Chapter 10
Chapter 10
dake cikin wani kekyawan tray dake gabanta miƙa mishi tayi tare da cewa "Jabeer Yaushene tafiyar taku?." Tankwashe kanshi yayi bisa kafaɗunshi kana a hankali ya ɗan kalleta tare da motsa laɓɓanshi a hankali yace. "jibi". ya faɗi mgnar a gajarce, gyara kishingiɗarta tayi bisa kilisan tum-tum dake gefenta, Cikin kulawa tace. "Da Umaymah zakuje ne?". Kanshi ya jujjuya mata alamun a a. Kanta ta rausayar cikin ƙasaita tace. "Naga kamar bacci kakeji Saida safe". Kanshi ya gyaɗa kana cikin girmamawa yace. "Allah ya bamu al'khairi". Amin tace, shi kuwa daga nan ya fita ya tafi. Koda ya koma sashinsa. A falo bakin ƙofar ya samu Jakadiya, tana ganinshi ta ɗan rusuna duk da tasan yana hanata hakan a hankali tace. "Akarmakallahu, Umaymah ce take biɗar mgna da kai, ta kirayi layinka ba'a ɗagawa, shine tace in kawo maka wayar". Kanshi ya ɗan sunkiyar a hankali yace. "Ummi kice mata tayi hakuri saida safe". Cikin mamaki jakadiya tace. "Lafiya dai ko Sheykh?". Kanshi ya gyaɗa mata alamar eh lfy. "To ba laifi zan gaya mata". Daga nan ta juya ta koma sashinta. Shi kuwa Sheykh Jabeer, daga bakin ƙofa ya dakatar da bayinshi. Kana cikin nitsuwa ya kallesu tare da cewa. "Sarkin ƙofar ka janye bayin dake bina da bin Jalal da Jamil, kaima ka koma can sashunku, ba'a buƙatar bibikon nan, in inada buƙatar ku Ummi zata sanar muku." Ciki girmamawa sukace. "To Sheykh". daga nan ya juya ya nufi ciki. Su kuma suka juya. Koda ya shiga ɗakinshi kai tsaye bathroom ya wuce wonka yayi tare da al'wala a cikin bathroom nashi da yafi makoncin wani kyau. Komai na bathroom ɗin glass ne mai ruwan garai-garai, bathroom ɗin katone, mai ɗauko da babban drower'n glass wanda yake cike da ƙananun kayan sirrin jikinshi kamarsu vets boxes and pants kana towels da rigunan wonka da jalabiyoyinshi masu masifar kyau da tsada da taushi da yawa, sai kuma 3 qtr da kuma turaruka dasu brosh da su makilin da dai sauran kayan buƙata na aske pravet part. Ko ina na kusurwan ban ɗakin da madubai. Bayan ya fitone, yayi shirin baccinsa cikin wani tattausan jallabiya mai masifar kyau da tsada, A bakin gadonshi na sarakuna ya zauna, idonshi ya zubawa woyoyinshi dake kan bedside drower' Woyoyin sun kai biyar, a hankali yasa hannunshin ya ɗauki ɗaya daga cikinsu data kawo haske, alamun ana kiranshi, Karawa yayi a kunnenshi tare da yin shiru. A can ɗaya sashin kuma kekyawar tsohuwar balarabiyace keta mishi faɗan ina ya shiga tana kiranshi bai amsawa. A hankali ya lumshe idanunshi tare da mirginawa ya konta tattausan gadonsa da shimfiɗar sa, wanda Jamil ke gyara mishi a koda yaushe, cikin harshen larabci yace. "Sitti raja'an!". shiru sukayi baki ɗayansu, can kuma sai yaci gaba da magana cikin larabcin, sawon 32 second yana maga kafin ya katse kiran, kana yayi laduban konciya bacci ya konta. Washe gari da safe da misalin karfe sha ɗaya na rana. Dawawonshi kenan daga fada, Yana shiga falonshi asalin falon dake gab da makoncinsa kiran Umaymah na shiga wayarsa. Ganin video call ne ya sashi, amsa kiran kana ya ajiye wayar kan Glass Stull dake gaban kujerar da yake zaune. Fuskar wata kekyawar Matace ya bayyana a fuskar wayar tashi, cikin sanyi ta zuba mishi idanu ganin yadda ya tonƙoshe wuyanshi bisa kafaɗunshi a hankali tace. "Jazlaan". Kanshi ya ɗan mirgina cikin wani yanayi ya jujjuya mata kai a hankali yace. "Jazlaan, Umaymah sai yaushe zan zama Jazlaan? Sai yaushe, Jazlaan zai wadaci rayuwarmu?". Murmushi mai ciwo a zuciya tayi tare da cewa. "In sha Allah nan kusa". A hankali ya lumshe idanunshi cikin sanyi yace. "Umaymah, kizo kafin mu tafi, ina so mu haɗu". Cikin tarin kulawa da tsananin ƙauna tace. "Menene matsalarka?". A hankali yace. "Ya Jafar...! Littafin na kuɗine. By *GARKUWAR FULANI* 📝🍇🍇🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘 *GARKUWA* PAGE 4 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 📝🍇🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘 *GAREKU MUTANEN NIGER, +22799460151 kuyi haƙuri an samu akasin number da nada bada, wayarta ta lalace. Yanzu ga number da zakuyiwa mgn +22799460151 300 ko 1k idan kun turata mata, saita turo min number ki/ka sai in saki/ka a group ɗin da kika biyawa🤝🏻. Gareku mutanen ƙasata ga number ta 09097853278, turo katin mtn na ɗari uku kacal, ko kimin TRANSFER ɗin darinki uku ko 1k ɗan samun SP Group. In kin biya sai kiyi screenshort ki turo min shaidar biyan kuɗin littafin GARKUWA ta wannan number dai 09097853276* Cikin nitsuwar da ya kasance halittarsa, ya ɗan ranƙwafar da kai yayinda fuskarshi ta ɗan sauya yanayi murya can ƙasa yace. "Ya Jafar! Yana buƙatar kulawata, baya son nayi nesa dashi, Umaymah Jalal da Jamil basu da hankali yaran basu da nitsuwa Umaymah basu san ciwon kansuba Affan kuma baya nan". A hankali wacce ya kira da Umaymah ta gyara zama cikin tarin kula da bege da tausayi da ƙaunar Jazlaan ɗin nata cikin tausasan laffazi tace. "Daɗewa zakuyi ne Jazlaan?". Hannunshin yasa yana ɗan shafa sumar kanshi cikin rumtse ido murya can ƙasa yace. "Sitti tace zamu daɗe a can, kuma Maimartaba ta gayawa kai tsaye, shi kuma ya faɗawa Abba kai tsaye umarni suka bani". Kai ta ɗan rausayar tare da cewa. "Ba komai Jazlaan in sha Allah babu abinda zai samu Jafar, in kaje kayi ta mishi addu'o'in kamar yadda ka saba, in sha Allah yana cikin kulawa da kariyar Allah". Kanshi ya ɗan gyaɗa mata, Domin bai fiye yawan maganaba in ba amɓaton Allah ba, dan ma ta kasance cikin mutun biyar ns duniya da yake iya yin doguwar magana dasu, musamman Maimartaba da mafi akasari faɗa ke haɗasu, sai ita sai kuma Umminshi Jakadiyarsu kenan wacce tun yana jariri itace uwar rainonshi sai Sitti da Jadda". shiru ta ɗanyi tana kallon yadda ya lumshe ido tamkar bazaiyi magana ba, bata dai katse kiranba har tsawon 3 minutes kafin ya ɗan motsa laɓɓansa ba tare daya buɗe kwayar kekyawan idanunshi yace. "Umaymahhhh". yadda ya kira sunanra ya tabbatar mata halin da zuciyarshi ke ciki, tafi kowa na duniya sanin matsalarki Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero. Cikin kulawa tace. "Na'am Jazlaan". tashi yayi zaune a hankali ya fuskanci wayar tasa da kyau, hannunshi ya haɗe wuri ɗaya tare da cewa. "Umaymahhhh Jalal". Cikin kulawar da ƙanwar uwa shaƙiƙiya kan iya bawa ƴaƴan ƴar uwarta, da tarin son da takeyiwa ƴaƴan ƴar uwarta Tata, musamman shi Sheykh, a hankali tace. "Me Jalal yayi". Kanshi ya ɗan ranƙofar tare da cewa. "Umaymahhhh Jalal bayaji, ya fiye gagara, da son jawowa Ahlinmu abin faɗa. Ɗazuma kwalaɓen giya fa ya shigo dasu cikin masarautar da ta kasance tsarkakkeya. Ga Jamil kuma babu nitsuwa tattaredashi, duk inda yaga mace, jikinshi na rawa yakebi ya zama kamar ɗan akuya, Umaymah in nayi nisa da gida, zasuyi abinda zai sasu a matsalar rayuwa". Wani dogon ajiyan zuciya Umaymah ta sauƙe a hankali tace. "Kada ka damu, in sha Allah babu abinda zasuyi da izinin Ubangiji rayuwarsu bazata lalaceba kodan addu'o'in da kakeyi musu, da irin tarbiyar da kake basu". Kanshi ya gyaɗa tare da taune lips ɗinshi na ƙasa yayinda lokacin ɗaya kwayar idanunshi sukayi wani irin kala su ba jaba sunba fariba. Cikin rauni miskilar muryarshi yace. "Na sanifa Umaymah babu abinda sukeyi, nasan Jalal ba mashayin giya bane baya shan komai,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185