Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 169

Chapter 169

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tare da ɗaukan cup mai ɗan girma, Tea mai kauri ta haɗa a ciki kana, ta taho inda take miƙa mata cup ɗin tayi tare da cewa. "Gashi amshi kisha, aiki kam ai saida lfy". Amsa tayi tana murmushi a hankali tace. "Lfyata lau ai Ummi kawai dai baccin ne ban san meyasa nake ta yinshi ba". Kai kawai Ummi ta gyaɗa mata, Kana ta juyo tace. "Hibba kawo mana namu abincin nan muci. Najiyo Muryar Jamil suna zuwa, kuwa wata ƙil dasu Imran zasu zo". To tace kana ta ɗauko musu nasu Foodflaks ɗin da plate and spoons da ta kawo musu. Jolof ɗin taliyace da kifin banɗa dasu Kabeji da karas da green beans da dai sauran kayan haɗin. Sai kuma, ferfesun kayan ciki. A plate ɗaya Hibba tasa musu, da ita kana ta sawa Ummi. Kana tasa musu fork, tare da cewa. "Bismillah Aunty Shatu sauƙo muci ko". To tace kana ta sauƙo, suka fara cin abincin. Amman ina tayi loma ɗaya sai ta kusan 4 minute bata kuma sawa a bakiba. Sai dai ta shanye tea ɗin ganin hakane yasa Ummi ta ƙara haɗa mata wani shayin. Shima ta shanye abinta fes, taliyar kuma baifi cokali biyar ba tayi. Su Jalal kuwa suna shiga suka wuce Dinning area suma sukayi breakfast ɗin kana suka fita, sabida hidimomin salla. Domin yau za'ayi hawan daba, Jalal kuma mayene mai zaman kanshi a kan sarrafa, doki, ɗan daga Affan sai shi. Bayan Sheykh a iya sarrafa doki kab Masarautar Joɗa . Amman shi Sheykh ya daɗe da cewa shi ya girma da yin wannan sakarcin. Su Ummi kuwa, kitchen Suka kuma shiga. Sanin yau tabbas akwai baƙi masu ɗimbin yawa da masarautar Joɗa zata amshi baƙoncinsu. Domun ƙananan sarakunan wasu garuruwanma duk zasu zo da tawagar su. Haka yasa suka shiryawa taron haiƙan ƙadaran ko wani Side dake gidan za'ayi abinci a ciccika manyan kuloli a kai fadar Lamiɗo, wani a kai sashin bayi. Kana kuma ko wani Side da baƙin su. Haka yasa su Ummi da Saratu da Larai zagewa. Sukayi abinci kala-kala kana suka ciccika kulolin aka kai fada akai wurin bayi. Sannan sukayi nasu kuma suka sassaka a Foodflaks masu ɗan karen kyau suka jera a Dinning table, tare da plate, spoons, and forks. Kana sun cika Fridge kuma da drinks kala-kala. Sun kuma yi Pepper Checken mai zafi na zabbi. Sai kusan ƙarfe ɗaya suka gama komai, Su Saratu suka kimtsa komai kana suka tafi. Su kuma duk suka shiga ɗaki da nufin yin wonka. Tuni zuwa lokacin Masarautar Joɗa ta fara ɗinkewa da baƙi tako wani sashin. Sheykh Jabeer kuwa, tunda ya tashi. Ya nufi cikin Garden ɗin nan da ababen tarihin masarautar Joɗa yake. Zazzagayawa yakeyi yana dubawa, dan tabbatar da babu wani abun da zai cutar da wani ko wata. Sabida yasan yau manyan baƙi zasu shigo ciki. A nuna musu ababen tarihi da dai sauransu. Gefen da curin da macijiyar nan yake ya nufa. Ya dudduba ƙofofin ba hayaƙi ba komai. Sai dai in mutun ya kasa kunne zaiji sautin numfashin macijiyar ka da ƴan ƙanana kuka irin na ƙananan macizai. A hankali ya ƙara matsowa bakin curin. Cikin nitsuwa yayi gyaran murya. sai kuma yaji sautin kukansu da kuma numfashin uwar ya ƙaru sosai. A hankali yace. "Assalamu alaikum, ya ke wannan halittar Ubangijin sammai da ƙasai". Gyara tsayuwarshi yayi jin numfashin na ƙara matsowa. A hankali yace. "Ba cewa nayi ki fitoba, nazo in roƙeki ne kamar yadda Manzon Allah ya sanar mana, dukkan halitta tanaji. Kuma ina kaga wani abun cutarwa a gidanka ka haɗashi da Allah da Manzonsa kace ya fita. Manzon Allah ya bamu tabbacin. Muddin ba mai cutarwa bane zai fita. In yaƙi fita kuwa ka kasheshi". Ɗan zagaitawa yayi jin kukansu ya kuma tsananta, cikin sanyi yace. "Ni bazan roƙeku kan ku fita ku bar muhallin zamanku da ban san tsawon shekara nawa kuke rayuwa a wurinba. Kuma bansan dalilin zamanku a wurinba. Shiyasa bazance ku bar Masarautar Joɗa ba. Kuma bazan kasheku ba, Sai dai roƙana garemu. Munada baƙi a Masarautar Joɗa kuma yau zasu shigo, dan Allah da Manzonsa, kada ku fito ku baiyana kanku ga baƙinmu kada ku razana mana baƙi kada ku cutar mana da mutanenmu. Kuyi zamanku a muhallin ku". Shiru sukayi tsit alamun sun jishi kuma sun gamsu". Fahimtar hakane yasashi cewa. "Na barku lfy". Yana faɗin haka ya juya, Lamiɗo da Galadima ya gani tsaye a bayanshi. Murmushi sukayi tare da matsowa inda suke. Galadima ne yace. "Kada ka damu da fitarshi da zamanshi da yaranshi Domin kai ke ganinshi a nan, amman duk in da wani mugu ya shigo masarautar Joɗa da nufin yiwa Lamiɗo wani abun zai ganta da yaranta a gabanshi. Amman wanda yake jinin wannan gidan bazai ganshiba. In kaga mutun ya ganshi saida sahalewar Lamiɗo". Shiru yayi yana kallonsu. Shi kuwa Lamiɗo a hankali yace. "A ƙalla yafi shekaru ɗari biyu da arba'in a cikin wannan curi a wannan Masarautar tun zamanin baban kakana Joɗo yake nan, ba kuma tsafi bane, ba sihiri bane, kamar yadda kowa ya sani shi maciji curi gidan zamansa ne, to bulalin caɗin masarautar Joɗa kuwa suma asali nan suke da zama curin ne ya binnesu, kana macijiyar ta shiga ciki, shine ma dalilin hana shaɗi to sai dai lokaci zuwa lokaci in an sarki maici yazo wurin yayi sallama macijiyar kan fito, in zata fito takan fito da balalin a binɗinta. Sai daga baya ta fara fita ita da ƴaƴanta suna yawo cikin masarautar Joɗa ne, muka gane yunwa ke sata fitowa, sai ta shiga cikin kaji tasha kwayaye ta haɗi ƙananan kaji. Lokacin da muka fuskanci haka sai muka fara kawo mata kwai a matsayin abincinta. Daga baya muka fahimci in mutun ya shigo da mugun nufi tana razanashi". Taɓa bakinshi yayi cikin rashin yarda bare gamsuwa yace. "Ni dai ban tambayeka ba, inma tsafine kaidashi Ni nan Muhammad Jabeer bani dalaifi a ciki nayi-iya yina in rabaku da wannan tsarabe-tsaraben na masarauta kun ƙiya". Ya ƙarishe mgnar yana juyawa ya nufi wurin da tsuntsayen wurin suke. Gefenda aku yake ya nufa. Tana ganinshi ta kaɗan fiffigenta tare da cewa. "Sheykh Jabeer ya dawo". Murmushi yayi tare da shafa kan akun yace. "Ya dai tsuntsuwa mai daraja ya gida". Cikin irin mgnarsu na Ali tace. "Lfy Sheykh ya madina garin Manzon Allah". Ta ƙarishe mgnar tana kaɗa kanta da jelarta alamun yiwa sauran tsuntsaye rigimar ance mata tsuntsuwa mai daraja. Murmushi mai faɗin Sheykh yayi ganin. Ɗawisun nan tazo gabanshi ta tsaya ta buɗe dogon jelanta ta kaɗashi tayi sama dashi. har yana taɓa gemunshi cikin sanyi yace. "A a kekyawar tsuntsuwa mai kyan ado da tafiya". A hankali ta karkaɗa jelan kana ta fara zagayashi. Tana nuna mishi kyan tafiyar. Su kuwa sauran tsuntsaye kuka suka farayi. Murmushi mai faɗi ya kumayi tare da cewa. "Tsuntsaye masu zaƙin murya da sauƙin firewa". Aifa nan suka tashi sama suna shawagi a wurin. A hankali ya juyo ya kalli tarin tattabarun dake gabanshi mazan ciki suna ƙotowa wa matansu. Kai ya rausayar tare da cewa. "Iyayen soyayya duk cikin tsuntsaye bayaku a soyayya". Ai sai suka fara irin kukansu nan guggdu-gudduu guuu". A hankali ya fita

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});