Chapter 2
Chapter 2
fara bin sawunta. Tana isa gaban tsuntsuwar tasa hannunta ta kamo hannun baiwar Allah nan da ita kadai Allah ya bawa damar ganin a mutun ba tsunstsuwar Boleru ba, hannunta data riƙo su kuma kab mutanen wurin gani suke fiffigen tsunstsuwar ta riƙo. Cikin kuka take shafa kan kurciya a ganinsu yayinda ita kuwa hawayen fuskar matar da take ganin take sharewa cikin muryar kuka tace. "Sannu sunji miki ciwoko, kice musu ke ba tsunstsuwa bace ki gaya musu ke mutunce kamarsu ki gaya musu kema bani adam ce karsu yankaki". Kuka ta kuma fashewa dashi ganin matar nan bata magana sai dai hannunta data riƙo ɗin ta ganshi tamkar robo wato alamun hannun a karye yake, cikin sauri ta sake hannun tare da cewa. "Appa mu tafi da ita mu kaita wurin masu gyaran ƙashi". To al'amarin parvina fa ya fara zarta zaton mai zato ya fara shallake tunanin mai tunani abin ya girmi shekarun Dattijannan. Shi kuwa Giɗaɗo kuka ya fashe dashi tare da nufarta yana mai cewa. "Ki bani tsunstsuwata ai tawace nine nayi ta renonta kullum tare muke cin abinci tare komai duk abinda naci sai na barmata dan tayi ƙatuwa, kuma yanzu kice baza a yanka min itaba". faɗawa tayi jikin matar wanda su a ganinsu ruggume tsuntsuwar tayi ita kuwa parvina cikin kuka ta juyo ta kalli Giɗaɗo tare da cewa. "Kai mayene ko? To Wlh bazan baku itaba in dai ina raye a duniya bazan bari a cutar da itaba, babu wanda zai kasheta a gabana sai dai in bana raye ku bar ce mata tsuntsuwa wallahi tallahi mutunce kamar kowa". Kiran sallan magriba da akayine yasa ɗaya daga cikin dottijon mai suna Yayari yace. "Arɗon Babayo lokacin salla yayi". Sai ya kuma kalli Giɗaɗo da Gainako da Seyoji da Ja'eh yace. "Maza kuje kuyi al'wala kuzo muyi salla, kai Giɗaɗo ka bar mata tsuntsuwar kurciyar kaji ko gobe da safe zabbi za'a yanka muku ku gasa kuci". Cikin kuka Giɗaɗo yace. "Wallahi Ni dai ta bani tsunstsuwata, bana son zabuwar ni ko ɗawisu zaku yanka min bana so kurciyata nake so a bani abuna". (Giɗaɗo sabo da kaza baya hana a yankata kenan) Cikin tsawa Arɗo Babayo yace. "Kai tafi daga nan ba kaine babba ba kaci girma ka bar mata tsuntsuwar kaji ko Giɗaɗona". Tura baki yayi yabi bayan yayun nashi yana cewa. "Ni a dena cemin Giɗaɗo ai dani Giɗaɗone da komai nakeso zaku bani". Basubi ta kanshi ba duk suka meda hankalinsu kan Parvina da tsuntsuwar dan ganin ƙasan tsuntsuwar Bolerun yana zubda jini, wannan abun ya sasu cikin nazari to, amman sai mgnar Parvina ta katse musu nazarin da cewa. "Allah sarki gashi sunji mata ciwo har sun fidda mata jini". Jin haka yasa suka sa a ransu yess jinin ne daya fita sanadin jin ciwo, cikin kula Arɗo Babayo ya matso parvina da taketa shafa kan tsuntsuwar da suke gani a idanunsu a hankali ya kamo hannunta cikin lallashi yace. "Parvina muje cikin gida ko, kinga dare yayi kiyi salla kici abinci, tsuntsuwar taki kuma ki saketa zata fire ta hau makwancinta". Da sauri ta fara jujjuya mishi kai hawaye na zuba tace. "Baffa Arɗo ta fire kuma? Bata da fiffigefa mutunce fa,tare zamu kwana da ita wallahi ba tsunstsuwar bace, mutunce ku daina ce mata tsuntsuwa, karmu barta ta kwana a woje". Sai ta kuma kama fiffigen tsunstsuwar tace. "Ga hannunta nan sun karya mata". Sai ta kuma kama ƙafafun tsuntsuwar tace. "Baffa Arɗo kaga ga sawunta ga idonta tanata zubda hawaye ga cikinta ga kunnenta ga bakinta ga gashin kanta har bayanta". Kallon-kallon suka tsaya sunayiwa junansu, domin kafiyar parvina kan cewa Wannan tsuntsuwar Boleru mutun ce bani Adam ce ya fara basu tsoro to ko dai ƴarinyar tayi gamone? Koko tsuntsuwar iskace?. cikin tsoron daya fara rufe Appa baki na rawa ya kamo hannun ɗiyar tashi da yake masifar so tamkar ƙoƙon ranshi cikin kaɗuwa da muryar fillanci kasan cewar sam fulanin ƙasar Cameroon basa jin hausa koda kawo min wuƙa in kashekane shiyasa cikin fillanci yace. "(Parvina tsonɗu on fa na ɗum innu adamajo, ko waɗi a vi'ata neɗɗo on) parvina tsuntsuwace fa ba mutun bace meyasa kicewa mutunce?". Kuka ta kuma fashewa dashi harda shessheƙan gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi ganin yadda jikin matar ke karkarwa. Ruggume tsuntsuwar kurciyar tayi a ganinsu yayinda ita kuwa cikekkiyar kamilar mace take gani hannunta matar ta kama ta juya ta nufi cikin gidansu dansu da Gainako suka shiga tana kukan shur-shur da hawayenta. Zurui sukayi suka rakata da ido har ta ɓacewa ganinsu. A mashigar gidan sukayi kiciɓis dasu Giɗaɗo da sauri ta koma gefe. Shi kuwa Giɗaɗo wani irin dundu ya kima mata a tsakiyar bayanta tare watsa mata harare cikin fillanci yace. "Hegiya muguwa wallahi sai na yanka tsuntsuwata muna fuka". da sauri tasa jikinta ta kare tsuntsuwar, tare dayin sauri tayi cikin gida. Seyoji ta samu tsaye gefen mamansu yana bata labarin tsuntsuwar da duk gidansu babu wanda bai san Giɗaɗo da itaba dan yanzu kimanin watanni takwas kenan kullum babu dare babu rana a nan gidan nasu tsuntsuwar take rayuwa kullum in Giɗaɗo yaci abinci ya rage inta kuma sai tazo tayi ta tsastsaga har sai tacinye duk abincin daya bari kana ya ajiye mata madarar shanu nanma tazo tasha, idan tasha ta ƙoshine sai ta juya da tafiya take barin cikin gidan ta koma bakin kogi. Da sauri Mamansu Giɗaɗo ta kalli Parvina tare da cewa. "Parvina na zo nan zo keda tsuntsuwar ki kada ki damu babu mai yankata". Da sauri ta iso gaban matar tare da cewa. "Inna ki hanasu yankata Allah kuwa ba tsunstsuwa bace mutunce". Cikin kula matar tace. "To parvina kada ki damu babu mai yankata daga yau ta zama taki, yanzu ajiyeta kije kiyi al'wala kizo kiyi sallah". Da sauri tace. "To". A jiye matar tayi bisa taburmar dake tsakiyar gidan, kana taje tayi al'wala tazo ta shimfiɗa sallaya a gefenta, itama Inna gefenta ta shimfiɗa suka sa baiwar Allah'n nan a tsakiya... Kamar da wasa da abin ya girmama domin koda sukayi salla isha'i fir parvina taƙi ta rabu da tsuntsuwar nan. Su kuwa su Arɗo Babayo sun mance batun tsuntsuwar ma, tunda sukayi sallan isha sukaci abinci. Suketa lissafin kan dabobbinsu kama daga kan Raƙuma, Dawakai, shanu, tumaki, raguna, awaki, ɗawisu, tolo-tolo, zabbi, tattabaru, saida suka waresu baki ɗaya dan sanin adadin zakkar da zasu fitar sannan suka gama fayace na zakkar kowanne daga ciki da shariya ta umarci a bada zakkanshi. Hira sukaci gaba dayi kan abinda ya shafi kiwon nasu. A can cikin gida kuwa, tunda Inna ta gama yiwa su Arɗo Babayo gashin zabbi ta haɗa da madarar shanu aka kai musu taketa fama da Parvina kan yadda ta tasa tsuntsuwar nan a gaba tana mata magiya kan tasa hannunta taci abinci, ganin bazata iya ci da hannun nata bane yasa iya tasa hannun tana bata abinci har baki tana amsa tanaci yayinda hawaye keta kwaranya a fuskarta babu ƙaƙƙautawa. Koda taci ya isheta sai ta mirgina alamun zata konta. Ganin hakan yasa parvina kallon inna cikin sanyinta da nitsuwarta tace. "Inna tare zamu kwana da ita". Kai inna ta jinjina mata kana ta miƙe tace muje cikin ɗakin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185