Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta shigo hadimanta na biye da ita a baya. Gefen Juwairiyya ta zauna ta zubawa su Sheykh ido, lokacin ɗaya hawaye ya fara kwaranyowa da idanunta, cikin rawan murya tace. "Sheykh lokacin na tafiya, Maimartaba ya aika a kirawo ka a zatonsa kana sashina, tashi kaje, Allah ya kiyaye hanya karka damu yayanku na ƙarƙashin kulawata musamman". A hankali ya miƙe ga mamakinsu sai gashi shima Jafar ya mike hannunshi yasa ya kamo ƙanin nashi, cikin rauni Sheykh yace, "Hajia Mama kodai in tafi dashine, kingafa baya son in tafi in barshine". Hannu tasa ta share hawayenta kana a hankali tace. "Bazai yiwu ka tafi da shiba, karka damu Jabeer komai zai wuce". Kai ya gyaɗa mata, sannan ya juya, ya nufi hanyar fita yana riƙe da hannun yayan nashi, Jalal na biye dasu a baya, Hajia Mama da Juwairiyya da yaranta na biye dasu. Koda suka zo tsakiyar farfajiyar gidan cikin bada umarni Hajia Mama ta kalli Sheykh tare da cewa. "Jabeer kuje sashin Hajia Fatima ka sallamarta". Ɗan jim yayi, a hankali ya kalleta, ita kuwa da sauri tace. "Umarnine ba shawaraba". Kanshi ya gyaɗa alamun to. Daga nan suka shiga sashin nata, bayan Jakadiya tayi musu iso. A folon forko suka Sameta, tana hakimce hadimanta na zagaye da ita. Tana ganinsu ta tashi ta zauna, cikin sanyi tace. "A a Sheykh da kanka". Ɗan rusunawa yayi tare da cewa. "Zanyi tafiya Hajia mamace tace inzo in sallameki". Da sauri tace. "Ayyah, to Allah ya kiyaye hanya ya kaika lfy ya dawo da kai lfy". Amin yace a takaice kana ya kama hannun Ya Jafar ɗinshi suka fito. Nan suka raka'a zuwa sashin Gimbiya Aminatu nan suka sameta a falon, sukayi sallama da ita. Daga nan ya wuce fada, Hajia Mama kuwa ta koma sashinta da hadimanta bayan ta mishi addu'o'in insa lfy. Juwairiyya kuwa parking lot ɗin su inda ta hango an jera motoci. Ta nufa inda Jamil ke tsaye da alamun waya yakeyi da Malika sahibarsa sabuwar budurwar da yayi. Shi kuwa Sheykh yana shiga fada ya samu Waziri ne kaɗai da Maimartaba da alamun zaman jiransa sukeyi. A gaban Maimartaba ya rusuna, tare dasa hannu ya tura hularshi ya maidashi baya, Cikin kulawa Sarki Nuruddeen yasa hannu kan tsakiyar kanshi ya dafa tare da cewa. "Allah ya kaika lfy, ya dawo da kai lfy, ya baka sa'an tafiya, ya kareka a duk inda kake". Amin Amin suka amsa baki dayansu, kana Waziri ma ya mishi addu'o'in sannan suka miƙe gaba ɗayansu sukayi woje dan mishi rakiya, Sarki Nuruddeen da bayinshi wazirinsa da bayinshi, shina Sheykh da bayinshi, sai ya zama rakiyar ta samu taron mutane, kana ga bayin Ya Jafar, nan suka shishshiga tsala-tsalan motoci a ƙalla motoci goma sha biyar ne sukayi mishi rakiya zuwa Airport. A wurin rabuwarsa da Ya Jafar ne yasa zuciyar kowa raunata domin Jafar kuka sosai yayi tayi da kyar dai suka dawo gida bayan jirgin su Sheykh ya tashi zuwa birnin Jalaluddin. Cikin abinda bai gaza awa ɗaya ba sai gasu a birnin Jalaluddin. Kafin jirginsu ya sauƙama a ƙalla motoci goma ne suka zo tarbansa, a ciki kuwa harda mai Alfarma Sarkin Musulmai Jalaluddin. Koda yaga jikan nasa mota ɗaya suka shiga, suna isa fadar musulunci, suka fito daga cikin motocin da sauri Sarki Jalaluddin ya zagayo ya kamo hannun jikan nashi, suka nufi sashin Amaryarshi Gimbiya Kulsum, jikanshi Kabir na biye dasu a baya, suna isa falonta gaba ɗaya ma'aikatanta suka fita ganin mai alfarma da kanshi, shi kuwa Jalaluddin cikin ɗan ɗaga murya yake cewa. "UmmuKulsum! UmmuKulsum!! Ga Jazlaan ya iso, gashi na kawo mikishi har ɗauki". Wata kekyawar tsohuwar balarabiyace ta fito da sauri, cikin tsananin soyayyanshi ta ruggumeshi, shima ruggumeta yayi cikin harshen larabci Sheykh yace . "Ana uhubbiki hubban axeeman ya Sitti". Kanshi ta shafa cikin tsananin son jikan nata tace. "Laisa li misluka abadan ya habibee". Murmushi mai faɗi yayi tare da bin bayanta, kai tsaye dinning area ta nufa dashi Kabir da Sarki Jalaluddin na biye dasu, da kallon sha'awa. Kujera taja ta ajiyeshi, kana ta jawa Jalaluddin tasa kujerar nan kabirma ya zauna, Suna zama sai ga wasu dattijan mata su uku sun shigo a jere a jere, suna zuwa duk kanshi suke shafawa shi kuwa sai murmushi yayi tare da kallon Mai alfarma Sarki Jalaluddin yace. "Malam kace su dena shafa min kai haka na gaji". Murmushi sukayi baki ɗayansu kana suka zauna, cikin kulawa babbar cikinsu tace. "Kazo lfy, ya jikin Jafar?". A hankali ya ɗan kalleta tare da cewa. "To Alhamdulillah jiki da sauƙi zance". Allah ya ƙara sauƙi cewar Jalaluddin Amin Amin suka amsa baki ɗayan su, ƙaramar cikinsun ce ta ɗan kalleshi cikin tsokana tace. "Ina mai gidanmu Sarki muminai". Taɓe baki Sheykh yayi tare da cewa . "Uhumm Jalal ne Sarkin Musulmai ko? Baki sanshi bane". Dariya sukayi duka kana suk gaggaisa sannan suka fita gaba ɗayansu, ita kuwa Sitti abinci tayi ta bashi har saida ya kwaɓe fuska tare da cewa. "Na tuba ki barni haka na ƙoshi". Kai ta gyaɗa kana suka dawo falo zata fara hira, yace shi dai ya gaji bacci yakeji hakanne yasa, Jalaluddin da kanshi ya kaishi makwancinsa. Asuba ta gari al'ummar Sokotawa A nan Ɓadamaya kuma cikin Rugar Bani Washe gari da hantsi, bayan duk sun karya, kowa makiyaya duk sun tafiya kiwo, manoma kuma duk sun tafi noma, kana mata masu shiga tallan nono cikin gari sun tafi, garin yayi tsit kamar yadda aka saba Ba'ana kuwa da Shatu suna zaune a ginɗin bishiyar mangoro dake bakin zauren su, ita tanata. Ciki shi kuma yanata woje, cikin sakin fuska ya kalli Junainah dake gefensu yace. "Junainah je cikin gida kice a baki ɗanyen kwai ki kawo mana in dafa mana". Da mmki Shatu tace. "Ka dafa mana kuma?". Kai ya gyaɗa mata, ita kuwa Junainah uwar kwaɗayi tuni ta tafi cikin gida Inna na tambayarta me zatayima Bata kulataba, sai ɗan kwano data ɗauko a konɗonsu kwan zabbi ta ɗebo a kalla sun kai goma, kana da gudu ta dawo wurinsu. Da sauri yasa hannunshin ya amshi robar, ita dai Shatu Ido ta zuba mishi taga ta ina zai dafa kwan, shi kuwa Ba'ana hannunshi yasa ya fara tona ɗan ma dai-dai cin rami, da mmki Shatu tace. "Ya Ba'ana me zakayi da tona rami kuma?". Cikin murmushi yace. "A ciki zan dafa mana kwan". Junainah kam gabanshi tazo ta zauna, tana kallonshi har ya gama tona ramin. Kana ya zuba kwayayen a ciki ya maida ƙasar ya binnesu. Sannan ya juyo ya kalli Shatu yace. "To musha hirarmu kafin kwan ya nuna". Junainah ce tace. "Ya Ba'ana ta yaya zai nuna kuma babu wuta?". Kamo hannunta yayi tare da cewa. "Ke dai zauna ki jira ki gani ƙaƙara". Kai ta gyaɗa tare da gyara zama, shi kuwa Ba'ana murmushi yake a baiyane a ranshi kuma cewa yakeyi. "Uhummm shi Bappa dan ina son yarsa bazai hanani yashe Garkensa ba, kuma da koyayen gidanshi kawai zan iya karya kafin da yayiwa garkenshi". A zahiri kuwa kallon Shatu a yayi tare da cewa. "Zakiji girkina mai daɗi". Kai ta jinjina tare da cewa. "Uhumm girki ko al'mara." Kanshi kawai ya gyaɗa alamun zaki gani daga nan

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});