Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 125

Chapter 125

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wakilai, shi a zatonsa ma shine mahaifin Jabeer cikin sanyi yace. "Kai kuma kaine matsayin mahaifi a gareta ku zame mata dangin ta data rasa, naso ace da mata a masu ɗaukanta, dan in danƙa amanarta a hannun macce yar uwarta. Amman ba komai, na baku amanarta dan Allah kada a cutar da ita, domin nima ta kasance amanace a uwurina, domin ƴaƴan mu da muka haifama amanace Allah ya bamu kuma abun kiyayewa, bare kuma ɗiya irin Shatu ɗiyace da take da nasabobi masu yawa a gareni". Cikin gamsuwa Lamiɗo yasa hannunshi ya amshi hannunta daketa karkarwa, tuni niƙab ɗin fuskarta ya jiƙe jilak da ruwan hawaye. Cikin Dattaku Lamiɗo yace. "In sha Allah zan kula da dukkan lamuranta tamkar yadda nake kula dashi Jabeer, kuma kada ka damu akwai masu meye mata gurbin uwa ƙanwa yaya dama duk danginta a cikin masarauta Joɗo, baƙoma baya kukan maraici bare kuma, matar sashin jinina". Cikin sanyi da wasu hawaye Bappa yace. "To Ngd matuƙa". Arɗo Bani ne ya dafashi tare da cewa. "Ka sanya mata al'barka a cikin aurenta ba zubda hawaye ba." Sosai Haroon ya zuba mata ido. Shi kuwa Sheykh Jabeer da mamaki yake kallon Bappa dake zubda hawaye. A hankali su Bappa suka ɗan ja da baya. Shi kuwa Lamiɗo ya juya ya nufi motar riƙe da hannunta. Haroon ne yayi saurin buɗe musu marfin motar, suka nufoshi gadan-gadan. Jalal kuwa ido ya zubawa yatsun hannunta da Lamiɗo ke riƙe dashi. Shi kuwa Jabeer idonshi ya rufe da ƙarfi. Sai kuma ya buɗesu, dai-dai lokacin Lamiɗo ya kawota bakin ƙofar motar tare da cewa. "Mamana kiyi bismillah ki shiga da ƙafar dama". Cikin shessheƙan kuka ta gyaɗa kai tare da yin bisimilla kana ta ɗan sunkuyo, sai kuma kukan ya kubce mata. Shi kuwa Jabeer da sauri ya buɗe marfin motar ta gefen hagunshi. Kamar gilmawar walƙiya ya fita cikin motar. Dai-dai lokacin da Shatu tasa ƙafarta ciki. da sauri yasa hannunshi ya buɗe motar Jadda tare da shigewa ciki yaja marfin ya rufe sabida ji yayi zuciyarshi zatayi bindiga, wani irin dogon ajiyan zuciya ya sauƙe mai ƙarfi. Ita kuwa Shatu, a hankali ta shiga ta zauna, don batama lura da shi bane tabbas dai taga mutun ya fita cikin motar. Tana shiga Haroon ya maida marfin ya rufe Shida Lamiɗo suka koma sit ɗin bayan wannan sabida su a zatonsu Jabeer na ciki. Ganin Lamiɗo ya shigane yasa duk kowa ya shiga motarshi. Hakama Jadda ya shiga ya zauna hankalinshi na woje. Sai da akaja motocin suka fara tafiya ne, ya juyo da sauri jin Jabeer na jan wani ja'irin tsaki mai tare da ajiyan zuciya. Cikin mamaki Jadda yace. "Haaahh kai kuma Meya kawoka nan? Yaushe ka shigo min mota!?". Bai kula Jadda ba, asalima yi yayi tamkar bai jishiba. Haroon kuwa cikin dariya ya ɗan bugi sit ɗin da yake zaton yana wurin cikin juya harcen Larabci yace. "Masha ALLAH, gasar Shaɗi tayi mana rana mun rabaka da gwauranci". Murmushi Lamiɗo yayi tare da kallon Haroon yace. "Saura kai". Murmushi yayi tare da cewa. "Ni ai nan kusa za'ayi". Jin shirune, yasa Haroon yayi shiru, Azotonshi ya ƙin mgna da shariyar ne suka zowa Jabeer bare, yasan yanzu a cike yake. Su Jalal kuwa kab da al'hini suke tafeyi. Jadda kuwa yayi iya mgnarshi yayi shiru ganin bai kulashi ba. A haka suka isa cikin Masarauta Joɗo. Suna isa kuwa Jabeer ya fito ya nufi Side ɗinsa, fitowarsa cikin motar Jadda ne yayi matuƙar bawa Haroon da Lamiɗo mamaki. Haroon kuwa bayanshi yabi da sauri. Suna shiga Side ɗinsa kuwa suka samu babu kowa. Suna gama tsayuwa Sallama ya nufi Side ɗin Gimbiya Aminatu bisa umarni Lamiɗo. Yana shiga a babban Falon ya samu. Umaymah, Ummi, Aunty Juwairiyya, Hibba, Adda Rumana wacce take yayarsu Jabeer yar farin Abba kenan, sai mai bin mata Rumaisa. Kana sai Gimbiya Aminatu dake tsakiyarsu, sai hadimanta. Koda ya sanar musu, sun iso. Kusan duk a tare suka miƙe sai Gimbiya Aminatu ce bata tashiba da hadimanta. Su kuwa da sauri suka nufi woje, Umaymah ce gaba sai Aunty Juwairiyya dake biye da ita a baya riƙe da wani tire wanda samanshi ke ɗauke da al'kyabbar irin tasu ta matan masarauta da kuma wasu sauran tarkace. Suna fitowa motar na isowa har bakin wurin. Da sauri suka nufi jikin motar. Ita kuwa Zuwa yanzu ta tsagaita da kukanta, sabida ababen da take gani a cikin masarautar ya shallake tunanin mai tunani, gaba ɗaya jikinta tsuma yakeyi, sabida idonta na gane mata ababe na ban tsoro. Cikin ranta take mgnar zuci. "Innalillahi wa innailaihi rajiun, wannan wanne irin gidane? Me yake faruwa da mutanen masarautar? Sunko san gskyar junansu?". Da sauri ta rumtse idanunta sabida wasu irin hayaƙi da take gani yana tashi tako ina na gidan yayiwa gidan rumfa gaba ɗayansa. A da sauri ta buɗe idonta jin an kamo tafin hannunta, Umaymah kuwa cikin tsantsar jin daɗin da farin ciki maras misaltuwa tace. "Marhababiki ya binti". Wani irin azabebben tsinkewar zuciya da firgici da razanine ya daki zuciyar Shatu a lokaci ɗaya. Da sauri ta ƙara ware idanunta, dan son kallon matar da take jawota tare da cewa. "Kiyi bismillah ki fito da ƙafar dama, ki riƙe hannuna da kyau ɗiyata, ki kalleni nan nice jagorarki ki taka ƙafarki a inda zakiga na taka tawa". Ido ta zuba mata, tare da fitowa a hankali. Tana fitowa bakin ƙofar Umaymah tasa hannu ta amshi al'kyabbar da Aunty Juwairiyya take miƙa mata. Kangeta tayi kana tasa mata al'kyabbar, sannan ta gyara mata rufuwarshi da kyau ta rufa mata hularshi. Yadda sam mutun bazai samu damar ganinta ba. Ga niƙab ga kuma hular al'kyabbar da lu'ulu'u danke reto a fuskarta. Da sauri Aunty Juwairiyya ta matso tare da cewa. "Marhabin yar uwarta, Alhamdulillah yau kam na samu yar uwa". Adda Rumana ce ta matso kusa da ita tare da yin mgna da fillanci tace. "Sannu da zuwa Masarautar Joɗa ƙanwata". Adda Rumaisa kuwa murmushi yaketayi tare da matsowa, haka suka sata a tsakiya. Jakadiyarsu kuwa sai bin takun ƙafar Shatu takeyin da ido. A haka suka zagayeta, kana hadimai suka mara musu baya. A haka suka isa babban falon Gimbiya Aminatu. Suna isa Umaymah ta kaita har gabanta ta ajiyeta, Cikin tsantsar jin daɗi tace. "Alhamdulillah Gimbiya yau dai ga sabuwar Gimbiya dan yanzu itace amarya ba keba". Cikin dariyar jin daɗi Gimbiya Aminatu tasa hannu ta kamo hannun Shatu da Umaymah ke miƙa mata tare da cewa. "Kishiya ban haushi, ta isa ta zama Gimbiya zakisa yanzu in korata woje". Dariya sukayi baki ɗayansu. Yayinda tuni hadimai mata suketa jere ababen maƙulashe a gaban Shatu. Danginsu, Zuma, Madarar shanu, Da ƴaƴan itatuwa masu sanyi. Ita dai Shatu ƙasa tayi da kanta, tana jin fargaba da kuma tsoron wannan bahagon gidan data shigo. Su kuwa nan sukayi ta mata hidima da nuna mata so. Ganin magriba ta ƙara to ne yasa, Umaymah ta jawo hannunta ta kaita wani ɗaki dake nan kusa dana Gimbiya Aminatu. Tare da cewa. "Yauwa ɗiyata kiyi salla. Za'a kawo miki abinci, kada kici komai sai nazo". Cikin sanyi ta gyaɗa mata kai. Ita kuwa Umaymah hannu tasa ta fara zare mata al'kyabbar, koda ta cire

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});