Chapter 1
Chapter 1
GARKUWA📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘 11:56 Am TUESDAY OCTOBER 20. *GARKUWA* PAGE 1 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘 *Littafi na ɗaya. Shafi na forko!* Free page *Gargaɗi! Gargaɗi!! Gargaɗi!!! Ban yardaba! ban Amince ba! ban lamunceba! A juya min labarin LITTAFINA tako wacce sigar bana so ban bada damaba in kana buƙata akwai number ta a jiki kika nemi izinina a kiyaye domin zama lafiya yafi zama ɗan sarki! In kunne yaji gaggan jiki ya tsira. Kuma hanyar lafiya a bita da shera yafi, wannan littafin haƙin mallakarsa nawane Aysha Aliyu Garkuwa!.* Bismillahirahamanirahim Ina mai farawa da sunan Allah mai rahama mai jinƙai mai komi mai komai. Ina gode Allah daya bani aron rai da lafiya da nitsuwa da konciyar hankali ya bani damar fara wannan littafinawa mai suna GARKUWA. Ya Allah ina roƙonka ka tsare min tunanina da hannuna ka tsare min al'ƙalamina daga rubuta shari da duk wani abu da zai zamo guba ko masifa a rayuwar al'ummar Annabi, ya Allah ka bani ikon rubuta al'khairi da abinda zai zamewa al'ummar Annabi dan al'farma Annabi da Alqur'ani mai tsarki, ya Allah ka bani rai da lafiya dani da masu karatu ka nuna mana ƙarshen littafin nan lafiya kamar yadda ka nuna mana forkonsa lafiya, Amin ya rabbil izzati... *LITTAFINA NA KUƊI NE, BIYA ƊARINKI UKU KACAL DOMIN SAMUN DAMAR KARANTASHI BA TARE DA HAƘƘIN KOWA A KANKIBA, AKWAI SP GROUP SHI KUWA 1K PASTING NASU YAFI NA ƳAN 300 YAWA, TURO ƊARI UKU TA ASUSUNA 0005388578 JAIZ BANK AISHA ALIYU GARKUWA, SAI KI TURO SHAIDAR BIYANKI DA WANNAN NUMBER TAWA 09097853276, ƳAN SPECIAL GROUP BANA SON KATI, GA POS BURJIK A GARI, KUMA YAN 300 IN DAI KINADA DAMA DAN ALLAH YIMIN TRANSFER TA AC YAFI, AMMAN IN YA ZAMA DOLE BA MATSALA TURO KATIN MTN NA ƊARI UKUN, KANA BA HOTON KATIN ZAKIYI KI TURO MINBA, A A NUMBERS ƊIN ZAKI RUBUCE KU TURO MIN* Dan girman Allah da Manzonsa. masu tambayata tsoffin littatafaina ku daina bana so. Ku nema a cikin groups zaku samu, in dai ba Hukuncin Allah ko NAKASA BA KASAWA BACE, da GARKUWA kada ku tambayeni in kuna ƙaunar Allah, in kuwa bakya ƙaunar Allah to tambayeni. *YAHUNDE! Babban birnin ƙasar Cameroon.* Cikin wani kekyawan rugar FULANI mai tarin al'barkatun duniya. Kota wani sashi Allah yayiwa Rugar Arɗo Babayo, ni'imomi na musamman, makiyaye ne cikakkun Fulanin ƙasar Cameroon. Ranar wata jumma da yammaci la'asar sakaliya, makiyaya nata dawowa gida yayinda kota ina. Shanu tumaki raƙuma awaki zabbi keta kai komo ko wanne na nufar garken ma-mallakinshi domin ko dabba tasan uban gijiyinta, Garken Arɗo Babayo yana ɗaya daga cikin garken da babu kamarsa a nahiyar Afirka baki ɗaya, Yanada MAKIYAYA a ƙala mutun arba'in. Garin ya fara duhuwar sanire alamun yanayin sanyin damina da ake ciki ko ina yayi kore shar ga tarin tsirrai kana ga igiyar ruwa da yayiwa rugar Babayo ƙawanya, Wasu dattawane a zaune bisa ƙarƙashin bishiyar ceɗiya dake ƙofar gidan Arɗo babayo Farin dottijon ne mai cikar zarra da mutun taka ke zaune a tsakiyarsu, kana sai wasu manyan mutane dake zagaye dashi. A gefen damanshi kuwa wani Babban mutun ne mai cikar zarra da wadatar zuciya ga tarin alamomin mutuntaka da cikar imani da haiba, bisa dukkan alamu tattaunawa sukeyi kan abinda ya shafi rayuwarsu. Da sauri Arɗo Babayo ya ɗago kanshi ido ya zubawa sashin damanshi, inda ya hango wasu ƴan saffa-saffan samari guda huɗu suna biye da ƙatuwar suntsuwar Boleru babban cikinsu ne a gaba wanda zai kai shekaru 15 sa mai binsa wanda zai kai shekaru 13 sai mai bin masa da zai kai shekaru 11 kana sai ƙaramin cikinsu da bazai gaza shara 9 ba, gudu sukeyi sosai da iya ƙarfinsu sun tasa tsuntsuwar Boleru nan a gaba wacce ta kasa firewa sai gudu takeyi da sawunta biyu, bisa dukkan alamu tsuntsuwar tanada tsohon ciki mai girma. Gudun da takeyi gudune na ceton rai. Arɗon Babayo daya buɗe baki kenan da nufin zaiyi magana sai kuma ya juyo ya kalli kekyawar yarinya ƴar kimanin shekaru 8 a duniya wacce take kan cinyar mutumin nan dake gefen damanshi. Ta miƙe da sauri cikin tsananin azama da harshen fillanci da ƙarfi tace. ("Acce mo) Ku barta". Sai kuma ta juyo ta fuskanci mutumin da take zaune kan cinyarshi cikin kaɗuwa da firgici da alamun tsananin tausayawa tace. ("Appa a vi'a ɓe acca tokkugomo nɓe naunanmo) Appa kace su dena binta zasuji mata ciwofa". Murmushi Arɗo Babayo yayi tare da cewa. "Kai Gainako ku barta zaku kamata a hankali ai". Da sauri wanda aka kira da Gainako yace. "Baffa Giɗaɗo ne yace mu kama mishi ita mu yanka mishi". Da sauri suka juyo kan ƴarinyar jin wani irin ihu da tai tare da cewa. "Ku yankata kuma, Appa kajifa wai zasu yankata, wayyo Appa kace musu kar su yankata, gashifa tanata kuka gashi sun sa taji ciwo a hannunta yanata zunda jini". Da mamaki suke kallon ƴarinyar sabida furucinta na wai hannunta yaji ciwo yana zubda jini, ina tsunstsuwar Boleru ina hannu?. Wanda ta kira da Appa ne ya jawota gabanshi tare da cewa. "Parvina tsuntsu kuma tanada hannune?." Da sauri ta miƙe tare da ɗaga murya tace. "Ba tsuntsu bane Appa wlh mutunce gata nan da ciki gashi ma tana kuka tana-ta kare cikin jikinta". Cikin mamaki suka zubawa tsuntsuwar Boleru ido su dai Allah ya gani gaba ɗayansu tsuntsuwa suke gani tana guduwa da kyar wanda kuma kowa ya ganta yasan tanada tsohon cikine. Giɗaɗo ne wanda shine ƙarami yaron ɗan shakara 9 kuka yasa tare da cewa. "Wayyo ya Gainako kayi sauri ka kamo min ita karta gudu". jin haka yasa ƴarinyar nan da aka kira da Parvina ta miƙe da gudu tabi bayansu tana gudu tana kuka wanda har ga Allah daga cikin zuciyarta yake fitowa kuma ita ba tsunstsuwar Boleru take ganiba a zahiri a fili da kuma baɗinin Allah ya nuna mata mutum take gani kekyawar mace mai cikar sura da kamala kana ga ƙaton cikin dake jikinta wanda haihuwa yau ko gobe. Ihu takeyi tana binsu tana cewa. "Dan Allah ku barta zataji ciwo Wayyo Appa kazo mu ceceta zasu kasheta." Ihu tasa da dukkanin ƙarfinta tana yarfa hannu cikin gigita take kurma ihu lokacin da su Gainako suka isa kan tsuntsuwar Boleru suka danne fikafikinta suka kama suka medata baya. Ihun da tayine yasa gaba ɗaya dattawan nan suka miƙe tsaye suka biyosu a guje dan ihun nata ya cika illahirin rugar babu wanda zaice baiji ƙaranta ba dan saida tsaunuka da kogin da suke gaɓarsu ya amsa da sautinda da take cewa. "Wayyoooooooo! Appaaaaaa! zasu kasheta, sun karya mata hannu". A gigice suka ƙaraso wurin wanda ganin yadda take a gigice yasa Appa kamata da sauri, yayinda ita kuwa taketa son zillewa tana fiffizgewa daga hannunshi, Arɗo Babayo kuwa tsawa ya dannawa Gainako tare da cewa. "Kai! Kai!! Kai!!! Gainako sake tsunstsuwar nan saketa". cikin sanyi Gainako ya sake tsunstsuwar, daga tsaye ta faɗi ƙasa hakan yasa, Parvina sake saka ihu da ƙarfi ta fizge ta nufi kan tsuntsuwar da ita mace take gani kuma sanadin saketa da akayi daga sama ta faɗi ƙasa a kife yasa cikinta buguwa wanda yayi sanadin a take naƙuda ya fara murɗarta kana ga jini daya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185