Chapter 96
Chapter 96
sallama?". Wani mugun kallo ya watsa mishi tare da cewa. "Kiyaye bakinka idan maza suna wuri." Cikin dakiya Salmanu yace. "Ina mazan!? Ai ni banga wani na miji a nanba sai mata maza. Ai namiji shi zai iya sa namiji ɗan uwanshi zubda hawaye ko tsuma da faɗuwa, a dai yanzu ai babu wani namiji a Rugar Bani da kewaye sama da Jarumin da bulalar SHAƊI bata sashi zubda hawaye ba Sheykh nake nufi". Wani irin zabura Ba'ana yayi ya nufi kansa alamun zai shaƙeshi. Da sauri ya tsaya jin Shatu ta saki ihu tare da cewa. "Bana so ya Ba'ana in dai kana son farin ciki na, to kada ka dakeshi ko ka cutar dashi da komai". Wani irin kallo ya mata mai cike da tuhuma da razana da kuma karaya, Ita kuwa Shatu cikin rawan murya tace. "Ya Salmanu ka tafi, bana so kaje ka bar koya min komai". Cikin sauƙe ajiyan zuciya na tsoro. Salmanu ya juya ya tafi. Shi kuwa Ba'ana, zama yayi inda Salmanu ya tashi, cikin taraddadin ko dai Shatu bata sonshi ne, ya nuna mata gefenshi. A hankali ta zauna, shiru tayi tana sauƙe shessheƙan kuka. Cikin ƙuna da baƙin cikin rashin sa wancan ɗan birni mai fata kamar ta jariri kukanne ya sakar mishi fargaba, cikin sanyi yace. "Mata!". Bata kalleshi ba kuma bata dena shessheƙan ba. Kiranta ya kuma yi a karo na uku. "Mata!". Cikin disashewar muryar tace. "Na'am". Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau a hankali yace. "Mata bakya so nane!?". A bazata tambayarshi tazo mata, ta ina kuma ta yaya zatace mishi bata sonshi, bayan tasan abin da yayi mata shekarun baya, dama fansar shi ta soshine kuma ta aureshi, da wanne bakin zatace mishi bata sonshi. wasu zafafan hawaye masu ɗumi ta zubda. Haƙiƙa ya Ba'ana mugune amman a iya saninta a kanta ya zama mugun, tunda sai wanda ya nuna baya sonta dashine yakewa mugunta, Babbar matsalarshi mushirkine kuma baya salla. Cikin rawan murya da kuka tace. "A a Ya Ba'ana Ni bance bana sonka ba". Da sauri yace. "Uhhmmm to meyasa bakya ganin laifin Salmanu akan duk abinda yake min, ko dai shi kikeso ne Mata!?". Da sauri ta jujjuya mishi kai sabida sanin ko jinkirin bashi amsa tayi zai iya yiwa Salmanu illa. Cikin rawan murya tace. "Bana son ka cutar da shine sabida, shi ya janye batun soyayyarsa gareni. Ka kuma sani karatu yake koya min amatsayinshi na wanda ya samu karantarwa a wata jami'a, Yana sona da al'khairi kai kuma kana ƙinshi, ko dai ka manta ka ce min zaka so duk wanda yake sona da al'khairi yake kuma taimaka min". Jiki a mace ya gyaɗa mata kai, sai kuma ya rumtse idanunshi da yakejin suna cikowa da hawaye yace. "Lokuta da dama sai inga kamar bakya farin cikin ganina, a madadin farin ciki sai inga tsorona cikin ƙwayar idonki." Juyowa tayi gareshi da kyau cikin kuka tace. "Ba kai ke bani tsoroba, abinda kakeyi ne yake sani tsoronka, ya Ba'ana ka bar wannan asirce-asircen babu kyau shirka ne, wanda yake ɗaya daga cikin manyan zunuban da Ubangiji ya haramtawa mumini yin tsafi haramun ne". Kanshi ya jingina da jikin gini yana kallonta tamkar yau ya fara ganinta, A hankali ya fara mgna cikin muryar da bata taɓa jin rauninta a muryarsa ba yace. "Mata ina sonki, wallahi Allah kenan rantsuwar musulmai, ina sonki, son da ni kaina bansan adadinshi ba, Duk abinda nakeyi a kanki nefa, Shatu ki min uzuri, na roƙeki kiyi min ɗa'ar riƙe tukuicin abinda nai miki a baya, Ki soni koda rabin yadda nake sonki ne. Kiji tausayina Shatu ina jin tsoron kada ƙaddara ta rabamu,". Kekkyawar fuskarshi ta zubawa ido, tana gani. Irin kyan da Allah yayi mishi sai dai sam babu kyan hali ya zama kyan ɗan maciji. Cikin sanyi tace. "Ya Ba'ana tsoro kuma?". Kai ya gyaɗa mata cikin sanyi yace. "Eh sabida muddin aka rabamu, zan zamewa fulani babban ƙalubale a rayuwarsa, kuma duk wanda yayi sanadin rabuwata da ke, wallahi zaiga toskun rayuwar duniya, zaiyi dana sani, zan zama mugun zahiri. Na san ke Kum bakya son hakan. Yau kuma fargaba na, yafi na baya yawaita da wannan jikan sarki ya iya daurewa azabar bulalina baiyi ƙollaba." Wani irin ajiyan zuciya taja tare da cewa. "Babu komai ya Ba'ana Ni dai ina tayi mana addu'an ALLAH yayi mana zaɓi mafi al'khairi a rayuwata, ya kuma shige min gaba a dukkan motsina". Ido ya zuba mata babu ko ƙebtawa, cikin sanyi yace. "Nine mafa al'khairinki Mata". Da sauri tace. "Baka saniba". A zafafe yace. "Na sani mana". Cikin tsoro tace. "Kai masanin gaibu ne kenan?". Miƙewa tsaye yayi tare da cewa. "Ehh kusan haka tunda nayi duba a kanki". A hankali tace. "Wa'iyazubillah. Duba ba gsky bane, zai iya maka ƙarya". Hannu ya ɗaga mata da sauri kana ya nuna mata hanyar shiga gida. A hankali ta tashi tsaye cikin sanyi tace. "Allah ya baka haƙuri ya shiryeka". Ta ƙarishe mgnar tana ƙoƙarin yin kuka. Da sauri ya juyo cikin sanyi yace. "Kada kiyi kukan mata, nayi haƙuri. yanzu na fasa jiran Sai kin gama karatu ayi mana aure. Duk randa wancan malamin ya dawo ya rama gasar Shaɗinsa. Za'a ɗaura auren mu a ranar, domin Koda duk bulalin duniyar nan zai zabgeni dasu wlh bazaici nasara a kainaba domin idona ba idon da zai zubda hawaye a kanki bane bilali ɗaya nake tsoro kuma babu wanda yasan inda suke. In kuwa aka samu wani akasin dama bazai samuba, to zan bar ƙasar nan zan koma ƙasar Cameroon can babban birnin Yahunde, inbi cikin Rugar wasu fulanin. Sai dai ko bana nan duk wanda ya aureki ya auri ajalinsa." Bata iya tanka mishiba, a haka ya juya ya tafi. Kana ita kuma ta koma cikin gida. A cikin masarautar Joɗa kuwa. Sai da akayi sallan isha kafin. Su Haroon suka dawo gida. Suna tafe, Abba da Lamiɗo da Galadima, da Dr Aliyu da kuma Sarkin Shaɗi. Suna biye dasu a baya. Kai tsaye wucewa sukayi har bedroom ɗin Jabeer har yanzu bacci yakeyi. Sai dai tunda lokacin salla yayi yaketa jin baccin ba daɗi sai dai kuma Allah bai bashi ikon farkawa ba. Dubashi sukayi tare da ƙara shafa mishi wasu magunguna kana suka fita suka tafi. Hakama Gimbiya Aminatu tazo itama har ɗaki sai dai samunshi yana bacci yasa ta tafi. Bayan fitanta ba daɗe Barrister Kamal da ɗan sa Sulaiman sukazo. Suma har ciki suka shiga suka dubashi. Kana suka tafi. A ranan a daren gaba ɗaya mutanen masarautar kowa yaji lbrin abinda ya faru. A falon su Jafar duk sukaci abinci. Ganin dare ya tsalane yasa Juwairiyya jan hannun Jafar suka tafi. Jalal, Jamil, Ya Hashim kuma sukayi musu saida safe kowa ya tafi side ɗin shi. Jakadiyarsu kuwa itama ta nufi sashinta, Ya zama dagashi sai Haroon. Sha biyu da rabi dai-dai na dare. Haroon zaune kan wata doguwar kujera irin ta sarakuna dake cikin ɗakin. Waya yakeyi da Jannart, yana konce ne dagashi sai boxes. Waya sukeyi irin ta mosoyan da shaƙuwarsu tayi yawa, Wani irin miƙa yayi wanda gaba ɗaya gabban jikinshi suka amsa. Cikin tarin kasala da masifeffen shauƙi yace. "Wash Allah na". Cikin kashe murya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185