Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 75

Chapter 75

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a lokacin Haroon ya kuma saɓan mota suka fara kita hanyan kawoshi Adamawa. Wanda sai ƙarfe uku da rabi suka isa. Kasamcewar dama basu taso da wuriba. Kasancewar isar dare sukayi babu wanda yasan Sheykh ya dawo. Ƙasar sai Lamiɗo da kuma hadimanshi, uku kacal da sune suka tarbesu. Sai washe gari da. Asuba, sautin muryarsa yana karatun limancin Sallah asuba ne ya shaidawa mutanen masarautar Joɗa dawowanshi. Gaba ɗaya kowa ya cika da mamakin, kana da farin cikin dawowanshi. Duk da kasancewar sa, mai larurar da wasu ke mishi kollo ko kiranshi majanuni, yasan kiyaye lokacin salla dama yinta cikin kushu'i. Wannan shine ya hanashi sallame sallar, da akeyi yana cikin sahu na tara, wanda jin muryar ɗan uwanshi ƙaninshi, ya sashi zubda hawaye masu ɗumi. Ya Jafar kenan. Jalal kuwa dake gefenshi wata irin sassanyan ajiyan zuciya ya sauƙe tare da lumshe kekyawan ƙwayar idanunsa da suke iri ɗaya dana Sheykh, ga kuma bacci daya cikasu, domin daren jiya, Ya Jafar ɗinsu ya hanashi bacci. Jin muryar ɗan uwansu da shi kaɗai ke iya sarrafa babban yayan nasune ya sashi sauƙe, numfashin. Jamil da Affan kuwa, wani irin yalwataccen murmushi ya sake jin muryar ɗan uwansun. Abbansu kuwa, shi dai har yau yana rasa me yakeji a kan ƴaƴan nashi, Especially Sheykh, yana jin zuciyarshi na mishi nauyi duk sanda yaron baya kusa dashi, sai dai kuma in yana kusa dashi sai yaji tamkar bai taɓa wani farin cikiba a rayuwarsa. Ya sani tabbas su abun tausayawa ne, suna buƙatar kulawarshi fiye data kowa a duniya, to amman ya rasa meyasa yake jin kamar baya son kusancisa dasu. Maimartaba kuwa, suna cikin sahun na forko bayan liman, Sai da sauran malaman fada. A cikin gida kuwa, jin sautin zazzaƙar miryarshi yana rere karatun al'ƙur'ani, ya ida fatiha, kana ya ɗaura, Arrahama, daga bisani ya rufe da lakadja'akum, kafin ya tafi zuwa ruku'uh. Haka nan Juwairiyya ta tsinci kanta da zubda wasu zafafan hawaye, masu ƙuna a rai, tabbas ta sani. Kasan cewar Sheykh a masarautar nanne kaɗai yasa, suke a ciki. Ta sani in badon daraja da al'farmarsa ba, da tun tuni, an tabbatar da sunan mijinta mahaukaci. Hannu tasa ta share hawayenta cikin sanyi ta miƙe dan gabatar da sallan asuba, a zahiri tace. "Allah ne gatanmu, kaine GARKUWAR mu, Sheykh in baka nan gidan kanyi mana duhu, ƙasar tanayi mana zafi." Daga nan ta tada kabbara. Ummi Jakadiyarsu kuwa, Tana bayan gida, tana al'wala ta jiyo muryarshi, wani irin murmushi tayi tare da yin mgna a baiyane. "Dan Halak kaƙi ambato, ɗa ɗaya tamkar dubu, maƙiyanka fadawanka, sunyi sake ɗan zaki ya girma, in sha Allah zaka dawo da farin cikin masarautarnan, sunyi sake, sun bar kari tun ran tubani, Muhammad Jabeer bawan Allah". Haka ta fito tana wasu irin kalamai masu wuyar fahimta. A can sashin Hajia Mama kuwa, Wata kekyawar budurwa, ce. Konce kan gado gefen Mama, datake zaune bisa sallaya. jiyo muryashine ya sasu saurin juyowa, suka kalli juna, Cikin tsananin farin ciki da tarin shauƙi budurwar ta diro daga kan gadon gaban Mama ta zauna cikin zaƙuwa tace. "Lah Mama, yaushe ya dawo! Muryar Sheykh Jabeer nake jifa! Mama ko dai dama yana nanne?". Wani irin kallo Mama tayi mata cikin sanyi da murmushi a fuskarta tace. "Batul shine, ya dawo!." Wani irin sassanyan numfashi ta sauƙe cikin tarin shauƙi tace. "Yes Mama, farin cikina ya dawo, kamar yasan, nazo. Alhamdulillah, Mama Allah yana sona, ki gani ina zuwa, na samu baya nan, naji baƙin ciki kamar in mutu jiya kafin inyi bacci, sai gashi Allah ya turo minshi cikin dare ɗaya." Murmushi Mama tayi, tana mai jin mmkin yadda Batul ke masifar son Sheykh har take gaza ɓoyewa. cikin haɗe fuska tace. "To yanzu dai, sai ki tashi kiyi salla, tunda kinji muryar da kikafi so a duniya, kin sauƙo kan gadon, sau nawa ina tadake, sai kiyi miƙa ki kuma konciya". Cikin jin dadi tace, "Wayyo Mama baccinne bai isheniba Allah ko jiya kwana nai ina zulumi, sai 3:44 na asuba na samu bacci." Murmushi Mama tayi kana ta miƙe ta kabbarta sallan. Ita kuwa Batul, miƙewa tayi da sauri ta shige, bathroom tana cewa. "Bari inyi wonka inyi salla, in shiga kitchin yau nida kaina zan mishi breakfast." Tana faɗin haka ta shige ciki. A masallaci kuwa, ana idar da salla kamar koda yaushe, da yawa basu fitaba saida sunata lazumi. Yayinda Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero da kuma Sarki Nuruddeen Bubayero, da Habibullah Nuruddeen Bubayero, suka jero, suka fito a jere, domin su kullum ana idar da sallan asuba, suke fitowa su koma cikin masarautar, inda kowa zai wuce Side ɗinsa, Yayi karatun qur'ani da kuma, Dua Azkar, inda har sai rana ta fito, kana suke ɗan maida bacci, to kuma sudayin breakfast sai 11. Suna isowa tsakiyar masallaci, Sheykh yaji an ruggumeshi ta baya, yasan mutun ɗaya ne rak zai mishi haka a cikin masallacin, Ya Jafar ɗinsu. Yana juyowa kuwa yaga shiɗin ne. Ruggumeshi yayi gam-gam Jalal, kuwa ido ya zuba musu, shi kuwa Sheykh hannu yasa shima ya ruggume ɗan uwan nashi. Yayinda ya zubawa Jalal kwayar idanunshi, ya rame sosai, hancinsa ya ƙara fitowa, sai sajenshi daya ƙara yin lib, da uban gashin daya tara, yayi wani kafurin aski. Ramar da Jalal yayi ta daki zuciyarsa sosai baya son ganin ƙannen nashi cikin halin matsala, a hankali ya janye kwayar idanunshi ya maidasu kan Jamil da Affan dake gefen damanshi, Calikan ƙanenneshi kenan ba, sheƙiyancinsu ɗaya, baki suka haɗa wurin cewa. "Sabahul Noor Al'Sheykh". A hankali ya ɗan motsa laɓɓansa, yana mai kallonsu yace. "Sabahul khair ya Uktih". murmushi sukayi, suna mai jin son ɗan uwan nasu, Abbs da Maimartaba kuwa, kai suka ɗan jinjina kana sukayi gaba, Ganin hakane suma suka bisu, a baya, shi kuwa Sheykh hannu yasa ya shafa kan Imran da yanzu ya iso gabanshi cikin sanyi yace. "Hamma Jabeer barka da safiya". jin yana shafa kanshine ya sashi lumshe ido, inama ace yadda Hammanshi ke nuna mishi so haka zai shirya da Mom ɗin shi, yana masifar son ɗan uwanshi baya jin daɗin yadda yake ganin wata iriyar mu'amala tsakanin Mom da yayunshi. Ganin Sheykh yaja hannun Ya Jafar sun tafine yasashi bin bayansu. Ƙofar dake cikin masallacin wacce zata ɓulla cikin masarautarsu sukabi. Suna shiga, kowa yayi sashinsa sabida sun sani ko sunbi Sheykh yanzu ba lokacin mgna bane, karatu zaije yayi. Shi kuwa Sheykh yana riƙe da hannun Ya Jafar ɗinsa suka shiga side ɗinsa, inda ya samu hadimai masu tsaron ƙofar, suna tsaye. Suna shiga, tamtsetsen falon nashi kai tsaye ya nufi wannan babbar kusurwar da zata sadashi da. Big part ɗin shi, Suna shiga suka ɓulla cikin wani mashahurin, falo, wanda yaketa tashin ƙamshi mai masifar sanyi da daɗin shaƙa, a hankali ya zauna bisa kujerar 3 str kana yaja hannun Ya Jafar ɗin suka zauna, tare. A hankali ya juyo kanshi ya zuwa ɗan uwanshi idonu, Karatu yakeyi kamar koda yaushe, yanayi cikin tsantsar lugga da tajwid, kana ga kushu'i, Suratul yaseen yake karanta, bisa alamu kenan ya kusa yayi sauƙa, domin step by step yake bin surorin, in yayi sauƙa sai ya sako daga sama, baya mancewa, kuma baya birkitashi, Wannan rahamar da

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});