Chapter 15
Chapter 15
kuma sauri-sauri, Kai ta sunkuyar tare da cewa. "Duk ƙarshen wata daga 21 zuwa 25". Shiru yayi kamar bai jitaba sai wasu rubuce-rubucen ya kumayi. Saida ya gama sannan ya tura mata folder ɗin gabanta. Jikinta na rawa tasa hannu ta ɗauki folder ɗin, ta yunƙura zata tashine, ya basu damar samun kusanci da juna, da sauri ya rumtse idanunshi sabida wani irin azabebben bugu da zuciyarshi keyi tamkar zaiyi tsalle ya faɗo woje, cikin zuciyarshi yake maimaita. "Innalillahi wa innailaihi rajiun." A hankali ya buɗe kyawar kyawan idanunshi jin bugun zuciyarshin ya fara yin ƙasa-ƙasa, ido ya zubawa mata ganin ta juya tana tafiya, wani abin al'ajabin a gareshi shine duk taku ɗaya da zatayi tana nesanta dashi sai yaji zuciyarshi na tsinkewa yana bada wani mugun bugun ras-ras, yayinda bugun tsinkewanta kuwa yaketa dai-dai-ta, Cikin mamaki ya sunkiyar da kanshi yana kallon yadda takeyin taku, tana riƙe da mararta, taje gab bakin fofar fitane, Taji wani irin murɗa da kartan da mararta ya farane yasa ta sakin wani sauti mai cike da wuya. "Wayyoooooooo Allah na, Wayyo Ummeyna cikina". Da sauri nurse ɗin nan yayi kanta tare da cewa. "Isah Allah rena joɗu". Ya ƙarishe mgnar da nuna mata kujerun farin ƙarfe dake gab da bakin ƙofar. Bata da zaɓin daya wuce ta zauna ɗin, domin gaba ɗaya ƙafafuwan ta rawa sukeyi alamun bazasu iya ɗaukar nauyinta ba ga duhun daya rufe mata ido. Sunkuyowa Nos ɗin yayi ya amshi folder kana yace. "Zauna bari inje Pharmacy in amso miki magungunan da alluran sai ayi miki". Kai kawai ta iya gyaɗa mishi tare da bashi. Har ya fita sai kuma ya dawo yace. "Ok sir". Jin Sheykh Jabeer yace mishi ya turo ta gaba Da sauri ya fita. Shi kuwa Sheykh Jabeer, tasbihinshi yaketayi da yankan yatsunshi yake ƙidayar, sabida, suma yatsun su kasance cikin bautar Allah shiyasa yake ƙidayar amman ba don wai yasan adadin salati da hailala da istigifarin da yakeyiba, wannan ubangijine kawai masanin adadinsu. Bayan fitar Nos ɗin da kamar 1 minute wata, Kekyawar budurwa ta shigo, cikin yauƙi da ƙasaita, sai wani irin masifeffen ƙamshin da take zubawa. Ƙarasowa tayi gaban table ɗin nashi ta zauna, cikin yauƙi da korkosa tace. "Barka da rana Al' Sheykh". Ko inda take bai ɗaga ido ya kallaba, ya lura ya gane akwai wani abu tattere da yarinyar, dan mafi akasarin ranaku sai tazo, wai bata da lfy, kuma takan zo da ciwuka mabanbanta ne. Sanin ba musulma bace yasashi ƙara tsuke fuskarsa tamkar zatayi aman wuta, a zafafe yace. "Name". Cikin yauƙi da son isar da aikin da aka bata tasa hannu ta jawo foldan ta dake sama tura mishi gabanshi tayi, Cikin harshen hausa da tasan bai fiye son English language ba a rayuwarshi a hankali tace. "Breast ɗina kemin ciwo, har bana iya sa bra." Sai kuma tayi ƙasa da mayafinta dake jikinta, hannu tasa kan zip ɗin gaban rigarta tana ƙoƙarin zugeshi ƙasa tare da cewa. "Kalli Nipples ɗin sun.... Cikin tsananin firgita da tsoro, ta miƙe da azaban ƙarfi, jin yadda yasa hannunshi ya bugi table ɗin da azaban ƙarfi wani irin gigitaccen tsawa mai firgitarwa ya daka mata tare da cewa. "Tashi, daga gabana". Karkar jikinta ke tsuma sabida kwarjinshi da tsoronshi sun daki zuciyarta da take cike da fajirci dama dan bata kallon fuskarshi ne ta iya faɗin waɗannan kalaman ma. Dai-dai lokacin kuma, Nos ɗin nan ya shigo, ganin yadda AYSHA ta gigice taketa karkarwa, alamun tana son ta miƙe kuma ta kasa tashi. Shi kuwa Sheykh foldan ɗin Rabeca ya jawo wani rubutu yayi saman foldan ɗin kana ya tura matashi gabanta cikin zafi da tsauri ya nunata mata hanyar fita tare da cewa. "Fice min daga Office daga yau in kina buƙatar ganin Dr kije gun Dr Ute, shi zakiyiwa duk sakarcinku na al'jihun baya. Ba niba, sannan daga nan ki wuce Zaria kije asibitin Shika domin ina zaton breast cancer kike dashi". Da sauri tasa hannu ta ɗauki foldan ɗin, gaba ɗaya jikinta na rawa, juyawa tayi ta fice tare da yin magana can ƙasa yadda bazai jitaba tace. "Allah ya sauwaƙa Ni bani da breast cancer, mugun bakin kawai." Shi kuwa Sheykh Jabeer komawa yayi ya jingina da jikin kujerar lumshe idonshi yayi a ranshi yake haɗa kalaman da yaci karo dasu a safiyar yau. Kakarshi tace mishi, aji mgnar Malam kada a duba aikinshi, ta jaddada mishi, wai yayi aure, kana wannan mayyar yarinyar da in tana kusa dashi zuciyarshi ke barazar fashewa, kuma tace mishi wai shine shugaban tuzuran ƙasar nan baki ɗaya. Tabbas wannan shaidace na abinda ake faɗa a cikin gari a kansa kenan, yaji ya sani Sitti ma da take son suje saudia wai so take ya zaɓi matar aure a can, ga wannan kafurar da ya san turota akeyi ta tallata mishi kanta, don a samu cinikin jarida ya hauhawa ta hanyar buga kanun labarai cewa, Sheykh mazinacine ko kuma mata yakebi shine ya hanasa aure. Jingina kanshi yayi da kujerar tare da mgn a zuciyarsa. "Ya ilahi ya mujibadda'awati". Ta yayane ta inane wa zai gayawa cewa, shifa yanada banbanci da sauran maza, ba kamar kowa yake ba, taya zai gaya musu ko zai samu a daina binshi da kalmar yayi aure, me zaiyi da mace ta yaya zai fahimtar dasu su barshi ya huta. Wannan shine nazarin da yakeyi cikin zuciyarshi, Ita kuwa Aysha ido ta tsurawa, ƙasan kujerar da yake zaune a kai tana kallon wani al'amari mai cike da ruɗarwa. Ido ta rumtse sabida bazata iya jurar ganin wannan abun ba. A hankali Nos ɗin nan ya matso gabanshi, magungunan da alluran daya amso ya miƙa mishi su. Cikin sanyi yace. "Sir ga magungunan". Kanshi ya ɗan tankwarar tare da cewa. "Kira Dr Ruƙayya tazo ta mata alluran". A hankali yace. "Sir na duba duk sun tashi, sabida babu kowa. A Reception ɗin, mune kadai muka rage". Kanshi ya jinjina, don shima yanzu zai tafi, sabida akwai gidajen likitocin a nan kusa koda shi ya tafi Dr Ruƙayya da Dr Ute suna nan cikin makarantar. Ta gefen idonshi ya ɗan kalli Aysha daketa fama da ciwo, Ganin Nos ɗin na haɗa allurar ne yasashi, fara tattara woyoyinsh dake bisa table ɗin. Shi kuwa nos ɗin. Yana gama haɗa alluran ya nufi inda take, tare da cewa. "Gyara in miki alluran". Cikin sanyi tace. "To". Yana isowa gabanta yace. "Dole ai sai kin tashi tsaye, kinga doguwar rigace a jikinki kuma sai kin naɗeta". Ido ta ɗan zuba mishi ta cikin niƙabin tare da jujjuya kai a hankali tace. "Um ummm". Kanshi ya gyaɗa tare da cewa. "Tashi mana sauri mukeyi lokacin sallah ya ƙara to". Shi dai Sheykh ido ya zubawa bayan Nos ɗin yayinda ita kuwa yake kallon gefenta, cikin bada umarni yace. "Kuzo". Da sauri Nos ɗin ya juyo ya nufoshi, hannu yasa ya amshi allurar, kana ya ɗan kalleta a fakaice yace. "Zo nan". A hankali ta taso cikin sanyi takeyin taku tana matsoshi. A take kuma bugun zuciyarshin ya fara hauhawa yana komawa matakin sama. Taku biyu tayi ana uku yaji ƙirjinshi ya bar tsinkewar da yaketa yi ɗin, sai kuma bugun da yakeyi da sauri-saurin ne yaketa tsananta. Taku takwas
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185