Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wanda ko uwa iya son da zatayiwa ɗanta kenan, tana ji dashi tamkar ranta, wata ƙil hakan baya rasa nasaba da tsananin kamanni da yakeyi da mahaifinta wanda shine baida lfy yanzu kuma shine tsohon Limamin Harami yanada zuriya mai tarin yawa yayansa na cikinsa zalla su arba'in da bakwai. Bar jikoki da ƙanne da yaran yan uwa, sai dai ya tsufa sosai tun shekaru ashirin da suka gabata ya ɗaura babban ɗanshi wanda yake ƙanin Sitti ne uwa ɗaya uba ɗaya a matsayin shi. Zuwa yanzu tsotsai tsufa ya kama Sarki Abdulkarim, Hairan wanda yake da shekaru ɗari da biyar a duniya, sai dai sufarsa suface mai tsabta tsuface da ka gani kasan an rainin ƙuruciyarta da tsoron Allah da ibada. Shiyasa babu gigita ko fita haiyaci, yana son diyarsa Sitti kakarsu Sheykh kenan so mai tarin yawa ko dan tayi nesa da shine, wacce ita kuma tun tanada shekaru ashirin da uku, Sarkin Musulmai na ƙasar Kautal na wancan ƙarnin yazo da babban ɗansa, Jalaluddin wanda a nan yaga UmmuKulsum Sitti kenan, ya sota, kuma Allah cikin ikonsa suka dai-dai ta, haka yasa kafin ya koma ma da amaryarshi ya koma dan sitti ta kafe ita dai tana son Bahaushen ga, duk da tasan yanada mata biyu, tace ai a gidansuma bata tashi ta samu mahaifiyarsu ita ɗaya ba. Tuni ita kam Allah ya mata rasuwa mahaifiyar Sittin kenan, yanzu mahaifinta ne kadai a raye, sai kuma ƙanninta da yake matsayin ɗaya daga cikin manyan limaman harami a yanzu sai sauran zuriyarta da yayu da kannenta. Kowa na ahlinsu yasan Sheykh domin Sitti tana yawan zuwa dashi tun yana ƙarami, kana tana zuwa da sauran ma baki ɗaya, to shi Jabeer anan ƙasar saudia ya haɗa digiri ɗinshi na forko dana biyu. Shiyasa ya zama duk zuriyar an sanshi farin sani, ga kuma tarin kama da yakeyi da mutanen zuriyar wanda da zaran ka ganshi kasan jininsu ne. Tafiya mai tsowo sukeyi cikin sararin samaniya suna keta gajumare, a ƙalla tsawon aha huɗu kenan suna tafiya. Kafin suka sauƙa cikin babban Airport ɗin jidda, wanda yake tamkar zai fashe da jirage, ko wacce ƙasa ta duniya tanada jirginta cikin wannan babban Airport ɗin, tashin jirage da hawa da sauƙansu tamkar babu wani abun hawa a duniya sai jirgi. Koda suka fito daga jirgin, wani jirgine na musamman suka shiga wanda yake daga fadar Mai Alfarma masarautar garin. Wanda ya turo a tarɓi ƴar uwar abokinshi da mahaifinsu keta begen gani. A take suka shiga jirgin ya wuce dasu, asalin cikin garin makka, wanda pilot ɗin kuma ɗane ga Umaymah ƙanwar Mamansu Sheykh wato shima jikan Sitti ne ɗan Umaymah sai kuma Jannart wacce ta biyo Haroon Dan tarban kakar tasu wacce ita kuma ƴace ga babban ɗan Sitti wato ƙanwar Juwairiyya ce kuma anan take karatu. Suna sauƙa a Airport ɗin, suka fito, a jere, yana gaba yana rike da hannun Sitti tana biye dashi a hankali tana taka step ɗin Jannart kuwa tuni itace a gaba. Haroon ne wanda yake biye dasu a baya yana kallon yadda kakar tasu ke taka step da kuma yadda ɗan uwan nashi ke rike da hannun ta, murmushi yayi tare da jingina a ƙofar bakin jirgin cikin harshen larabci yace. "Ko dai zaka goyeta ne ka sauƙar da ita". Sheykh bai kulashi ba, har saida suka sauƙo ya gyarawa Sitti tsayuwarta, kana ya miƙawa Jannart hannun Sitti alamun ta rike musu ita. Cikin jin daɗi Jannart ta riko hannunta tare da cewa. "Ana Uhubbiki ya Sitti". Cikin jin daɗi da son jikokin nata tace. "Ana". Sai kuma suka juyo suna kallon Sheykh dake tsaye cikin shiga ta al'farma shigar salihan bayi, wata dandatsetsiyar al'kyabbace mai masifar kyau ruwan ƙasace al'kyabbar sai surfani da aka sarrafa a jikinshi wanda yake da kalan gold, haka takalmanshi da hiraminshi duk masu ratsin Golding color ne, cikin tsananin jin daɗi Haroon ya fara sauƙowa daga step ɗin, yana kallon ɗan uwan nashi manda suke sa'anni, ruggume juna sukayi, cikin jin daɗi Haroon yace. "Marhabin da zuwa Al'Sheykh, ya gida?, ina ƙannena? Yaya jikin Ya Jafar? Ya Hajja Mama da kowa da kowa." Kwaɓe fuska ya ɗanyi tare da janye jikinshi daga na Haroon cikin sanyinshi yace. "Duk in kana son ganinsu kaje Nigeria zaka gansu, kana nan kullum sai yawo a jirgi kamar turuwa a daji, duk ƙasashen duniya ka gama zagayesu". Murmushi Haroon yayi tare da cewa. "To ai dama na sani bakinka ɗaya da Umaymah'nka, zan koma ne in sha Allah, zan koma inyiwa ƙasarmu aiki, suma ai suna buƙata na". Fuskarshi ya ɗan kauda tare da cewa. "Da yafi kam". Juyowa sukayi jin Sitti na cewa. "Kai Haroon ku taho mu tafi, ka tsareshi da surunka tun daga nan ko?". murmushi Haroon yayi kana ya nufi inda take tare da cewa. "Oyoyo My Sitti". Kai ta juya tare da cewa. "Rabu dani ba kaga ɗan uwanka ka shareni ba". Ruggumeta yayi ta baya tare da cewa. "Na isa in share uwar gida ran gida a gidan Sarki Jalaluddin". Jannart ce tai dariya tare da cewa. "Sitti karki yadda da daɗin bakinshi". Hannunshin yasa ya ɗan dungure kan Jannart tare da cewa. "Kishi ko dan kinga gani ga uwar gida". murmushi Jannart tayi tare da jan hannun Sitti sukayi gaba, shi kuwa Haroon baya ya dawo ya saita da Sheykh suka fara tafiya a jere, duk wanda yaga salo da tsarin tafiyar Sheykh zai gane cewa jini na sarauta na gudana a jikinshi, zai kuma gane nitsuwa ta addinin musulunci da kamala da haiba na hasken imanin ya game jiki da zuciyarshi. A haka suka jera suna tafe, suna hira wacce ƙarfinta duk Haroon ke yinta. Suna tafiya kaɗan. Nan suka samu wasu irin zafafan tsala-tsalan motoci masu masifar kyau da tsada, suna jere a ƙalla sun kai goma sha biyu, motocine masu azabar kyau da sabunta da sheƙi da kyelli suna jere. Kana ga kekkyawa fararen larabawa yan uwa da abokai Da sauri suka rinka ɗan rusunawa suna, gaidasu Sitti da jikokinta, wani cikinsu ne da yake jikin wata dan datsetsiyar mota ƙirar Mercedes Benz maybach Exelero wacce kuɗinta zai kai kimanin $8 million dollars. Motace mai masifar kyau da tsada, tana da inƙancin da ko bilet baya shigarta. Bisa dukkan alamu kuma sabuwa ce dal. Direban dake jingine da ita ne yayi maza ya budewa Sitti bayan ta, a hankali suka ƙaraso gaban motar gaba ɗaya ma'akatan sunyi musu ƙawanya, cikin so da ƙaunar jikokin nata, ta yiwa Sheykh nuni daya fara shiga, ba musu kuwa ya shiga, motar, kana itama ta shiga sannan Haroon ya shiga, ya zamana sun sata a tsakiya, Jannart kuma gaba ta shiga gefen drivern, suna gama shiga aka maida ƙofofin motar aka rufe. Kana duk sauran hadiman suka shishiga motocin. Kana suka fara tafiya a jere-a jere, tafiya sukeyi cikin salama da nitsuwa da bin doka da ƙa'idar tuƙi, kai tsaye suka wuce tushen ahlin nasu. Wanda kafin su zoma, duk labarin zuwansu ya riski al'ummar family, kamar yadda aka saba, haka aka shirya musu tarba ta musamman an gyara sashin na musamman wanda nanne masaukin Sitti asali kuma sashin mahaifiyartace, anan cikin sashin kuma duk ahlinta da zaizo daga ƙasar Kautal nanne masauƙinshi, kuma

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});