Chapter 112
Chapter 112
goma sha ɗaya. Ata goma sha biyu ne, da ya tsula mishi yayi wani irin gantsarewa sabida wani irin azabebben ƙaiƙayi da yaji wurin yanayi mishi. Da sauri yasa hannunshin a bayanshi alamun zai sosa. Ife-ife da sowan da matasa suka farayi ne da Muryar Barmuji na cewa. "Dokar gasa banda susa". Da sauri ya dawo da hannunshin tare da cewa. "To ya dane karatun da yakeyi, bana so, ya dena kira min sunan Allah". Wata bulalar Sheykh ya zabgawa shege tare da cewa. "Sunan uwarka zan kira maka in ban kira sunan Allah ba?". Arɗo Bani kuwa wani irin ajiyan zuciya mai ƙarfi yaja. Shi kuwa Ba'ana wani irin masifeffen ƙaiƙayi ne yakeji a duk inda Jabeer ya zuba mushi bulala, a bulala ta goma sha biyar ne, da aka zuba mushi. Yayi wani irin gantsarewan da yafi na ɗazu. Wani irin azabebben zafi da raɗadine yakeji yana tsarga mishi jiki da zuciya. Zuface ta ketomishi tako wanne sashi na jikinshi. Cikin sauri Jabeer ya juya bulalar ya amshi ta biyu ya haɗa data forkon. Ya damƙesu a hannun hagunshi. Wanda dama shi badamene kuma bahagone duk abinda hannun damanshi kan iya yi to na hagun yana fi iyawa. Sai dai kasamcewarshi mutun mai ilimi da sanin addini shiyasa yake amfani da hadinsin nan da Manzon Allah ke cewa. A cikin dukkan abinda zamuyi mu wakilta dama a forko, har dai sai in shiga bayan gidane aka ware shiga da ƙafar hagu. To juya hannun yayi da hannun hagunshi, kana ya riƙe mahaɗin al'kyabbar jikinshi da hannun damanshi. Gyara tsayuwarshi yayi kana ya ɗaga bulalar da ƙarfi ya zubawa Ba'ana a tsakiyar bayanshi. Wani irin azabebben ihu mai ƙarfin amo da karaji Ba'ana ya kurma tare da fara karkarwa kar-kar tamkar mai farfaɗiya. Ihun da ya kurmane yayi masifar tada hankalin dukkan kafurai magoya mayanshi. Arɗo Bani kuwa a gabansu Lamiɗo ya tashi tsaye ya juya ya fuskanci al'ƙibila yayi sujjada. Bappa ma da kanshi wani irin murmushin jin daɗi yakeyi. Hakama duk sauran dottawan. Shi kuwa Ba'ana wani irin azabebben kuma masifeffen zafi yakeji a dukkan sashin jikinshi. Wani irin tsalle ya buga da ƙarfi lokacin da aka kumayi mishi bulala ta ashirin. Wani irin tsuma da karkarwa jikinshi keyi hatta Ba'anansa miƙewa tayi tana karkarwa, wata tafasashiyar zuface ta sinƙo mishi, zafi yakeji har cikin ƙoƙon kanshi da zuciyarshi. Bulala ta ashirin da biyu akayi mishine yasashi fashewa da wani irin kuka mai azaban ƙarfi wani irin masifeffen fitinenne fitsarin azaba ya fara kwaranyo mishi, ihu mai cike da azaba yayi. Wanda gaba ɗaya rugar saida kowa ya jiyoshi. Ƙabilar ɓachama kuwa gaba ɗaya suma kuka suka saka. Shi kuwa Ba'ana da ƙarfi ya faɗi ƙasa yana burbuwa, tamkar wanda yayi al'janu. faɗuwanshi ƙasane yasa Jabeer rusunowa ya rinƙa tabka mishi bulalar, ihu da burbuwa da rarrafe alamun guduwa Ba'ana yakeyi cikin azaba da karaɗi da kuka yake cewa. "Wayyo! Wayyo!! Wayyo Bonon!!! Ka ceceni zan mutu zai kasheni. Wayyo Bononnnnnn! Yau bakayi min ranaba, ga bulalin karin sihirina sun iso gareni wayyoooooooo Bonon meyasa baka gaya minba na hudu tun kan wannan malamin ya kasheni ya karya min komai na jikina da sunan Allah." Ya ƙarishe mgnar da ƙarfi tare da miƙewa tsaye ya fuskanci kudu. Ya ɗiba a guje ya ari ta kare ya nausa a guje. Wani irin taku Jabeer yayi tare da biyoshi baya da sassarfa abunka da dogon mutun sai gashi ya isoshi a gigice ya fara kai mishi bulalin hagu da dama, Jin azabar ta zarce azabar da yake zatone, yasa Ba'ana kurma ihu da kururuwan da yasa kab mutane suka nufosu. Gudu yakeyi Jabeer na binshi yana zaneshi har ya fiddashi cikin taron gaba ɗaya. Barmuji ne ya riƙe hannun Jabeer tare da cewa. "A dokar gasa Shaɗi in dai ya gudu ka bishi ka korashi cikin farfajiyar shike nan ya faɗi a gasa kaci. Kuma bazai sake samun damar shiga gasarba bazai kuma sake zama a garinba." Wani irin busar sarewa da al'gaita kana da kiɗe-kiɗen tsantsar farin ciki, al'ummar Rugar Bani suka farayi. Sunayi suna zagaye Jabeer. Haroon kuwa da Arɗo Bani da Galadima miƙewa sukayi cikin farin ciki suka ruggumeshi. Jamil, Jalal, Imran, Hashim, Sulaiman. Suma kab farin cikine ya cika musu zuƙata. Laminu kuwa ji yakeyi tamkar ya shaƙo Jabeer ya karshi sai dai tabbas dama ya zaci aha dan shi mari ɗaya nema Sheykh ya masa ya kusan suma, shiyasa ya tausayawa Ba'ana. Lamiɗo kuwa jinjina kai yakeyi yana tattausan murmushi. Koda su Galadima suka ruggumeshi, Arɗo Bani kuwa kama hannunshi yayi ya ɗaga sama alamun yaci gasar Shaɗin. A haka suka iso gaban Lamiɗo hannunshi yasa ya dafa kan Jabeer tare da sanya mushi al'barka. Mutane kuwa duk an kacame da farin ciki. Ya Salmanu kuwa kusan suma yayi tsabar masifar jin daɗi. Alhamdulillah yau dai burinshi ya cika ya samu konciyar hankalin duniya an ɗauka musu fansa, shida masoyan Shatu na baya, harma da yayanshi. Jan gefe makaɗan suka sabi, da sauran zugar jamar gari. Jabeer kuwa mamaki yakeyi yadda yaga. Fulani nata shigowa garin tako ina wasu bisa dawakai wasuma ƙan raƙuma. Lamiɗo kuwa waya yakeyi da amalun a sirrance yake mgnar sabida ko Jabeer ɗin dake kusa dashi baya jinshi. Bisa umarnin Arɗo Bani ne aka rinƙa fito da ƙwaran nono da fura da dambu da ƙwaran zuma, Ana kawowa su Lamiɗo. Wanda fadawa da dogarai ne sukasha. A hankali Jabeer ya kalli Lamiɗo cikin gajiya yace. "To ai sai ku tashi mu tafi ko!". Shiru Lamiɗo yayi mishi, ganin hakane, ya gyara hiramin kanshi kana ya kuma cewa. "Mu tafi ko". Galadima ne yace. "Ai bamu gamaba". Cikin sauri Haroon yace. "To meya rage kuma?". Galadima ya buɗe bakin zai bashi amsa kenan. Sai kuma duk suka juyo suna kallon wasu tsala-tsalan motocine masu masifar kyau da tsada, suna shigowa Rugar Bani a jere-a jere. Cikin fidda numfashi Haroon ya ɗan kalli motocine da mamaki yace. "Ha Jabeer kalli wannan kamar tawagar motocin Uncle Abdulkarim da Abudulfata kalli kamarfa harda Jadda". (Sarki Jalaluddin suke cewa Jadda) Sai kuwa ya juyo ya kalli Lamiɗo cikin nitsuwa yace. "Lamiɗo lfy kuwa?". Kanshi ya gyaɗa mishi alamar eh Lfy kau. Shi kuwa Sheykh Jabeer cikin nitsuwa yake kallon ayarin motocin a fakaice tabbas. Su Jalaluddin ne da yaranshi. Kana ga kuma Baban Haroon, ga kuma su Dr Aliyu da Barrister Kamal da su Baba Basiru Baba Nasiru dama duk sauran manyan masarautarsu. Da sauri ya juyo ya kalli Lamiɗo da nufin yin tambaya sai kuma yayi shiru ganin Lamiɗo na mgna da Galadima da kuma wani amintaccen bafadanshi. Tsaki ya ɗan ja tare da cewa. "To wannan ƙus-ƙus du na menene, ku duk abinda babu kyau kuna jin daɗin yinshi." Shiru yayi ganin motoci sama da talatin ne suka shigo Rugar. Kana duk manyan mutanene kuma sun fito cikin motocin sun nufo inda suke zazzaune. Wanda tuni Arɗo Bani yasa an kuma firfito da taburman cikin masallacin su. Kana yasa an fito da sauran dardumai da kilisai anzo an shimfiɗa. Suna isowa sarki Jalaluddin da Abba suka dafa kafaɗun Jabeer tare da sanya mushi al'barka kana suka zauna gefenshi ya zama sun sakashi a tsakiya. Kusa dashi Abbanshi ya zauna, Kana Jalaluddin ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185