Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 92

Chapter 92

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kana ta zauna kusa da Shatu. A hankali ta jingina kanta da kafaɗan Shatu, Rafi'a kuwa miƙewa tayi ta shiga kitchin ɗin su. Abincin data dafa musu ta kawo musu. Ta ajiye gefe, sannan ta ɗauko tsintsiyar kwakwa ta share ta kwashi naman kab ta maidashi cikin babban akoshin, ta rufe, sannan taje ta wonke hannunta kana tazo ta zauna suka fara cin abincin. A can cikin fadar masarautar Joɗa kuwa. Jin jiri na ɗibanshi ga duhu dake rufe mishi ganine ya sashi, tafiya a hankali tare da dafa jikin gini. A haka har ya isa bakin Jakuzin, A hankali ya zare al'kyabbar jikinshi, ya wurgar dashi can gefe, kana ya tura ƙofar ya Jakuzin ya shiga, tsayuwa yayi tsakiyarshi, hannun na rawa ya buɗe shawan ruwan ɗumi. Wani irin numfarfashi wahala ya sauke lokacin da yaji ruwan ɗumi yana ratsa raɗi-raɗin azabobbun bulalin da yasha. Wasu irin hawaye masu masifar zafine yaji suna tsastsafo mishi cikin jijiyoyin kekyawan idanunshi, sai dai basu kai ga damar samun zobowa ba. Wani irin tsuma duk illahirin sashin jikinshi ya fara, zafin ruwan yakeji har cikin ƙoƙon ranshi, wani irin karkarwa haƙoranshi sukeyi har suna dukan juna, kat-kat. Kanshi ya sunkuyar tare da buɗe idanunshi a hankali, ruwan dake gangarowa daga jikinshi yana bin ƙasa in da zai gangara yake kallo, sabida zakace jinine ba ruwaba, Sabida yana wonke mishi jinin jikinshi. Haka ya tsaya a ƙasan ruwan ɗumin har saida yaga jinin ya daina zuba kamar da fari. Sannan yasa hannunshi ya ɗauki daddaɗan sabulun wankan shi, ya fara murza sabulun taki wani sashi na jikinsa, wani irin wahaltaccen ƙara yayi lokacin da sabulun ya ratsa inda ya farfashe a jikinsa, cikin rauni yace. "Wayyo Allah na! Wayyo Mamey na zan mutu, zafi zai kasheni tun kafin cikar burina." Ci gaba yayi da murza sabulun tare daci gaba da cewa. "Wayyo Umaymah wayyo Ummi". Sai kuma ya taune lips ɗinshi kana ya rumtse idanunshi yayi ta murza sabulun tako ina yanayi ruwan ɗumi na dukanshi. A haka yayi wonka ya wonke duk wani jini dake jikinshi yayi fes. Al'wala yayi, kana ya fito cikin Glass ɗin sannan ya ɗauki wanni tattausan baby towel fari ƙal ya ɗaura a ƙirjinshi ya sauƙo har zuwa guiwansa. Hannunshi yasa ya murza farin boxes dake jikinsa wanda ɗazu yake jiƙe da jini yanzu kuma yayi fari tas. Murza boxes ɗin yayi har ƙasa, kana ya ɗaurashi kan al'kyabbar jikinshi da ya cire, Cikin Woshing mashine yasasu, Kana ya fara yin taku a hankali ya iso gaban drower'n glass ɗin dake cikin bathroom ɗin. Wani tattausan gajeren wondo fari tas mai ratsin sky blue ya saka, gajeren wondon yazo mishi har guiwarsa, kuma mai ɗan faɗine, Wata tattaunawar riga mai guntun hannu wacce itama farace da ratsin Sky blue, ya saka, kana ya zaro wata ɓakar tattausar jallabiya doguwa har ƙasa tazo mishi daya zurata, Wani hulan taɓa kaji Hadisi ya kifa kan suman kanshi dake da ɗan damshin ruwan ɗumin. A hankali yake taku sabida zuwa yanzu wani fitinenne zazzafan zazzaɓi yakeji. Jiki na rawa ya fito, bisa sallayarshi dake shimfiɗe a wata ƴar kusurwa yaje ya hau. Yana hawa kan sallayar ya fuskanci gabas, yaji zuciyarshi tayi wasai, baya tuna komai, baya kuma jin ciwon komai a jiki da zuciyarshi sabida kushi'i da tawakkali da kyutata ibada baya jin komai sai hasken farin cikin ibada. Kabbara ya tada tare da niyar sallan la'asar daya mannata bisa laruri ya makarar dashi. A falonshi kuwa, hankalin Haroon ya tashi yana nan tsaye bakin ƙofa yana ta magiyar ya buɗe mishi, bai saniba shi yana can har cikin bathroom ɗin shi. Yana nan tsaye, mai Martaba Lamiɗo da Galadima suka iso tare da Sarkin Shaɗi. Cikin sanyi yacewa Lamiɗo. "Ya shiga ciki kuma ya rufe ƙodar ta ciki, inata kiranshi baya amsawa. Murmushi Lamiɗo yayi kana, yacewa Galadima. "Muje". Kusan a tare suka fito falon. Suka zauna, kana ya kira Abba, yace yazo yasa ɗanshi ya buɗe musu ƙofar. Jin hakane yasa Abba tahowa da sauri. A can babban falon kuma. Cikin damuwa Jamil ya labartawa Jakadiyarsu da Aunty Juwairiyya abinda ya faru. Ga mamakinsu sai sukaga Jakadiyarsu tayi wani ƙayataccen dariya cikin sakekkiyar murya tace. "Alhamdulillah wannan shine abinda muka daɗe muna jira tsowon shekaru da dama. Kuma jinyarsa abune mai sauƙin". Cikin ruɗani Jalal yace. "Ummi kuka daɗe kuna jira kuma?". Kai ta jinjina mishi, kana ta miƙe ta nufi kitchin dan harhaɗa aikin da akasata. A nan Abba yazo ya samesu. Jalal na ganinshi ya kauda kanshi. Hakama Jamil Imran kuma bayanshi yabi suka nufi side ɗin Jabeer ɗin. A falo ya samu iyayen nashi, Cikin girmamawa ya rusuna yayi Lamiɗo Barka da yammaci kana ya matso kusa da baƙin ƙofar Bedroom ɗin Jabeer cikin ɗaga sauti yace. "Muhammad! Muhammad Jabeer! Jabeer!! Jabeeey!!! Ka taso maza kazo ka buɗe min ƙofar nan ina jiran ka". Jabeer kuma da yanzu yake raka'ar ƙarshe, sam hankalinshi baya ga jin kiran Abbanshi domin a yanzu yana gaban Ubangijinmu ne. Haroon kuwa wayar dake kunnenshi ya gyara riƙewa cikin shaƙiyancinsa yace. "Uhumm Umaymah ke dai kicewa Sarki Jalaluddin da Sarki Abubakar baban Daddy na, suyiwa masarauta Joɗo gudumowar suturu. Domin yau dai ran ƴan maza ya ɓaci, nasan sai ya yayyage kab wani abu mai yaguwa a masarautarsu". Cikin wani irin farin cikin wannan labarin da Umaymah taji tayi kekkyawan dariya tare da cewa. "Haroon yayan naka kakeyiwa tsiyako?". Cikin tura baki yace. "Allah ko Umaymah kecema kike sawa Jabeer yana rainani wai yayana". Da sauri tace. "To ba yayanka ɗin bane?". Cikin yamutsa fuska yace. "Yayan kwana arba'in, shiyasa yake min kallon kobo biyu da sisi, sabida yana jin kuna ce mishi yayana, wani lokacin har cemin yaro yakeyi dan tsabar son girma da manyance, Ni mamaki da yake bani kawai sai in zuba mishi ido in naga yana min faɗa kamar wani ɗan cikinsa". Murmushi Umaymah tayi kana, tace. "Gobe zuwa jibi in sha Allah ina nan zuwa Masarauta Joɗo, sabida zanzo in lallashi ɗana nasan yayi zazzafan fushi tunda yaƙi kula Dr Aliyu ma". Daga nan sukayi sallama. Shi kuwa Sheykh Jabeer saida ya isar da sallameshi yayi addu'o'in shi Kafin ya tashi a hankali ya nufi bakin ƙofar sabida zuwa yanzu zanan bulalin sunyi tsami ga zazzaɓi daya mishi rubdugu. A hankali ya murɗa key ɗin ƙofar ya buɗe ta, kana ya juya ya koma kan gadonshi, sabida rawa da jikinshi keyi na zazzafan zazzaɓi da wahala. Yana konciya ya lumshe idonshi tare da fara karanta Suratul Khaf kasancewar yau yammacin jumma'a ne. Su kuwa a falo suna jin sautin buɗe ƙofar, suka zubawa ƙofar ido ganin shiru bai fitobane yasa. Galadima da Haroon suka nufi cikin ɗakin. Jim kaɗan da shigarsu Galadima ya fito da sauri ya kira sarkin Shaɗi, da Lamiɗo kana da Abba. A tare suka nufi cikin ɗakin, suna shiga Haroon ya fito. Babban Falon ya koma ya nufa yana kiran Jakadiyarsu da sunan da suke kiranta. "Ummi! Ummi!!". Da sauri ta fito kitchen ɗin riƙe da filas da kofuna, sai kuma wani ɗan kwarya mai kyau ruwan ciki na tururi. Da sauri ta miƙa mishi tare da cewa. "Yauwa Haroona gashi kai musu da sauri". To yace kana ya amsa

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});