Chapter 94
Chapter 94
mana hankali, tunda dama duk cikinmu yaran Lamiɗo babu wanda ya ba koda sarautar fadanci ce sai Yaya Muhammad, to kuma dan ya rasu sai a maida sarautar kam jikoki a tsallake ƴaƴan duka." Cikin tafasar zuciya Laminu yace. "Yo waya ma sani ko sune suka kashe mana Babanmu dan mulkin ya koma hannunsu, ku kuma kuka barsu". Da sauri Baba Nasiru yace. "Muka barsu kuma, ai Allah ne zai barshi ba mu in bamu ɗauki mataki ba, Allah ya nuna ikonaa yanzu shi Jafar ɗin kallon me akeyi mishi?". Da sauri Gimbiya Saudatu tace. "Mahaukaci tuburan". Dariya sukayi kana cikin rashin gamsuwa Laminu yace. "To kuma duk da haka ai ba'a dawo da sarautar kanmu ba sai, aka bawa ɗan tsohon sarkin wannan bappan naku mai farin gemu. Bayan nan kuwa duk bawa kowa mulkin komai ba, dan sakacinku an ɗauki mulkin Garkuwa an bashi." Cikin sanyi Ya Hashim ya harari ƙanin nashi tare da cewa. "Laminu kafa ji tsoron Allah ka tsarkake zuciyarka, ka raba kanka da wannan zalumci da kafurar zuciya". Cikin zafi Gimbiya Saudatu tace. "Rufe min baki, samodaran banza sako tumaki ɓallo jakai,". Cikin sanyi yace. "Umma badake nakeyi ba da". Cikin mgnar in-ina Baba Nasiru yace. "Tafi daga nan damu kakeyi mana, ka fake da Laminu, maza tashi ka bamu wuri". Miƙewa yayi ya fita ya bar musu wurin ya nufi sashinsa wurin iyalanshi. Su kuwa nan sukaci gaba da sabgogin gabansu. Nan Gimbiya Saudatu ke cewa. "Sai gobe da sassafe zanje in salon hegen balaraben nan". Dariya Laminu yayi tare da cewa. "Yau da yaga haza, yaga zai zanu sai cewa yayi, wai shi ba bafulatani bane, a kirashi dama duk ƙabilar da akaga dama". Playing video yayi ya miƙa wa su Baba Basiru tare da cewa. "Jaridar safi ta gobe da safe da wannan labarin zai fito a shafin forko nako wanne kamfanin jarida, Kana wannan abun shine hirar da BBC Hausa da kanshi zasuyi karin kumallo dashi. Sai wannan lbri da video da hotuna sun bazu tako ina, dan ina jirane sai jaridu sun fidda shi kafin in watsashi kafafen yaɗa labarai na duniyar gizo-gizo". Cikin tsananin jin daɗi suka jinjina wa basirar Laminu. A can sashin Gimbiya Aminatu kuwa, kekyawar tsohuwar bafullatana ƴar kimanin shekaru 61 sosai hankalin ta ya tashi jin labarin abinda ya samu jikanta mafi soyuwa a gareta. Cikin rawan jiki ta miƙe tare da juyawa zata nufi Side ɗin ta. Da sauri Lamiɗo yayi gyaran muryar dake mata nunin ta zauna ta nitsu. Cikin tashin hankali ta koma ta zauna tare da cewa. "Allah Rane zanje in duba halin da yake cikine". Cikin ƙasaita da bada umarni yace. "Koma ki zauna ki nitsu kin ga magriba ta ƙara to. Bawai zan hanaki zuwa bane, ki bari ayi sallan magriba da isha'i sai ki aika Jakadiya ta dubo miki in idonshi biyu sai kije". Ba don ta soba ta amince da hakan. Hajia Mama kuwa, tana jin lbrin abinda ya faru daga bakin Abba, kai tsaye daga sashinsa sashin Jabeer ɗin ta nufa. A falo ta samu Haroon kadai zaune cikin shigar kakanan kaya. Cikin tashin hankali da kiɗima da firgici ta nufi hanyar side ɗin. Jabeer ɗin ido na zubda hawaye. Da sauri Haroon ya miƙa tsaye cikin sanyi yace. "Mama ya samu bacci ne, kuma Dr Aliyu yace kada a tadashi, jikin da sauƙi ma sosai ki kontar da hankalinki". Ina hankalinta bai konta da hakanba, saima ƙara kutsa kai cikin falon side ɗin shi takeyi. Cikin sanyi ta tsaya jin Haroon na ce mata. "Dan Allah Mama kiyi haƙuri, Allah kuwa jikin da sauƙin, Abba da Lamiɗo da kansu suka kula dashi, yanzu haka bacci yakeyi." Cikin tashin hankali murya na rawa tace. "Haroon hankali na ya tashi sosai, ina tsoron kada a cutar min dashi kamar yadda akayiwa Jafar." Hannunta ya kamo kana yaja suka dawo falo, cikin sanyi yace. "In Sha Allah babu wani abinda zai sameshi, in Allah ya yarda an gama samun nasara a kansu, yanzu warakace ke kusantosu, in sha Allah duk sarƙaƙiyan dake sarƙafe cikin masarautarku da mutanen cikinta zai worwore, za kuma ayi walƙiya kowa zai ga kowa!". Wani irin lumshe ido tayi tare da cewa. "Allah yasa haka". Cikin kontar mata da hankali yace. "Amin Amin. Umaymah ma tace tana nan tafe". Cikin tarin mamaki da baiyana tsantsar jin daɗin ta tace. "Alhamdulillah kai naji daɗin wannan mgnar ko ba komai in tazo ai zan samu wacce zan tattauna damuwar raina, sabida hirar waya bata wadatar wa". Murmushi yayi tare da nuna mata hanyar fita cikin tsokana yace. "Wato kun san ɗan naku ragone shiyasa duk kuka tashi hankulanku." Cikin share hawayenta tace. "Haroon yayanka nefa". Tura baki yayi tare da cewa. "To naji Hajia Mama je kiyi salla lokacin salla yayi, kinji an fara kiran salla". Da haka ta fita. Shi kuwa Haroon a hankali ya nufi cikin ɗakin, kamar yadda yabar Ya Jafar zaune a tsakiyar gado yasa Jabeer a gaba, yana karatu tare da gyara mishi rufuwar shi. Haka ya sameshi yanzuma, Kuma har zuwa yanzu idonshi bai daina zubda hawaye ba. Kana ganin fuskarshi zaka hango zazzafan so da ƙanan da tausayin ƙanin nashi cikin ƙwayar idonshi. A hankali Haroon ya matsosu. Cikin sanyi yakai hannunshi ya kamo hannun Ya Jafar ɗin. Kanshi ya ɗago ya zuba mishi ido. Murya cike da rauni Haroon yace. "Ya Jafar tashi kazo muje masallaci lokacin salla yayi. Muje muyi salla muyiwa Sheykh Jabeer Addu'o'in samun lfy". Kanshi ya gyaɗa sabida in dai abu na ibadane to bai kasance jiɓeɓɓe a kanshi ba. Sunkuyo wa, yayi ya sumɓaci goshin Jabeer kana, ya sauƙo kan gadon. ƙofar Bathroom Haroon ya nuna mishi da yatsa. Shiga yayi bayan ya fitone, shima Haroon ya shiga ya sabunta al'wala kana, suka fita. A babban falon suka samu, Aunty Juwairiyya da Jakadiyarsu suna shirya musu abinci bisa dinning table. Cikin kula Aunty Juwairiyya ta kalli Haroon murya a sanyaye tace. "Haroon ya jikin nashi dai?". Ɗan tsayawa yayi tare da cewa. "Alhamdulillah gsky zama muce ya worke, sabida ya amayarda duk wani dafin dake jikin bilalin yanzu naga shatin kunaman ma duk sun ɓace a jikinshi, ya zama sai shatin bulalin". Murmushi Jakadiyarsu tayi tare da cewa. "Suma nanda kwana uku in sha Allah babu tabonsu a jikinshi. Na gaya muku ai jinyar Shaɗi ba abu mai wuya bane a masarautar Joɗa, yanzu da asibiti aka kaishi, koda ko ƙasar waje za'a fiddashi a ƙalla sai anyi watanni uku ana jinyarshi, in yanada nisan kwana ya worke da kyar in kuma kwananshi sun ƙare ya cika a can. Amman yanzu yana tashi bacci zaiji sauƙin sosai". Cikin mamaki suka zuba mata ido. Jalal da Jamil da yanzu suka shigone suka haɗa bakin wurin cewa. "To wai Ummiy meyasa naga kamar farin cikin, abun kikeyi keda ko ruwan sama bakya son ya taɓa lfyarmu mu bare ɗan gatanki". Kanta ta ɗan jijjiga tare da cewa. "Abune mai duhu shekarun ku baiyi yawan da zaku gane haskenba, su kansu magautan Jabeer duk basu san ƙarfin iko da sani da shaharar wannan masarautar akan al'adun Shaɗi bane,." Jafar ne yayi gaba bayan ya duba agogon hannunshi ganin hakane duk suka bi bayanshi. A can
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185