Chapter 160
Chapter 160
da ibada, yanzu Jamil ya dena zuwa hirama wata ƙil kuma ya ɓata da Khadijah naji yanzu wata Maryam yake kira, Jalal ne dai yake ɗan fita shima ba sosai ba". Gyara tsayuwarshi yayi tare da cewa. "To Alhamdulillah, eh shi Jalal ba matsala fitanshi, nasan dashi. Ya Hibba kuma tana azumi ko batayi?". Cikin murmushin da kallon inda Hibba take tace. "A a Hibba ai an girma yanzu ta rage rakinma". Ɗan karamin mataji ya ɗauka yana kontar da sajenshi yace. "To Ummi na gaisheku, na kira Aunty Juwairiyya kam nani jikin ya Jafar da sauƙi sosai mun gaisa da Hajia Mama, har take cemin Affan ɗina zai dawo a salla". Da sauri tace. "Uhum Sheykh". Ajiye kum ɗin yayi tare da cewa. "Na'am Ummi". Cikin sanyi tace. "Ga Shatu". Shiru yayi baiyi magana ba, kuma bai katse kiranba, jin haka yasa ta kuma cewa. "Sheykh". "Na'am Ummi". Ya kuma cewa. A hankali tace. "Ga Shatu". Still baiyi mgn ba, hakanne yasa a hankali ta mannawa Shatu wayar a kunne ta. Kana ta sa hannunta ta kamo hannun Hibba suka fita babban falon. Shi kuwa Sheykh Jabeer shiru yayi tsaye gaban dreesing mirror, yana kallon gemunshi. A hankali yake jiyo sautin sauƙar numfashin can ƙasa-ƙasa, ɗis ɗas haka yaji ƙasan zuciyarshi na harbawa. Ita kuwa shiru tayi tanajin sautin tasbihi da yakeyi can ƙasan-ƙasan maƙoshinsa, Lips ɗin shi na motsawa a hankali suna fidda sautin can ƙasa. Jin shirun yayi yawane yasa a hankali ta buɗe bakinta tare da cewa. "Assalamu alaikum". Sai kuma tayi shiru ta kasa kunnen dan jiran amsarshi. Gyara zamanta tayi tare da ƙara riƙe wayar, numfashi ta sauƙe a hankali. Hakan yasa yaji sautin iskar. Har ta cire tsammanin zai amsa sai kuma taji muryarshi can ƙasa yana cewa. "Wa alaikissalam. Ashe kin iya sallama?". Ya jefo mata tambayar a gajarce. Cikin juya ido tace. "Ba'a koya min da wuri bane!." Shine mgnar da tayi niyar gaya mishi, sai kuma tayi mgnar a zuci, ta danne abun. Sabida tana son ta nemi al'farman addu'o'in a kaba, aka yayunta da suka bace, shiyasa cikin sanyi tace. "Eh, Ummi ta koya min". Shiru yayi kamar bai jitaba, ita kuwa a hankali tace. "Ina kwana". Kanshi ya ɗan kalla a madubi tare da cewa. "To Kifin rijiya su nan yanzu wunine". Cikin sanyi da sassauta Muryar son isar da buƙatar ta tace. "To ina wuni". "Alhamdulillah". Ya bata amsa. Miƙewa tsaye tayi ta nufi bedroom ɗinta. Tare da cewa. "Ya ibada?". "Alhamdulillah". ya kuma cewa. "Har ya kai hannunshi zai janye wayar sai kuma ya tsaya jin tana cewa. "Uhmm, Ayyah Yah Sheykh..". Sai kuma tayi shiru. Cikin saurin jin an kira salla murya a nitse yace. "Uhumm Ayyah, me ɗin?". Da sauri tace. "Dama.. dama!!...". Gajeren tsaki yaja tare da cewa. "Sauri nakeyi zan tafi masallaci, kada kisa na rasa damata". Cikin rauni da muryar dake nuna cewa tana zubda ƙwalla tace. "Ayyah dan Allah da Manzonsa. In kaje kayi min addu'a a harami mana". Juyowa yayi yana kallon Haroon da Ya Hashim da suka shigo yanzu alamun kiranshi zasuyi. Cikin wata iriyar murya a hankali yace. "Addu'ar me zan miki?". Murya na rawa tace. "Allah ya dawo min dasu Yayana lfy, ya kare minsu a duk inda suke, ya baiyana sucikin gaggawa". Cikin rashin fahimtar zancen nata yace. "To zan miki saboda Allah da Manzonsa da kikace". Cikin jin daɗi tace. "Ngd matuƙa Allah ya biya maka buƙatunka." Wani irin sassanyan numfashi ya sauƙe tare da lumshe ido a hankali yace. "Amin ya rabbil izzati, kema kuma kiyita addu'a ki dage da ambaton Allah zai cika mana dukkan burinmu". Yana faɗin haka ya katse kiran. Ita kuma murmushi tayi tare da share hawayenta. Cikin sanyi tace. "Ya Allah ka dubemu da idon rahama". Hibba dake shigowane tace. "Amin Amin." Daga nan suka fito falo suka kama sabgoginsu. A kwana a tashi asarar mai rai. Yau da gobe kayan Allah. Kamar yau aka kama azumi gashi yau an kai azumi na ashirin da tara. Wanda ake tsammanin tsalla gobe ko jibi. Irinsu Hibba duk sunfi fatan wata ta dawo yau. Gaba ɗaya wunin yau aiki Ummi da Shatu da Saratu suka wuni yi, wanda aikin salla ne. Zabbin da Jalal ya kawo bisa umarnin Hammansun. Da kuma kajin da Lamiɗo yasa aka rabawa al'ummar masarautar Joɗa. Ko wani Side in dai akwai mace kaji goma ake kaiwa. Da tarin kayan miya komi da komi, wanda shi cikin lambun masarautar ake cirewa. Kajin kuma daga gidan Gidan gonar MJ aka kawo, kana zabbin da aka kawo manyan sashin Masarautar Joɗa ma daga gidan gonar MJ aka kwasosu. Haka ƙoyayen kaji. Duk an rarraba ko ina. kuma duk saida aka yanka su aka gyarasu aka rarrabusu, dan haka aiki kawai aka fara babu kama hannun yaro. Hadimai da bayi sunata aiki. Duk sauran ɗinku nan suma sun dawo. Kasan cewar kusan a kitchen ɗin suka wuni ne, yasa Shatu ta ɗauki zabbi uku tun da azahar tayi musu gyara na musamman. Hibba kuwa tana Side ɗin Aunty Juwairiyya anayi mata zanen lalle. Akan sai dare za'ayiwa Shatu shiyasa taketa kimtsa aiyu kanta da wuri. Dama sunje da sassafe an wonke musu kai an gyara musu. Ummi kuwa tayi lallenta na gargajiya tana kwance a falo. Hakane yasa Shatu ta kira Gimbiya Aminatu. Cikin wasa tace. "Gimbiya a ƙaro min mai taya aiki yau Ummi na tasa lalle, Hibba ma tana can ana zana mata, nida Sara ce kaɗai a kitchen." Dariya Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa. "To Sayyadar Sheykh bari Larai tazo". Cikin jin daɗi tace. "To Gimbiyar Lamiɗo". Dariya sukayi duka kana sukayi sallama. Juyowa tayi ta kalli Ummi tare da cewa. "Tace zata turo Larai, Ummi ta iya aiki ko?". Kai ta gyaɗa mata tare da cewa. "Sosai ma kuwa". Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa kana ta miƙa wa Ummi wayarta tare da cewa. "Ummi sai mun nitsu ki bani number Gimbiya Aminatu". To tace kana ta koma kitchen ɗin. Wanke zabbin tayi fes tare da ɗan matsa lemun tsami kaɗan a ciki. Kana ƙara lallaɓeshi. A tukunyar ƙirar ƙasar Cameroon ta zubasu. Kana tasa al'basa, Curry, Maggi, kanamfari, citta, tafarnuwa kaɗan, da gishiri ɗan ƙanƙani. Ta rufe tukunyar da zabbin uku suka cikashi. Bisa gas ta ɗaurashi kana tasa wutan dai-dai. Saratu kuwa sa sauran tayi a babbar tukunta tasa kayan ƙamshi da ɗanɗano. Sannan ta ɗaura. Dai-dai lokacin Larai ta shigo. Bayan sun gaisa ne, ta ɗauki markaɗen waken ƙosan da zasuyi na kaiwa masallaci. Da markaɗen tattasan da taruhu da al'basan. Ita kuwa Shatu yau kunun basise ta dama mai kyau, ta cika kulolin. Kana Ta daura ruwan tea Yana tafasa ta ɗura a flaks. Duk wannan zabbin sunata sulaluwa suna bararraka sai wani irin masifeffen ƙamshi da yake tashi. Har yawunsu na tsinkewa. Fruits ta ɗebo a Fridge ta gyarasu ta shiryasu a tray biyu shiri mai kyau. Kana ta medasu cikin ƙaramin Fridge ɗin data kashe dan sanyi su ya daidaita. Larai na dawowa, suka fara suya. Ita kuma ƙullun waken kaɗan ta ɗiba. Kana tasa dafaffan ƙan data ɓare. Da al'basan da kifin data tafasa ta murmusa a cikin ƙullun ta sa mai da Maggi curry da dai sauran
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185