Chapter 141
Chapter 141
da azumi. Duk kuyi niya, ɗaukar azumi talatin ko talatin ba ɗaya." Sai ya kuma ya ɗan tsagaita tare da kallonsu Jalal da Jamil cikin sanyi yace. "Dan Allah Jalal Jamil ku nitsu kunsan halin da muke ciki. Kun san matsalar rayuwarmu kunsan damuwarmu, wannan dama ce da zamu yi amfani da ita wurin tsananta addu'o'in ba dare ba rana. In sha Allah, Wata rana komai zai dai-dai-ta domin Allahu sami'uddu'a ne. Jamil kaji tsoron Allah ka ribaci wannan watar, ka raba kanka da zuwa club, ka yayewa kanka masifar nacin liƙewa mata da waya." Juyowa yayi ya ɗan kalli Jalal kana yaci gaba da cewa. "Jalal yawon bin yan iska da wani shegen shiga mara kan gado ba tsarine na Musulmin ƙwarai ba. Aunty Juwairiyya Hibba Ummi Ke uwar bacci". Ya ƙarishe mgnar da kallon gefenda Shatu da take zaune tana ɗan lullumshe ido, da sauri ta waresu don a sama taji muryar tasa. Baki ta tura tare da sunkuyar da kanta, shi kuma jenye idonshi yayi daga gefen da take cikin ɗan ɗaga sauti yace. "Watan Ramadan ya bambanta da sauran watanni. Domin a cikin watanne daren laylatul Ƙadir yake, kuma a cikin watanne Allah ya sauƙe al'ƙur'ani mai girma. Kana a cikin watar akwai ranakun da malamai sukeyi hasashen a daren laylatul Ƙadir yake, Daren 21, 23, 25, 27, 29. Sai dai ba'a tabbatar, da sahihin rana ɗaya tsayeyye ba ƙauli mafi rinjaye shine ranar 27. Abi mafi kyau shine kada mutun ya sake koda dare ɗaya na Ramadan ya wuceshi. Mu raya dararen da ibada da ambaton Allah, wajibine mutum ya tsare bakinsa, da munanan zantuka walau a baki walau a rubuce a social media, Domin mu ribanci watar da ambaton Allah da samun ruɓanyar lada, wannan abubuwane da kullum nake gaya muku su, sai dai aiki dasu ya gagareku." Kusan haɗa baki sukayi wurin cewa. "In Sha Allah zamuyi ƙoƙarin kiyayewa". "Allah yasa yace, tare da sallanmansu duk suka fita sai Ya Jafar da Ummi. Ganin yadda Hibba keta zuba hamma ne ya sashi cewa. "Muhibbat tashi Kije ki kwanta". Kusan a tare ta mike ita da Shatu. da sauri yace. "Banda ke". Cikin bacci ta turo baki tare da cewa. "Ayyah dan Allah fa". Murmushi Ya Jafar yayi tare da zuba mata ido. Wanda koda baya mgna ana iya gano yadda yake sonta a ranshi, so kuma irin son da yakeyiwa su Hibba. Ummi ce ta ɗan kalleta tare da cewa. "A barta tai bacci aiki mukeyi tun ɗazu". Shiru bai kulasuba, ganin haka ita kuma tabi bayan Hibba. A zatonta bai saniba, har sunje bakin ƙofar taji yace. "Saura ki binƙire kiyi ta bacci, kada ki tashi ki raya daren. Sai gari ya waye ki buwayi mutane da ife-ife da rashin kunya". Ya ƙarishe mgnar cikin jin haushinta tare da Binta da kallon fitinenneyar yarinya. Ganin Ya Jafar ya miƙa ya juya zai fitane yasa yayi saurin. Bin bayanshi ya rakashi kana ya dawo ya konta. Ummi ma ta konta. Ƙarfe ɗaya da rabi Sheykh ya tashi yayi ta nafilfilinshi tare da jere addu'o'in da neman warakar damuwar rayuwarshi data ahlinshin. Ummi ma tuni ta tashi. Ƙarfe uku ta fito. Falon hango haske a ɗakun Shatune ya tabbatar mata sun tashi. Kitchen ta wuce. gas ta kunna ta ɗumama musu miyar, kana ta haɗa plate spoons and cups tazo ta jere bisa Dinning table. Sannan ta koma kitchen ta ɗauko musu drinks and water masu sanyi tazo ta jere komai yadda ya dace. Kana ta dawo falon ta zauna riƙe da carbinta. Ƙarfe huɗu dai-dai su Jalal suka buga ƙofar sanin sune yasa, ta tashi ta buɗe musu. Suna shiga ana buga bindigar sanarda mutanen masarautar Joɗa cewa lokacin sahur yayi. Bayan mintuna talatin kuma za'a kuma sakin bindingar. Cikin gudu Shatu ta fito falon jiki na rawa, kiciɓis tayi da Ummi da takeda niyar zuwa ta ta kirasu suzo suyi sahur. Ruggume Ummi tayi ƙam-ƙam tare da neman inda zatasa ranta. Allah ya sani tana tsoron ƙaran abu biyu, ƙaran aradu da walƙiya da kuma ƙaran harbin bindiga". Cikin mamaki Ummi tace. "Oho Aysha duk wannan tsoron na ƙaran harbin bindiga ne, lallai kuwa in baki sababa kafin Ramadan ya ƙare zakisha wuya." Hibba ce ta fito tana dariya tace. "Allah ko Ummi ana ɗaukan alhaƙin Aunty Aysha". Babban Falon suka nufo yayinda duk jikinta ke karkarwar." Dinning area Suka wuce. Bayan duk sun zaunane Ummi tace Hibba tasa musu abinci. Buɗe kulolin tayi. Jolof ɗin taliya da kifi Aunty Juwairiyya tayi, sai kuma Flaks ɗin kunun gyaɗa. nasu kuma tuwon semo da miyar ɗanyar kuɓewan sai tea da sauran kayan sha. Ta zubawa kowa abinda ranshi keso. ita dai Shatu mamakin abincin Aunty Juwairiyya na yau takeyi sabida idonta bai gano mata wani mugun abu a cikiba. Haka yasa itama shi taci. Da kunun. duk sunyi nisa a yin sahur ɗin. Amman shi bai fitoba, Sai ƙarfe huɗu da rabi ya fito. A hankali ya iso Dinning area ɗin gaban washing hand Baby ya ɗan tsaya tare da wonke hannunshi. Ita kuwa Shatu tana ganinshi ta ɗanyi gyatsa tare da cewa. "Alhamdulillah kana ta miƙe". Kujerar dake gefen Jalal ya zauna, Yana zama ita kuma ta juya ta nufi cikin falon. Shi bai ma kalli inda takeba. Cikin falo ta koma hannunta riƙe da cup ɗin kunun da take sha. Cikin kula Ummi tace. "Sai yanzu?". ta ƙarishe mgnar tana zuba mishi tuwon semo da miyar ɗanyar kuɓewar da yaji nama da kifi da man shanu. gyara zamanshi yayi tare da cewa. "A jinkirta sahur a gaggauta buɗa baki Ummi Manzon Allah yace." Murmushi tayi tare da cewa. "Hakane". Bismillah yayi tare da gyara zaman shi, ya fara cin abincin. yaci mai ɗan yawa dan daren jiya baici komaiba. tea ta haɗa mishi. Hannunshi ya wonke kana ya amshi tea ɗin ya fara sha. Jalal, Jamil, kuwa ci sukayi sukayi haninƙan kana suka miƙe zasu tafi. Cikin kallonsu yace. "Kadafa kuje ku kwanta, kuyi al'wala ku wuce masallaci." To sukace kana suka tafi. Shi kuwa yana gama yin sahur ɗin ya koma Side ɗinsa, Wonka yayi tare da al'wala kana yayi shigarsa ta farar jallabiya. Bayan sun idar da salla gari ya ɗanyi hasken ya taso ƙeyansu, suka dawo gida. Side ɗin su suka wuce. raka Ya Jafar yayi har Side ɗinsa kafin yazo ya shiga sashinsa. Shiru falon babu kowa, bisa alamu kuwa tuni Ummi ta kimtsa ta share da goge ko ina, ta sassake labulaye, tare da sa turaren wuta mai ƙamshi. Kana ta kashe hasken ko ina, babu abinda ke tashi sai ƙamshi da sanyin A/C da karatun Alqur'ani mai girma da kuna. Falonshi ya nufa yana shiga, ya zauna a falo, Dua Azkar ya fara yi cikin zazzaƙan muryarshi. Bayan ya isane kuma ya fara karatun al'ƙur'ani. Sai bakwai da rabi dai-dai ya shafa addu'a kana ya wuce bedroom ɗin shi. Wutan ya kashe tare da ƙara ƙarfin gudun AC. sannan ya nufi luntsumemen gadonshi ya kwanta bisa gefen damanshi tare dasa hannun ya jawo blanket ya rugu. A hankali lips ɗinshi ke motsawa, alamun tasbihi yakeyi. Cikin 13 minute bacci mai daɗin gaske ya kwasheshi". Haka can wurinsu Shatu ma, saida tai karatun al'ƙur'ani sosai kafin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185