Chapter 59
Chapter 59
kafin nan to jin wannan na gaggawa kuma da jikan Sarki za'ayi yasa, mutane taruwa, gashi ranar jumma'ace, duk matasan rugogin suna, gida tunda suka dawo sallan jamma'a. Rugar Bani ta cika tayi maƙil da bani adam, tako wacce kusurwa tsastsafo akeyi kusufa-kusufa. Jin karan tamɓarin ganganr Shaɗi ne ya ƙara gaiyato mutane harda na cikin garin Shikan, tuni ƙabilun Bonon sun garzayo cikin Rugar Bani. Bukar kuwa mahaifin Ba'ana shida kanshi yaje, cikin Garkensu ya ɗauko tukunyar tsumin bulalim shaɗin da Ba'ana ke tsumasu da dafin kunamai da sauran sihirurruka, na dodon tsafinsu Bonon. Matasa majiya karfi ne keta ɗebo ruwa, cikin rijiyoyin garin. Suna jiƙa taron wurin dandamalin, da za'ayi gasar kaɗe-kaɗen duk sun taru sun cika kunnen kowa. Jabeer kuwa bugun da zuciyarshi keyi shiyafi komai tada mishi hankali. A can cikin gidajen Rugar kuwa, duk yan samari da yara sun firfito. A gidansu Shatu kuwa, Tunda taji Shelan da Nasuduka yakeyi cewa gasar Shaɗi tsakanin Ba'ana da jikan sarki. Kuka ta farayi, cikin tashin hankali da kiɗima ta kamo hannun Ummiy da tayi shiru sai ido take binsu dashi, murya na rawa tace. "Ummiy kijifa, zasuyi ya kashe, wani wanda baijiba bai ganiba, sunfa san illar dake cikin bulalinshi." Ganin Ummiy dai ba mgna zatayi ba, yasa ta kamo hannun Junainah cikin tsananin tashin hankali tace. "Junainah ki gudu, kije kicewa Bappa kada ayi gasar nan, Ni dai a bari na haƙura zan auri ya Ba'ana a yadda yake, zan zauna dashi, zanyi ƙoƙarin gyara mishi, rayuwa na gaji, kada a sake cutar da wani a kaina". Da sauri Rafi'a ta kalleta jin ta kamo hannunta cikin zubda hawaye tace, "Rafi'a wlh ya Ba'ana zai iya kashe mutun a kaina, da dafin kunamai yake tsuma bulalinshi, da wani tsafin, me ribata ayi ta cutar da mutane a dalilina, babu fa wani mahaluƙin da zai iya cin Ya Ba'ana gasar Shaɗi, babu wanda zai iya jurar azabar bulalinshi fa." Cikin sauri ta miƙe tare da miƙar da Junainah, sai kuma duk suka koma suka zauna, Jin muryar maƙocibsu Sarkin aska, yana cewa. "A a Shatu kada ki tura kowa, kada kuma kije kin tsumayi sakamakon gasar yau in sha Allah zata banbanta da na baya . Yanzu ma Arɗo Bani ne ya aikoni da in gargaɗeki." Yana faɗin haka ya juya da sauri ya fita, kana ya nufi wurin gasar. Da ido suka bishi. Ita kuwa Junainah da sauri ta miƙa ta nufi kitchin ɗin su, tana cewa. "Yauwa Adda Shatu, barin in kawo mana gasassun zabbin da Ya Ba'ana ya kawo mana muci. Ɗazu da nace muci Adda Rafi'a ce, tace mujiraki." Cikin sanyi Rafi'a tace. "Yauwa Junainah kawo mana, muci yau tunda gari ya waye bamuci komaiba." Gyara zansu sukayi, kana ta kalli Shatu cikin kula tace. "Dan Allah Shatu muci abinci, kinga Ummiy ma taƙi cin komai ganin, yadda kiketa kuka tunda kikaji ɓatansu ya Giɗi da rasuwar Ya Lado da Inna." Cikin zubda hawaye ta gyaɗa mata kai, sabida ita kanta tasan tana jin wani irin masifeffen yunwa, tamkar zai kasheta. Da sauri Junainah ta nufosu riƙe da akoshin gasassun zabbin da aka zuba dafin macijin a cikin. A can cikin tsakiyar garin Rugar Bani kuwa. Tuni su Ba'ana an gama shiryawa zalumci, domin dama ai a ƙa'ida shi zai fara duka, Yana tsaye sai zagaya filin yake yana zane iska, makaɗa da mabusa nata yi mishi kirari. A cikin wurin da Fadawa suka kange Lamiɗo da tawagarsa kuwa, anata kai ruwa rana da Sheykh Jabeer, Cikin kufula, yake cewa Sarki Jalaluddin da suke waya dashi. "Nifa babbar matsalarta wannan abun da za'ayi ba *Sunna* bace ba kuma *Farilla* bace, ba kuma *Mustahabbibace*, kai ko a babin *Makaruhi* ban taɓa cin karo da wannan banzar al'adar da kukeso in yarda ayita dani ba, Ina kuma da yaƙini in da zan bajeta a babin musulunci, kai tsaye za'a iya karhantashi, sabida ai cutar da kaine kuma, Musulunci bai yarda mutun ya cutar da kanshi ba, haka kurum kuce wai in tsaya a zaneni, inji shi kanshi kakan Lamiɗon Joɗo da yaji haza a gasar Shaɗin shine ya hana wannan al'adar a masarautarsa sannan yanzu ace za'a saketa a kaina bayan tsawon shekaru 145 ba'ayishi ba, tun zamanin jahiliyan ma an bar abu sai yanzu ku tara abu a kaina, to wallahi bafa zai yiwuba." Cikin kufula Sarki Jalaluddin yace. "To ya kakeso ayi ɗan masu ilimi kowa jahiline sai kaine mai ilimi sabida tsabar tsoro da ɗan karen son jiki kana gudun abinda zai taɓa lfyarka shine zakayi ta jawo mana wasu dogin falsafofi, a hir ɗin kafa Jabeer ko uwarka bazan sata abu taimin musuba". Gaba ɗaya sun hautsuna mishi zuciya, Ji yadda suketa zageshi, dan kawai yace bazaiyi abinda al'adace ba addiniba sai wani ce mishi suke ko uwarka ko ubanka, bayan sun san baya kuran hakan, rai a ɓace yace. "Uwata kace ai tunda ita ai ka haifa ba niba ko?, zancen gsky bafa za'ayi wannan abunba, sun daɗe basu ce mana lusaraiba, dolene, sai sun yarda mu fulanine, kai yau nifa ba bafulatani bane. A kirani da ko wacce ƙabilar ma in anga dama aikin kawai!". Yana faɗin haka ya katse kiran. Laminu kuwa da yake cikekken ɗan jarida, tuni yana naɗe komai a faifai jawaban su. Shi kuwa Sarki Jalaluddin, ido ya zubawa wayar jin jikan nashi ya katse kiran, murmushi yayi, irin nasu na manya, kana da sauri ya kira, Umaymah. A can Babba birnin Katsina, kuwa Gimbiya Khadijah Umaymah kenan , wacce take matar ɗan Sarkin Tsinako, Kekkyawar mata mai cikar haiba nitsuwa, tana kishinɗe, bisa wata tattausar doguwar kujera, yayinda Hadimanta biyu ke mata tausa. Jin wayarta na suwane, yasa ta buɗe idanunta dake lumshe, tunda sukayi waya d, ɗan ta Haroon ke gaya mata inda sukaje da ƴaƴan ƴar uwarta mafi soyuwa a rayuwarsu ne, taketa murmushi. Ganin sunan mahaifinta ne yasa tayi saurin amsa kiran. Bayan sun gaisane, Sarki Jalaluddin ya ɗanyi murmushi cikin nitsuwa yace. "Khadijah, kira ɗan ki, ki bashi umarnin bin umarnin mu, domin yana nuna mana ai bamu muka haifeshi ba, bazamu tirsasashi ba". Cikin tarin girmamawa tace. "Ranka ya daɗe, me kukeso in bashi umarni a kai nasan bazaiyi min musuba". Cikin jin daɗi yace. "Kice dashi ya amince da gasar da za'ayi". Cikin sauri tace. "To An gama yanzu kuwa, in sha Allah zaku sameshi mai biyayya a gareku". Daga nan sukayi sallama, Kana ta kirashi, sau biyu tana kiranshi baya ɗagawa, sabida kanshi ya ɗau zafi yana ganin za'a tirsasashi ya cutar da kanshi. Ga wani irin azabebben tsinkewa da zuciyarshi keyi, Ji yake tamkar zata faso ƙirjinsa ta fito, tayi ta tsalle a doron ƙasa. Gashi duk tsoffin Masarautarsun sun zagayeshi. Kowa da abinda ke ce mishi. Ga uban kiɗen-kiɗen dake hawa mishi kai. Ita kuwa Umaymah ganin bai amsa kiran bane, yasa ta kira Haroon yana ɗagawa tace. "Ina Jazlaan bashi wayar". Da sauri yace. "To Umaymah uwar Garkuwa gashi nan ido ya raina fata". Cikin barkwancinta da yaron nata tace. "Kaci gidanku Haroon Ni ɗana ba ragobane". Murmushi yayi tare da cewa. "To mu gani a ƙasa mana Umaymah". Yana faɗin haka ya miƙa Jabeer wayar wanda yake cewa Lamiɗo. "Bafa zan yiba, tsohon
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185