Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 123

Chapter 123

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sakeba". Nan duk suka nufo cikin falon. Suna isowa Hajia Mama na shigowa Batool na biye da ita a gefe. Jafar kuwa da sauri ya koma bayan Sheykh tare da riƙe hannunshi ya fara ja alamun su tafi. Shi kuwa Sheykh ƙara tsuke fuskarsa yayi ganin Batool cikin sauri ya gaida Mama, ta amsa fuska a sake tare da sanya masa al'barka. Kana ya nufi hanyar fita, da sauri Jafar yabi bayanshi. Umaymah kuwa da Ummi da Juwairiyya da Batool nan suka zauna suna ɗan hirarsu. Jalal kuwa da Jamil a tare suka fita, shi kuwa Haroon falon Jabeer ya koma. Yana shiga ya kira Jannart bayan sun gaisa take tambayarshi yaushe zai je masarautarsu nan yake ce mata. Yana nan tafe a satin nan. Shi kuwa Sheykh Jabeer yana fita kai tsaye Valli Hospital ya nufa. Asibitinshi mai zaman kanshi. Asibitin da duk nahiyar Ɓadamaya babu kamarshi. Asibitin da in kana cikinsa zakayi zaton a ƙasashen turawa kake. Haka lamarin yaci gaba da tafiya. Babu mai yiwa Sheykh Jabeer batun Aysha. Itama Aysha gani take kamar ziyara tazo ba aureba. Tunda ita dai da idonta bata taɓa ganin mijinba, sai dai taji sunanshi. Sosai ta shaƙu da Hibba da Umaymah, hakama Gimbiya Aminatu da Ummi. Lokuta da dama takan shiga Bathroom tai ta kuka sabida begen ƴan uwanta. Yau kwananta uku cur a gidan. Idonta ma baiga ranaba. Umaymah kuwa a sashin Jabeer yana fita. Wata tirela ta iso har bakin Side ɗin shi. Nan aka fara sauƙo da kayayyakin ɗaki na amare. Ana shigarwa ciki. Kana masu aiki na ɗaure komai suna kimtsashi. Sai kusan la'asar suka gama komai kafin. Suka tafi kana su Umaymah suka taho. Suna shiga asalin babban falon, Aunty Juwairiyya da Hibba suka haɗa baki wurin cewa. "Wow masha Allah, Kai Umaymah ƙara so da sauri kiga falon nan yadda ya zama fadar masarauta". Da sauri Umaymah da Ummi suka ƙara so. Masha Allah! Masha Allah!! Masha Allah!!! Shine abinda kawai Umaymah keta mai-mai tawa, sabida kyau da tsaruwan falon yayi masifar kyau. Kasan cewar falon irin ƙaton nanne mai faɗi da tsawo. Wasu irin kujeru ne Daimond set masu masifar kyau da tsada, a shirya a cikin tamfatsen falon.masu Golding color mai ɗan karen sheƙi sai surkin Brown color mai sheƙin gaske da ratsin ruwan madara.. Kana haka ma kalan labuyen falon masu tsawo da faɗi da taushin gaske.sai wani table na glass mai Golding color da aka ajiye a tsakiyar falon bisa wani tattausan carpet mai azabar kyau. Sai wani babban Tv dake liƙe a jikin bongon, kana gefen dama kuwa wani babban majigine manne wanda yake baiyana rubutun Kur'ani reras daki daki. Can gefen kuwa steps ɗin hawa Dinning area ne, wanda aka canza Dinning table and chairs ɗin, Aka zuba wasu masu masifar kyau da tsadan gaske. Ba'a wani cika falon da tarkace ba, amman yayi matuƙar kyau. Tafiya kaɗan zakayi ta gefen hakun zaka ratsa cikin wani madaidaicin falo. Yayinda na Jabeer yake hannun dama. falon ɗakin da Umaymah ke tsauƙa in tazo kenan. 2 bedroom ne wannan falon yake dashi ko wanne da bathroom a ciki. Kana sai Dinning area matsakaici daga nan gefen Dinning area kuma akwai ɗan ƙaramin corridor wanda zai sadaka da kitchen da store. wasu irin datsa-datsan kujeru masu masifar kyau da ɗaukar hankali aka kimtsa a falon wanda komai na ciki. Peach and white coffee ne mai ɗan karen kyau. Hakama Dinning table and chairs ɗin. Still labulayen ma hakane. Sai kuma cikin bedroom ɗin wanda duk girmansu ɗaya, haka yasa aka shirya wasu tagwayen gadaje masu masifar kyau suma Golding color ne mai sheƙi da ɗaukar ido. Saɓanin side ɗin Jabeer komai Sky blue and white ne, wanda hakan yasa kana shiga sashinsa sai kayi zaton a sararin samaniya kake rayuwa. Komai yayi kyau. Especially kitchen ɗin dake matsakaicin falon. Domin wancan kitchen ɗin dake babban falon ba'a taɓa shi ba, hakama Side ɗin Sheykh. Sai kuma sama wanda shi a rufe yakema, sam babu kowa a ciki. Sosai fa su Umaymah suka yaba da kyan shirin da akayiwa wurin. Nan suka zauna a falon. Umaymah ce ta kalli Jakadiya cikin sauƙe numfashin tace. "Alhamdulillah, gobe kuma zakiyi musu jagora shida matarshi su zaga ta gaida ahlin masarautar Joɗa, ta gansu su ganta su san juna, gudun kada a haɗu a wani wurin ba'a san junaba". Wani gwauron numfashin Ummi ta sauke tare da cewa. "A nan gizo ke tsakar ko ta ya zamu samu, Sheykh yayi wannan al'adar yadda ya dace ake kuma yinta, kinsanshi mutunne mai kunya, koda yana son abunma bare ba wani son abun yakeyi ba". Cikin yarda da kai Umaymah tace. "Kada ki damu yana ɗaya daga cikin dalilin da yasani, na zauna sai naga kamun ludeyin zaman nasu." Haka dai suketa tattaunawa, Suna nan zaune Gimbiya Saudatu ta shigo tare da hadimanta, kana da Laminu da Baba Basiru da Baba Nasiru. Cikin isa da ƙasaita ta nufi kujerar da duk canjin da akayiwa falon ba'a canzashi ba sabida kujerace ta masarautar Jalaluddin, cikin isa take taku yayinda ta bawa ƙofar shiga baya. Cikin gatsali ta kalli Umaymah data tsareta da ido. Kallon uku saura tayi mata kana tace. "Duk mutun muna fuki abin tsorone. Amman munafurcin balaraben Mutun yafi na kowa muni da bada tsoro. In banda salon munafurci ayi aure yau kwana uku a gaza fito da amarya a nunata ga mutanen masarauta, bare a fanshi idonta." Ta ƙarishe mgnar tana kai mazaunanta bisa, Kujerar. Sai kuma tayi maza ta miƙa, jin muryar Jabeer da yanzu ya shigo, ko mgnar ta, ta ƙarshe baijiba. Cikin isa da ƙasaita da rashin tsoronta, da kuma tsare fuska alamun Ni bani da lokacin ki, kuma ni ba sa'an yinki bane ya nuna mata hanyar fita da yatsarshi tare da yamutsa fuska cike da ƙarfin zuciya ya kalleta ita da ƙannen Mahaifin nashi yace. "Fice min daga gida, bacci na dawo zanyi so banda lokacin jin ihunku na kar...! By *GARKUWAR FULANI* "Muhammad!". Ya kira babban sunanshi tare da jawo hannunshi, ya zaunar dashi bisa kujerar da ya tashi a kai. Cikin wani irin yanayi mai cike da tashin hankali da tsoron abinda suke shirin aikatawa, ya kalli Mahaifin nashi, kana ya juyo ya kalli Lamiɗo da Galadima gefen damanshi ya juyo ya kalli Jadda cikin rauni ya kuma kalli mahaifin nashi tare dayin ƙasa da murya yace. "Abba kada ka bari su ɗaura auren nan, dan Allah kace musu su bari, kada su ɗaura". Ya ƙarishe mgnar cikin tashin hankali da ɓacin rai da tarin rauni a fuskarshi. Cikin zuba mishi ido Abbanshi yace. "Meyasa? Sabida me za'a bari!? Meyasa baka so!?." Kanshi ya jujjuya tare da haɗe hannayenshi wuri ɗaya ya fuskanci mahaifin nashi cikin sanyi yace. "Ni dai bana so. Abba dan Allah kada ka bari suyi. Bana son garin nan bare mutanen cikinsa, kuma bawai haka banza naƙi auren nan ba, Abba inada matsala, Please Abba na tuba dan Allah kace su bari. In yaso a ɗaura da wani amman banda ni kam". Lamiɗo ne ya kamo hannunshi cikin isa yace. "Auren' nanfa, kamar ma an ɗaurashi an gama, domin babu wani abu ko wani mahaluƙin da ya isa ya hana wannan ɗaurin auren, gwarama

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});