ya Gaini suna komawa suka tafi kiwo, kamar dai yadda suka saba, sukaje kiwo lfy suka dawo lfy. Washe gari ranar Litinin! Saudia. Sheykh ne konce, bisa wani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185