Chapter 25
Chapter 25
yatsunta biyu a baki, amman ina aman yaƙi zuwa sam. Kawai sai tasa mishi kuka. Cikin tashin hankali yace. "Kiyi haƙuri Mata wlhi bazan taɓa shayar dake wani abu na guba, ko na ƙiba, duk abinda nasan bazaki shashi da sanenki ba bazan taɓa bakishi a ɓoyeba. Ki yarda dani wlh ban shayar dake komaiba". Ina taƙi ta saurareshi sabida tayi matuƙar firgita da tsananin razana da ganin abinda ke cikin kwaryar, cikin sauri yasha gabanta tare da cewa. "Ki gani mana ki duba babu komai a ciki fa madarar shanunce". Tsayuwa tayi tare da zubawa cikin kwaryar ido tas farin nonone kamar ko wanne nono da bashi da gamin komai". Hannutasa ta mutstsuke idanunta tare da kuma sake kallon, cikin tuhuma ta maida idanunta kanshi tana mishi kallo mai cike da tuhuma. A hankali ya sunkuya ya ajiye akwaryar kana ya taso ya fuskanceta da kyau fuska ya haɗe tare da cewa. "Sam bakya min adalci Mata, na lura dake, wani mugun zato da zargina kikeyi. A zatonki wai zan iya cutar da kene? Shin kin mance tun kina ƴar tatsitsiyarki nake sonki ne? Da inada mummunar niya a kanki da na cutar dake tun kina ƙarama. Kullum idanunki na nuna min baki yarda dani ba. Me kike nufi? ko dai wani kikeso ba niba?". Ya ƙarshe tambayar da taune bakinshi kana ya tsareta da idanunshi, da sauri ta sunkuyar da kanta tare da cewa. "A a ni kam babu wanda nakeso." Kanshi ya ɗan rausayar kana ya dawo ya zauna a bakin bukkar tashi, cikin kakkausar murya yace. "Dawo ki zauna". A hankali ta dawo gefen gaban bukkar ta zauna, shi kuwa wani ɗan randar ƙasan dake gefenshi ya buɗe, cikin haɗe fuska ya ɗan kalleta tare da cewa. "To zakiyi sabon Saurayi. Salmanun Arɗo Yabani, zai fara nemanki, kamar yadda munafukan tsoffin rugar nan suke tsarawa, dan ana son rabani dake". Da sauri taketa jujjuya kai tare da cewa. "A a Wallahi ni Yaya Salmanu, ba sona yakeba, ka sani tun ina ƙarama duk abinda ya shafi karatuna shike koya min har dai yasa aka sani. Makaranta kai kuma baka hanaba". Cikin haɗe fuska yace. "Ehh ai nasan ke baki san yana sonkiba, amman na lura shi yana sonki, kuma zanci ubanshi da bulalin shaɗi bashi babu sake kallon duk wani abu da nakeso". Cikin tarin tsoron kada a cutar da Yaya Salmanun tace. "Wallahi ƙarya ake mishi, baice yana sona ba, shi yama tsaneni ne yanzu, dan Allah Ya Ba'ana kada ka yarda da ƙaryar mutane". Kai ya rausayar tare da cewa. "Uhum kinga nan cikin ranɗar nan, to bulaline wanda nake shaɗi dasu, yanzu tsawon shekaru biyu kenan da aka hana shaɗi basu samu wanda suka dakaba, na tsumasu da tarin tsumi mai zafi, wanda muddin na zana jikin mutun dashi sai ya fashe, Kuma gasu a ƙalla sun kai tamanin a cikin randar nan kuma a ƙa'ida da guda goma sha bibbiyu kawai zakayi shaɗi to kinga kenan zan iya shadi da mutun sama da shida dasu basu ƙareba". Kanta taketa jujjuya mishi tare da cewa. "Ya Ba'ana kada ka yarda da sharrin mutane kasanfa Yaya Salmanu shike karantar dani, tun ina ƙarama kuma ko yanzu dana girma tunda shi ya rigada ya gama digiri ɗinshi shike fahimtar dani duk abinda ya shige min duhu, kuma tunda nazo hutun nanma ban haɗu dashiba". A hankali yace. "Eh ai yau kam zaki haɗu dashi". Yunƙura tayi ta tashi tare da cewa. "Uhumm, shike nan ni bari in tafi gida an fara kiran salla." Da sauri ya miƙe ya fito yabi bayanta tare da cemata. "To Mata jirani inzo in rakaki Mana". To kawai tace mishi, a haka suka jero suna tafiya yana gaya mata irin tsumin da yayiwa bulalin nashi. Suna isa dai-dai garken su Shatu, ta ɗan tsaya hango yayunta sun dawo daga kiwo, cikin jin daɗi ta ɗan juyo ta kalleshi tare da cewa. "Bari inje wurinsu Ya Giɗi, in tayasu ɗaure shanun". Murmushi yayi kana yace. "To Mata ki kulan min da kanki kada shanu ya taɓa min ke, dan akan ɗan mai shanun zan rama miki ba kan shanu ba". To tace tare da juyawa ta nufi cikin tsakiyar taron dabobbi su da aƙalla zasu kai guda dubu da yan ɗaruruwa tsakanin shanu, tumaki, awaki, rakuma. Da sassarfa take kutsa tsakiyar dabobbin tana cewa. "Yaya sannunku da dawowa". Da sauri Giɗi da Seyo suka juyo murmushi sukayi tare da cewa. "Yauwa ƴar ƙanwarmu, daga ina kike?". Da ido ta nuna musu Ba'ana dake tsaye can gefe ya zubawa dabbobin nasu idanu tamkar mai ƙidanya su. Gaini ne da Lado suka zuba mishi ido domin gaba ɗaya ya shagala da kallon da yakeyi, har wani ƙan-ƙance idanu yakeyi. Sam bayaji kiran da Babanshi Bukar ke auna mishi. Har saida Giɗi yace. "Heyy Ya ba'ana Ubanka na kiranka". Ya ƙirishe mgnar da bagwariyar hausarsa. Shi kuwa Ba'ana da sauri ya juya ya nufi wurin babanshin da yanzu ya dawo kiwo. Cikin sakalci da gajiya Giɗi ya kalli yayunshi mazan tare da tura baki gaba yace. "Wayyoooooooo Allah bayana zai karye, Ni dai na gaji bazan iya sunkuyon ɗaure shanu ba, ga Shatu zata tayaku". Sai ya kuma kalli yadda duk suka sunkuya sunata ɗaure dabobbin suna ɗan dariyar yadda itama Shatu ta dage tana tayasu. Junainah ce wace dama duk lokacin dawowarsu zata kawo musu sassanyan kindirmo susha tun a nan kafin su koma gida. Da saurinta take ratso cikin shanayen tana cewa. "Ya Giɗi tareni, na gaji ga damunku". Da sauri ya nufi inda take kwaryar ya amsa kana suka dawo gaban bukkokin da nanne ma kwancin masu gadin dabobbin suke. Zama sukayi ludeyayen dumar dake kan fefeyin daya rufe kwaryar ya ɗauke kana ya buɗe kwaryar, ludeyi ɗaya ya sa musu a ciki. Aysha dake kusa da sune ta zauna tare da cewa. "Ya Giɗi kama ka bani". Kai ya gyaɗa mata kana ya cika ludeyin yasha sannan itama ta ɗebo rabin ludeyin tasha, kana ta bawa Junainah itama ta kamfato ta cika ludeyin ko rabinshi bata zuƙaba. Ta miƙawa Ya Seyo dake tsaye gefensu, da murmushi a fuskarshi ya amsa ya sha, sauran nata, Shatu ce ta gyara zamanta ta matso kusa da ɗan uwanta tsokonta Giɗi abokin tsamarta, gyara zamanta tayi kana tace. "Ya Seyo zauna ga fili." To yace kana ya zauna suka fara sha, Lado ne ya kallesu cikin gajiya yace. "To wai mu aka kawowa ko kune?". Shiru babu mai magana sai kamun ludeyin da sukeyi, Gaini ne ya matso gefe shima ya zauna kusa da Junainah yasa hannu ya ɗauki wani ludeyin, nan suka zauna suna sha, ganin hakane, Ya Lado yace. "To ni naci girma". Da sauri Shatu ta mike wurinda ta tashi ta nuna mishi tare da cewa. "A a ya Lado zauna kusha ni na ƙoshi". Murmushi Bappa dake gefensu yayi, wanda yanzu ya iso da jarkan ruwa a hannunshi, Cikin kallon so da tausayin yaran nashi yakeyi, Cikin kula yace. "Sannunku- sannunku da rana, Allah yayi muku al'barka". Amin Amin suka amsa baki ɗayansu, Sai kuma ya kalli Aysha da Junainah yace. "Ayshatu maza kama hannun Junainah ku koma gida, kinji an fara kiran salla". To tace tare da kamo hannun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185