Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 137

Chapter 137

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tayi rolling kanta da mayafin wanda dai dai inda zai zauna a goshin akwai duwatsun. Turare ta fesa, kana cikin sanyi da kasala ta nufi, falo. A falon ta samu, Hibba a kwance tayi shiru. Ganin bata gan fitowarta banema, Yasa ta nufi inda take gefenta ta zauna tare da cewa. "Hibba ɗauko mana awaran". Cikin sanyi Hibba tace. "To". Kana ta miƙe ta nufi falon, jin shiru ba kowa a cikine, yasa ta nufi kitchen a hankali-hankali. Foodflaks ɗin da suka sa awaran da suka soya ta ɗauko. Tana dawowa ta zauna kusa da Shatu tare da cewa. "Gashi". Kai ta gyaɗa mata tare da nuna mata kitchen ɗin ta, tace. "Ɗauko mana plate da roban yajin da Gimbiya Aminatu ta aiko mana. Kizo mana da ruwa". Ba tare da tace komaiba ta juya ta tafi. Bayan ta dawone suka zauna suka fara cin wanda suka zuba. A can falon Hajia Mama kuwa, duk mgnar da Umaymah da Ummi keyi, shiru tayi ta zuba musu ido. cikin sanyi Umaymah tace. "Addana kiyi haƙuri, kin san yaran sai a hankali, dan Allah kada kisa wani abun a ranki wata ran ko ance tayi miki bazatayi ba". Murmushi tayi mai cike da ma'anoni kana tace. "Uhummm ba komai Khadijah jekici gaba da shirin tafiyarki, karki damu kinji". Ido suka zuba mata domin duk basu gamsu da mgnarta ba, to amman ya zasuyi tunda tace ba komai. Haka suka tashi suka dawo falon. Yau su Jalal ma basu zoba. Shi kuwa Sheykh Jabeer, tunda aka idar da sallan azahar ya dawo, ya wuce su Umaymah a falon ba tare da yace musu ƙalaba. koda ya shiga ɗakin ya samu yayi bacci tsakanin azahar da la'asar kamar yadda ya saba, hakan bai samuba. Sabida abubuwan dake ranshi. Bathroom ya shiga ya sakarwa kanshi ruwan sanyi, tare da fara yage towel ɗin dake hannunshi. haka yake tsaye a ƙasan ruwan har saida yaji an kira sallan la'asar. Nanne ya fita ya tafi masallacin. Bayan an idar da sallan ne ya dawo gida. Ganin babu kowa a falon ne yasashi zama, bisa kujerarsa. Ƙafarshi ɗaya ya ɗaura kan ɗaya. A haka su Umaymah suka sameshi. Gefenshi Umaymah ta zauna bisa kujerar dake kusa dashi. Ummi kuwa gabanshi ta zauna bisa carpet. A hankali ya buɗe kwayar idanunshi. Cikin tarin ɓacin rai ya kalli Ummi tare da cewa. "Ummi ina wannan fitsarerren abun da bai san darajar manya ba!?." Cikin sanyi Ummi tace. "Allah ya huci zuciyarka tuba takeyi, in sha Allah bazata sakeba, Hajia Mama da kanta ta yafe mata". Gyara zamanshi yayi tare da cewa. "Ummi ko dai kece kika bata dama da matsayin yiwa Mama hakane?". Cikin sauri tace. "Wanne ni wlh bani bace". Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Umaymah da itama shi take kallo cikin ɓacin rai yace. "Umaymah har akwai wani abun da zai hana mama shigowa sashina? Har yaushe waccar babyn robar ta samu dama da ikon bada izinin shiga da fita cikin sashina da abinda ya shafi rayuwata? Me take nufi dani da iyayen nawa." Kauda ido Umaymah tayi daga kallonshi kana a hankali tace. "Ba isa bane! Akasi aka samu! Nifa inaga har yau Shatu'n bata gama sanin mutanen masarautar Joɗa da kuma dangantakar makusan tankaba, ayi mata haƙuri a mata uzuri a dai wannan karon". Juyowa yayi ya kalli Ummi tare da cewa. "Ummi a kira min waccar abar". Da sauri Ummi ta miƙa tare da cewa to. A falon ta samesu, cikin fuskar da babu yabo babu fallasa ta kalli Shatu dake gefen Hibba da alamun ta cire hannunta a cin awarar kanta ta ɗan kauda tare da cewa. "Kizo Sheykh yana kiranki". Kai ta gyaɗa tare da cewa "Toh". miƙewa tayi taje Dinning area ta wonke hannunta, kana tazo tabi bayan Ummi. A gabanshi Ummi ta zauna ganin haka itama ta zauna a gabanshi. shiru tayi tana kallon yatsun fararen sawunshi. Shi kuwa kanshi na gefe ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace. "Ke ki shiga hankalin ki, kisan abinda kikeyi da wanda zakiyi! Ke har kin kai matakin da isar da zaki ƙaddamar min da iko da isa a cikin gidana? Ko dai ce miki akayi gidan nakine?". Kai ta gyaɗa mishi alamun eh ance mata gidan natane!. Wani irin tsuke fuskarsa yayi tare da ci gaba da mgna dan shi bai ga sanda ta gyaɗa kanba hakama Umaymah, sai Ummi ce kaɗai ta gani, su kuwa sai murmushi sukayi. Cikin kausasa murya yace. "In baki san darajar manya da iyayeba, to ki zama kurma bebiya makauniya a cikin giddannan kafin Ubangiji ya zantar da Hukuncin da ikon zamanki da barinshi dan ikone na Allah bana waniba. Har kin isama Mama tazo ki koreta dan idonki basu da ɗigon kunya. Ko karen gidannan baki da ikon hanashi abu da sakashi bare Mama. ke ta bawa abun ne da zakice bakya so. Kece mai bakin mgn uwar fitsararru ko?". Sam abinda bai saniba zuwa yanzu hankalinta, tunaninta nitsuwarta, jinta, da ganinta duk suna kan farar ƙamarshi ta dama, da zanen maciji ke liƙe kamar macijin na tafiya. Wani irin ba hagun numfashin ta sauƙe a hankali, tare da rufe manyan idanunta da azaban ƙarfi. Sabida gani takeyi Tamkar macicijin ne ma da kanshi ke manne a jikinshi yana kuma motsa ɗan bindinshi dake saman babbar yatsarshi. A hankali ta buɗe idanun kana tabi kan rumfar ƙafar da ido, inda take ganin zanen maciyar yabi. Kasan cewar a zaune yake ya kuma ɗan tattare al'kyabbar jikinshi. Shi yasa tana iya ganin har ƙarshen rumfar tafin ƙafar nashi. Inda iya nan jallabiyar jikinshi ta rufe. da sauri ta ƙara rusunar da kanta wai ko zata ga ci gaban tafiyar macijiyar. Umaymah ce ta ɗan kalleta cikin wata iriyar murya tace. "Ki tashi muje ki bawa Hajia Mama haƙuri, ku nemi yafiyarta ki kuma kiyaye gaba, kinji". Cikin sanyi tace. "Toh". Still Bata miƙeba, cikin ɗan ɗaga murya yace. "Tashi muje yanzu ki bata haƙuri, in ta haƙura kinyi babban Sa'a". cikin sanyin jiki ta miƙe tsaye. Shima miƙewa yayi, Ummi kuwa da sauri ta nufi ɗakin Shatu. Jim kaɗan ta fito da wata kekyawar al'kyabbar matan masarauta ta zuramata. Bayan ta gama gyrashi ne, tasaka hular. Shi yayi gaba ita kuwa. Tabi bayanshi Umaymah da Ummi suka biyo bayanshi. Suna isa bakin mashigar farfajiyar Side ɗin Hajia Mama, ta tsaya gis tare da yin ƙasa da kanta. Ummi ce tace. "Muje mana". Shiru batayi mgna ba, jin hakane yasashi juyowa, karon forko kenan da ya zubawa tsawonta ido. cikin ɓacin rai yace. "Muje ki lashe aman da kikayi da kanki". Cikin sanyin sauti tace. "Ni bazan shigaba". Da mamaki Umaymah tace. "Innalillahi wai ke Ayshs wani irin taurin kaine dake? Menene manufarki?". Murya can ƙasa yana rawa alum zatayi kuka ta kalli Umaymah tace. "Kiyi haƙuri Umaymah ki gafarceni, amman ni bazanje ba, in kuma zanje to ku ku koma, zanje ni ɗaya zan bata haƙuri". Cike da al'ajabi Umaymah tace. "To sabida me bazaki je da muba". Cikin faɗa Sheykh yace. "Sabida muna furci mana, ba zuwa zatayi ba, shiyasa zatace sai dai in ita ɗaya zataje, maza wuce muje a gabana zaki bata haƙuri". Cikin sanyi Umaymah tace. "Jazlaan barta mu tsaya

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});