Chapter 162
Chapter 162
cewa. "To ni kam ga tsaraba ka kai musu, wannan na Shatune Hibba gobe zan dawo da nata. Kai kuma in kaso ka koma hannu rabbana". Kanshi ya sunkuyar kamar baijiba. Sai kuma tace. "Jazrah tace in gaidaka, wai tunda kazo bata ganka ba". Cikin sanyi yace. "Yoh dama ya zanyi in bari ta ganni yarinya sai kallon masifa". Miƙewa Umaymah tayi ta fita. Tana fita Haroon da Ya Hashim suka shigo. Nan suka ɗanyi hira kafin suka tashi suka tafi masallacin dan shabiyu ta kusa a fara tuhajjudin. Nan suka tafi. Washe gari aka tashi da azumi na talatin. Allah cikin ikonshi aka kaishi lfy. Watan Shawwal ya baiyana Ramadan ya tafi kuma sai mai nisan kwana. Shatu kuwa a wunin ranar Yar aikin Aunty Juwairiyya Sato, ta zana mata jan lalle mai ɗan karen kyau. Koda ta dawo kuma jarakuna madarar shanu data gayawa Gimbiya Aminatu tanaso Aka kawo mata ta tafasashi kana tasashi a manyan kware da ƙananan kwore da kyawawan robobi tasa tsami kaɗan a ko wanne kwarya da roba. Ta rufesh ta jerasu a Fridge a ƙalla sunfi kore goma madaidaitan ƙananan sun kai kore takwas sai robobin su kuma sun kai goma suma. Bayan sallan magriba ansha ruwa anyi nak. Hibba sai tsalle da farin ciki da kiraye-kirayen ƙawaye da yan uwa da abokai sai tsiya Jamil ke mata. Bayan sun gama shirya komai na aikin da zasuyi gobene. Suna zaune a falo Ummi ta kalli Jamil tare da cewa. "Jamil wai sai yaushe zaka share Side ɗin Sheykh ne, munyi waya da Umaymah ɗazu tace min gobe fa zasu dawo. Anayi sallan idi a can zasu taso". Gyara zamanshi yayi tare da cewa. "To naga mutun ga matarsa ace Ni in mishi shara". Ko inda suke Shatu bata kalla ba. Ummi kuwa jingina tayi da jikin kujera tace. "Ai bazata san ƙaidar yadda yakeson a gyara mishi ɗakinshi ba. Dole sai ka nuna mata." Cikin gamsuwa da hakan yace. "To ba matsala sai gobe da sasafe mu hau kan aikin abinda ɗakin ba wani ƙura da tarukucene da shiba". Eh hakane Ummi tace tare da kallon Shatu tace. "Gobe in Allah ya kaimu Shatu ku gyara mishi ɗakin nashi". "To Allah ya kaimu. tace ba tare da ta kalli inda sukeba. A can ƙasa mai tsarki kuwa. Ana idar da sallan isha'i da yawa suka fara ɗawafi. A cikinsu kuwa harda Sheykh Jabeer da mai sunanshi kana da Haroon A nitse bisa tsari suke ɗawafin sunje ƙafa biyu ana uku sun isa dai-dai. Maƙama Ibrahim. Sheykh Jabeer ya juyo kanshi ya kalli gefen damanshi da sauri cikin tarin mamaki al'ajabin Fuskar mutumin da ya ga ya wulgawa a idonshi...! Littafin GARKUWA na kuɗine idan kina buƙatar saya ga number 09097853276 katin mtn na ɗari uku. Normal group in kuma special Group kikeso 1k zakiyi min TRANSFER ta ac ɗina 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. By *GARKUWAR FULANI* Cikin sassarfa bisa tsarin addinin yaci gaba da ɗawafin. Yana mai bin bayan tawagar mutanen da yaga fuskar wannan mutumin a cikinsu. Idonshi yaketa karkasawa amman ina ya kasa sake ganinshi. Zuciyarshi nike da mamaki. Haka yaci gaba da ɗawafin. Saida sukayi. Kana suka fito. A hanyarsu ta komawa gidane ya haɗu dasu Jannart da Jazrah da Umaymah da Sitti da kuma Aunty Hafsat ƙanwar Umaymah dake ƙasar Masco. nan Aunty Hafsat tayi ta sayan kayan tsaraba tana bawa Sheykh wai a kaiwa surkarta. Dan dole ya amsa sai kuma Aunty Rahma ƴar autar Sitti itama a gaban Aunty Hafsat ta girma. Kuma sa'ar Sheykh Jabeer ce shiyasa akwai yar tsama a tsakaninsu. Cikin hausarsu data fara basu wuya tace. "Ba dai kayi auren sirri ba, in sha Allah zanzo zamuzo auren Haroon zamuga amaryar, inga surkar tawa ya take" Taɓe baki yayi tare da cewa. "Ke tafi daga nan da Allah ki bar manya suyi mgna ba irinki ba". Murmushi Umaymah da Aunty Hafsat sukayi dan sun san tsamarsu. Kuma suna masifar shiri. Ammi suke kiranta ita Aunty Rahman. Jazrah kuwa hakanan take jin daɗi in ta ganshi. Shiyasa taketa murmushi. Haroon kuwa girarshi ya ɗagawa Jannart tare da cewa. "Wai auren ya kusa ko?". Cikin jin kunyar Umaymah tace. "Ban saniba." Haka dai sukaci gaba da tafiya. Washe gari da safiya. Duk kan al'amur musulmai na duniya suna farin ciki da ranar salla. Manya da yara tsoffi maza da mata duk anata shirin zuwa idi. A dukkan ƙasashen duniya a ko wani saƙon da suke da musulmai. Hakace ta kasance a ƙasashen Afrika ma. Wanda ciki ƙasar Nigeria yake. Tun daga idar da sallan asuba. Saratu da Larai sukazo. Nan suka samu Ummi da Shatu suna kitchen. Its Ummi fura take kirɓawa mai ɗan karen laushi da ƙamshi yaji sugar. Ita kuwa Shatu dakkeren Couscous tayi, dambu inji hausawa. Bayan sun gamane suka killace shi gefe. Kana ita Shatu. Ta haɗa kajin nan tayi Pepper Checken mai ɗan karen kyau yaji jajjagen taruhu da al'basa mai yawa ga kayan ɗan-ɗano dana ƙamshi sunji komai yayi maɗau. Su Sara kuwa robobi ta miƙo musu, suka rinƙa mulmula gumbar nan manya manyan mulmulellen masu kyau sai sheƙi da ƙamshi gumbar keyi, dakkeren kuma a robobi Ummi ta rinƙa zubasu. Hibba ce data shigo tare da kuloli a hannunta tace. "Wow Aunty Shatu lallai yau masarautar Joɗa zata amsa sunanta masarautar Fulɓe zata kuma gane an auro mata cikekkiyar ba fulata, gsky tsarin yayi kyau". Cikin jin daɗi Ummi tace. "Gsky nima naji daɗin wannan abu. Dama ace ko wanne yare ranar salla tayi abincin da yarenta keyi ta rabawa maƙota. Hakan zaisa asan cimar juna, kuma yasa aci abincin salla da marmari, amman kayan haushi duk sai a tafi kan shinkafa taliya masa, da dai ire-iresu. Su kuma akeci kullum". Murmushi Shatu tayi tare da cewa. "Ha Ummi ai yanzuma sai nayiwa su Jalal koda dafadukan taliyace, nasan zasuce wannan ai sai mu". Da sauri Hibba tace. "Tab wlh Aunty Shatu karkiyi komai, kinga yanzuma an kawo abincin gidan Barrister Kamal. Ga kuma na gidan Aunty Juwairiyya. Sannan kuma Gimbiya Aminatu ma zata aiko". Cikin sauri tace. "Allah ko Ummi mu huta kawai kenan?". Da sauri tace sosaima. Dan duk yawanci sai an kawo abinci nan wai tunda ke baƙuwace, wannan karamawar masarautar Joɗa akan bago. Kuma koda kin dade ana aikawa juna abincin salla part 2 part". Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa. "Shike nan mu haɗa wannan a kai ko wanne sashin". Ta ƙarishe mgnar tana rufe ƙatuwar Foodflaks ɗin da ta juye Pepper Checken ɗin. Bayan ta ɗebawa sashin Ya Jafar da kuma Lamiɗo da Hajia Mama. Ƙananan robobin da a ƙalla suma nonon dake cikinsu zai kai kwanon sha ɗaya da rabi ta fara firfitarwa. Kana ta fito da madaidatan ƙoren da zasuci kwanon sha biyu da kaɗan sai manyan da sukaci kwanon sha uku da rabi-rabi. A hankali ta jerasu kan table ɗin dake tsakiyar kitchen ɗin. A hankali ta buɗe ƙwaryar forko dake gabanta. Wani irin murmushi tayi tare da cewa. "Alhamdulillah kunɗirmo ya konta yayi bacci yayi kyau". Leƙowa Ummi tayi tare da buɗe na kusa da ita. Nonon yana konce yayi lib ya daskare yayi fari ƙal-ƙal sai alamun maiƙon man nonon da yayi ɗan yellow-yellow
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185