Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 57

Chapter 57

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gaba da baya, kamalarsa da kwarjini shi ya cika dukkan idanun bani adam dake kan doron ƙasar wannan wurin. Ya Hashimu ne da ya samu ya dawo gida jikinsa da sauƙine, yayi wani irin kabbara mai ratsa zuciya, cikin sanyi yace. "Ziyararku tayi haske sabida kun zo mana da mai hasken addini a jiki da zuciyarshi". Ga mamakinshi sai yaji Ɗanzagi na cewa. "GARKUWA ya amsa Sheykh Jabeer Jikan sarki tsatson sarki gaba da baya". Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali yake takunda yasa al'kyabbar sa buɗuwa tana bajewa, sabida ɗaga hannunshi da yayi yanai musu sallama irin ta addinin Musulunci. Mafi akasarin mutanen tafukan hannunshin suka zubawa ido, sabida kai da ganin tafin hannunshi kasan ya gauraye da ni'imar ambaton sunan Allah da rike littafi al'ƙur'ani, da kuma jin daɗin. Shi kuwa Jabeer ƙara sarƙafe carɓin shi yayi cikin yatsun hannunshi, kana, ya fuskanci gefen hagunshi, ya ɗanga musu hannu tare dayi musu sallamar kamar yadda yayiwa yan gefen damanshi. A haka har suka isa tsakiyar ƙaton filin. Inda Lamiɗo da sauran tawagarsa ke zaune. Bisa fararen kujerun robar da anka jera musu cikin rumfar suka zazzauna. Bayan sun amsa musu sallamar da sukayi. Cikin nitsuwa Lamiɗo ya kallesu tare gyara zamanshi. Muryar Ɗanzagi ce ta karaɗe wurin da cewa. "Gyara kimtsi. A saurara dai Lamiɗo jikan ɗan Lami Bubayero jikan Lamiɗo Joɗa zaiyi mgna". Wani irin harara suka watsawa Danzagin, shi kuwa Lamiɗo cikin nitsuwar datattaku tace. "Da farko dai zan fara da baku haƙurin zalumcin da akayi, muku, Allah ya jiƙan wanda suka rigamu gidan gsky." Da ƙarfi Ɗanzagi yace. "Amin". Su kuwa dattawan ido kawai suka zuba mishi. Shi kuwa Lamiɗo a hankali yaci gaba da cewa. "Ina mai baku haƙuri da kuma umarnin kada kuce zaku ɗauki mataki domin ramuwa." Kamar daga sama sukaji Muryar Bakur yana cewa. "Babu wani sarkin da ya isa ya hanamu ɗaukar fansa sai, Ubangijin daya busa mana, numfarfashi". Da ƙarfi Wani dogarin ya ɗago zabgegiyar bulalarshi ya zabgawa Bukar. Wanda saida yayi tsalle ya kurma ihu. Cikin tsauri Lamiɗo ya ɗagawa duka fadawanshi da hadimanshi da dogara shi hannu alamun kada su sake dukan kowa. Saura su Waziri kuwa duk shiru sukayi, Jabeer kuwa, a hankali yaci gaba da tasbihin da yakeyi, sabida danne abinda yakeji zuciyarshi nayi. Shi kuwa Lamiɗo cikin sanyi ya fara mgna, dan yasan zafin rashin da sukayi ne yasa sukace sai sun rama, a hankali ya kalli fuskokin dattawan da yasan sunje mishi har fadanshi dan neman zaman lfy, cikin kula ya kalli Arɗo Bani tare da cewa. "Arɗo Bani zaku haƙura, hukuma da masarauta ta bi muku kadun cutar damu da akeyi, ko zaku ɗauki makami dan ramawa?". Cikin tarin kufula da harzuƙa da kuma son cinma wata gagarumar manufar da ya daɗe yana fatan ya samu da sai yau, fuska a haɗe yace. "Babu wani wanda zan kuma hana ɗaukan makami, Dan kare kanshi da ramuwar kisar gillan da akeyi mana." Cikin tarin Mamaki da al'ajabi Bappa da sauran dattawan suka buɗe baki tare da kallon Ardo Bani, Jabeer ma idon ya buɗe cikin sanyi yace. "Baba Ardo kayi haƙuri, muyi aiki da al'ƙalami, domin al'ƙalami yafi tokobi, ina nan inata shirin samar da tsaro na musamman kan FULANIN ƙasarmu da nake shugabanta." Cikin nuna tsantsar fushi da son fusata Lamiɗo Arɗo Bani ya dakawa Jabeer tsawa tare da cewa. "Kada rufe min baki, meka sani akan Fulani? Me ruwanka damu? Damuwarmu ta shafeka ne? Ina kake sanda ake kashe mana mata, yara, jikoki, mu kanmu bamu tsiraba, in munje mun kai kukanmu a koremu tamkar karnuka, sabida duk baku san darajar fulani ba." Cikin sauri Ɗanzagi yace. "Hattara dai Ƙaramin Ardo, wannan sarkine na fulɓe masarautar filɓe ce gaba da bayanta". Cikin ɗaga Muryar Ardo Bani yace. "Tafi can baƙin bawa, bawan banza bawan wofi mai ka sani kan fulɓe, meka sani banda bauta da fadanci, masarautar da kuke bautawa bata san menene fulɓe ba". Cikin sauri Waziri ya yunƙura zaiyi mgna, da sauri Lamiɗo ya dakatar dashi, sabida zuwa yanzu zuciyarshi ta fara tafasa, yaya daga kawowa mutane ziyara dan ja-jantawa suke neman tozarta mushi masarauta. Cikin ɓacin rai ya kalli su Bappa daketa kama hannun Arɗo bani daketa fizge-fizge yana kwaza musu baƙar mgna, cikin fushi yace. "Masarautar Joɗa ɗince bata fulani ba?". A harzuƙe Arɗo Bani yace. "Tabbas dan data fulanice, da an bamu kariya da tsaro, da an duba kukanmu, a kashemu a hanamu ɗaukar fansa, an kuma kasa bamu tsaro. Nan da mukaje ina shi jikan naka da yake matsayin Garkuwan Fulani, yana can ƙasashen woje, da iya dukiyar da ake bashi tsaro da kariya shi rai ɗaya ta kai a kula da fulanin daji dubu a kuma basu tsaro. Yau kwana uku da kashe mana mutane sai yau zaku ɗebo manyan riguna kuzo mana da batun wai kada mu rama, sara da suka da yanka mana mutane da akeyi, Kaida kab zuriyar ka da masarauta ka, babu mutun ɗaya da zai iya jurar koda bulalar *(SHAƊI)* ma bare sara da yanka da suka da wuƙa a hakan kuke ganin kanku Fulani". Cikin tarin zafin ƙuna da tafasar zuciya Waziri yace. "To me kuke so muyi muku, tun randa akayi abun munzo bamu sameku ba". A harzuƙe Bukar yace. "Ƙarya ne babu wanda yazo". A hankali Jabeer ya buɗe baki da nufin zaiyi mgna sai yaji Lamiɗo na cewa. "Uhum jinina kuke cewa ba fulaniba, to ko jaririn da aka haifa yau a jikin masarautar Joɗa zai iya jurarar bulalar SHAƊI bare manya ko ɗan baiwa zai iya bare jinina ƴaƴana ko jikokina, ko kun manta masarautar Joɗa ce tushen Shaɗi?". Cikin son harzuƙa Lamiɗo Arɗo Bani yace. "A da can baya ba, yanzu kuma da aka san lusarai ake haifa a masarautar inji an haramta shaɗi a masarautar, yau in kun isa fulani ka bada ɗan ka ko jikanka ayi gasar Shaɗi dashi, in ya iya jurewa, to mun yarda mun gamsu ku fulanine ku masarautar Fulani, in kuwa kun kasa fidda goninku to, ku ba masarauta fulɓe bace." Wani irin karkarwa jikin Lamiɗo ya fara sabida fusata, wai suda masarautarsuce tushen fulɓe a ƙasar, su ake cewa ba fulani ba, har ake kiransu lusarai, Galadima, Waziri, Wambai, Ɗan iya, Ɗan buram, Ɗan Maliki, Sarkin Dawaki. Gaba ɗaya hankalinsu yayi masifar tashi sabida ganin tsananin fushi da tashin hankalin Sarki Lamiɗo. Jamil Jalal Haroon kuwa , hankalinsu na kan Jabeer bisa alamun yana cikin wani hali. Shi kuwa Jabeer bugun da zuciyarshi keyi ne yasa, Hankalinshi tashi, ƙarfin addu'o'in da yakeyi ne, yashi iya fahimtar abinda suke cewa. Kamar daga sama kamar cikin mafarki, sukaji murya Lamiɗo na cewa. "Ga jikana, Jabeer GARKUWAN FULANI, na badashi a matsayin matashi mai yin gasar Shaɗi ku fito da duk gwanin da kukega shine makurar gwayen yankinku. Ayi Shaɗi dashi yadda zaku samu gamsuwar yakai matsayin ya kasance GARKUWAN FULANI". Tunda ya amɓaci sunan Jabeer, Sarkin Fada yayi wani irin murmushi mai cike da jin daɗin alamun burinshi zai cika. Hakama Arɗo bani wani irin asirtaccen murmushi yayi. Jala, Jamil, Haroon, Hashim, Imran, Galadima, kuwa wani irin zazzaro ido sukayi. Cikin tsananin kaɗuwa da firgicin batun Lamiɗo suka zuba mishi ido. Bukar kuwa cikin karaji yace. "Ba'ana Bukar

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});