Chapter 143
Chapter 143
salla zata zo. In ta gama aiyu kanta kafin ƙarfe goma dai zata tafi, sai anyi sallan azahar kuma zata zo. Daga nan kuma sai mun gama aikin buɗe baki, ta tafi dana Gimbiya Aminatu da nata, sannan sai ansha ruwa anyi sallan isha'i da asham sai ta dawo tayi yan wonke-wonken da taimaka mana aikin sahur, to in ta tafi kuma sai washe gari in anyi sallan asuba ta dawo." Cikin ɗan fito da idonta tace. "Wannan zirga-zirga haka Ummi to ta zauna anan kawai mana ta huta". Juyowa tayi ta ɗan kalleta kana tace. "Mijinki ba irin waɗannan mutanen bane, baya son a turo mishi yara suzo suyi ta zirga-zirga a kanshi, kinga duk lokutan da take zuwa basa haɗuwa." Baki ta ɗan taɓe tare da yin mgna a zuci. "Kai mutun komai tsari, wannan babu shakka baida gskya ne wannan ɓoye-ɓoyen waya sanima ko cin zan-zanane a jikinshi da saɗaure wata ƙil shiyasa yake kima tabka-tabkan Al'kyabbar ajikinshi dan ya boye abubuwan". Murmushi Ummi tayi dan ta lura Shatu bata san mgnar ta fito fili ba. Shiru Shatu tayi ganin alamun Ummi na jin wa'azin, Hakane yasa tayi shiru sabida kada ta takura mata. Ƙarfe ɗaya dai-dai na rana, akayi addu'a aka rufe taron sai kuma Goben in Allah ya kai rai. Da yawa mutane basu fitaba, mafi akasari Kur'anai suka ɗauka suna karatu. Kamar yadda Sheykh yakeyi. Ƙarfe ɗaya da rabi aka kira sallan azahar. Miƙewa Shatu tayi tare da cewa. "Ummi bari inje inyi salla zan zo muyi wata mgna". Cikin binta da ido Ummin tace. "To". Bayan anyi sallan azahar an idar ne, ta fito ta nufi ɗakin Ummi, ganin bata nan ne, yasa ta nufi falo, nan kuwa ta sameta zaune bisa kujera. gefenta taje ta zauna. Tana zama wata ƴar matashiyar budurwa ta shigo, cikin nitsuwa tazo ta rusuna gabansu tare da gaidasu, Cikin kula Ummi tace. "Yauwa Saratu kin zo ko?". Cikin nitsuwa tace. "Eh Ummi nazo ɗazu bakwa nan sai na koma sai yanzu na kuma zuwa". Kai ta jinjina tare da cewa. "Yayi kyau,". Inda Shatu take ta ɗan kalla tare da cewa. "Ɗiyata ga Saratu. Saratu ga Saiyada Shatu matar Sheykh Jabeer". Cikin mamaki da dariya sunan da Ummi ta liƙa mata wai Sayyada, ta kalli Saratu tare dake gaisheta cikin ladabi da biyayya, fuska a sake ta amsa. Cikin sanyi Saratu tace. "Ummi me za'ayi ne?". Gyara zama Ummi tayi tare da cewa. "Ki wonke shinkafar masa dama na jiƙata, kana ki gyara mana ganyen alaiyahu, sannan ki fere Arish. Sai kuma ki jajjaga kayan miya, ki yanka al'basa mai ɗan yawa." Cikin nitsuwa da bin umarni tace. "To Ummi". Ta ƙarishe mgnar tare da miƙewa ta nufi kitchen, tana shiga ta fara aiyukan da aka sata. A falon kuwa, gyara zama Shatu tayi tare da kallon Ummi cikin sanyi tace. "Ummi dama mgnar da zamuyi ko!." Sai kuma tayi shiru tana nazari, jin muryar Ummi nace mata, "Uhum ina jinki faɗi". Sunkuyar da kanta tayi a hankali tace. "Uhumm dama cewa, zanyi in ba matsala a rinƙa yin abun buɗa bakin ana kaiwa masallacin Masarautar Joɗa mana, tunda dole talakawan gari na zuwa nan sallan magriba." Murmushi mai yelwa Ummi tayi tare da cewa. "Allah sarki, Shatu mai tausayi, ba matsala amman ki tambayi mijinki in ya amince dai ba matsala, dama kuma ana fitar da abinci a sashin Gimbiya Aminatu, da Gimbiya Saudatu da kuma gidan Galadima, da Hajia Mama. Da gidan Dr Aliyu da sauran duka, kuma ko Juwairiyya ma tanayi". Murmushi ta ɗanyu tare da cewa. "To Ummi muma ai muna son ladan wannan aikin". Da sauri tace. "A sosai ma kuwa. Sai dai ki sanar da maigidankin in ya yarda yanzu incewa Saratu ta ƙara hannun sosai". cikin kwaɓe fuska tace. "To Ummi shi wannan sarkin zirga-zirgan ina zan ganshi?". Cikin yin ƙasa da murya Ummi tace. "Yana falonshi yanzu ya dawo, yana wucewa kina fitowa, jeki sameshi da sauri kada yayi bacci ya zama kin tadashi a bacci dan babu abinda yafi ɓata mishi rai sama da ya fara bacci a tadashi". Cikin juya ido tace. "Ummi to ni me zan ce mishi?". Murmushi Ummin ta kumayi kana tace. "Abinda kika cemin shi zaki ce mishi, tashi kije musan yadda zamu fuskanci aikin". Ta ƙarishe mgnar tana miƙar da hannunta, a hankali ta miƙe tsaye, doguwar rigar jikinta ta gyara tare da yane mayafinshi. Ganin ta tsaya ne yasa Ummi cewa" "kije mana." Allah yasani badon tana son ladan aikin ciyar da marasa ƙarfi da basu abin buɗa bakiba da bazata sake zuwa tambayar abu wurin wannan kurman ganganɗinba, tun randa taje tana mishi mgnar yacewa Umaymah ta bar musu Hibba ya shareta take jin haushinsa in ta ganshi kamar ta ɗirka mishi dundu a baya. Muryar Ummi data kuma jine yasata, juyawa, ta nufi corridor'n da zai sadata da falonshi. A hankali take taku, tana jin sanyin tayis ɗin wurin na ratsa mata ƙafa, sallama tayi a bakin kofar tare da kutsa kai ciki, tana mai murtuƙe fuska. Bisa 1 str ta sameshi zaune, da alamun waya yakeyi da Umaymah. Dan taji yana kiran sunanta. Gefenshi ta ɗan tsaya tare da kallonshi ta wutsiyar ido. Shi wai ko shi kaɗai ko a ɗakinshi shi ɗaya sai ya zauna da kima-kiman riguna, ganshi wata ƙil basa damunshi". Haka taketa maganar zuci, har ya gama wayar da yakeyi bata, saniba. shi kuwa baibi ta kantaba yaci gaba da ɗan aikin da yakeyi a wayar. Jin shirune yasa ta ɗan kalleshi, ganin ya gama wayar da yakeyi ne yasa, cikin dakiyar murya tace. "Uhummm dama so nake in ba matsala ko zamu rinƙa yin abin buɗa baki ana kaiwa masallacin, da kuma bawa bayi nasu daban". Bai kulata ba, asalima yamutsa fuskarshi yayi, ya lura wannan abar bata gama iya sanin makamar mgna ba, ji yadda take mgn a kaikace. Kamar ba ba fullatanaba, bayan anyi ittifaƙin bayan larabawa babu ƙabilar dake da luggar iya sarrafa harshe sama da Fulani. Shiru tayi tare da tura baki kana ta ɗan murguɗashi, tare da cewa. "Ayyah ka amince mana?". kanshi ya sunkuyar tare da ɗaga system ɗinshi ganin biyu dai-dai ta cika. Miƙewa tsaye yayi tare da motsa lips ɗinshi a hankali yace. "Eh". Da sauri ta juya ta fita tana hararan bayanshi. Shi kuwa bedroom ɗinshi ya wuce. Rage kayan jikinshi yayi kana yasa hannunshi ya jawo pillow'nshi ya wurgar can gefe gaban gadon inda babu carpet, a hankali ya kwanta a wurin, Gudun kada daɗi gado yasashi yayi baccin da zai makara sallan la'asar, Yana konciya ba jimawa yayi bacci. Ita kuwa cikin jin daɗin amincewar da yayi, tacewa Ummi. "Ummi ya yarda yace muyi". Miƙewa Ummi tayi tare da nufar kitchen a tare suka shiga. Tana cewa. "Yauwa to taho mu gayawa Saratu abinda za'ayi. A tsaye suka sameta a tsakiyar kitchen ɗin kusa da kitchen table, tana gyara ganyen. "Yauwa Saratu kin wonke shinkarfa masan ne?". Kai ta gyaɗa tare da cewa. "Eh na wonke,kuma mafa tun ɗazu da nazo kuna kuma bacci na jiƙa wani, sai dai hannuna ya zarce yayi yawa, yanzu ina gama tsinkar ganyen zan kai markaɗen ne in na dawo an kwaɓashin sai in fara firan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185