Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 53

Chapter 53

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ɗago kanta ta kalleshi domin yauce karo na forko rana ta forko a tarihin rayuwarta da taji ya kirata da Shatu, cikin mamaki tace. "Na'am ya Ba'ana". Girgiza kanshi yayi kana ya fara fito da wasu sabbin aska cikin zabirar da yanzu ya jawota, a hankali ya ɗago ya kalleta cikin yaƙini yace. "Shatu, zan faɗa miki abinda, babu wanda ya sani a kaina a duniya, Shatu zan nuna miki abinda duk duniya ban yarda da in nunawa kowaba, sabida ban yarda da kowaba sai ke ɗaya rak Shatu, nasan zuciyarki ciki da woje, ke mai imanice, bazaki taɓa zalumtata ba, bazaki bari a kuma zalum ceniba. Na amince da soyayyarmu, zamu rayu a tare har gaban abadan." Ido kawai ta iya zuba mishi. Ganin Junainah ta iso wurin ne, yasashi jawo akoshin gasassun zabbin gabanshi. Ita kuwa Junainah da sauri ta kuma sa hannu zata jawo akoshin. Kanshi ya jujjuya mata alamun ta bari. Cikin kwaɓe fuska da ɗan karen kwaɗayi da yunwar da takeji yana azalzalar ƴaƴan hanjin cikinta tace. "Yah Ba'ana ka bani mana yunwa nakeji". Cikin sanyi yace. "Bazan bayar ba". Da sauri tasa hannu ta zari akoshin tayi gaba Shatu ce ta fara kiranta tana. "Junnu! Junnu!!! Junnuhhh!". Ina bata kulata bama bare ta juyo. Shi kuwa Ba'ana ajiyan zuciya yayi tare da mgnar zuci. "Uhummm ƙuda garin kwaɗayi kya mutu, kwaɗayinki ne zai karki". Kai ya gyaɗa wa Shstu kana ya juyar da kanshi. Ita kuwa Aysha shiru tayi tabi Junainah da ido. Shi kuwa Ba'ana cikin sanyi ya wore ƙafafuwan sa, takalmin roba na sau ciki wato, tashi kabi shanun dake ƙafarsa ya zare. Sabbin askan ya ɗauka, kana ya fito da wasu ƴan kananun layu guda biyu. cikin yaƙini yace. "Shatu, kinga waɗannan layun?". Kai ta gyaɗa mishi cikin yin kici-kici da fuska. Jinjina mata kai yayi kana yaci gaba da cewa. "Wadannan sune, maƙurar, mgnin kariya da zan saka a jikina, zan sasu a gaban idonki, wannan ƙaramar ita zan saka a dundunyar ƙafar dama, itace kuma layar, ƙarfe, mudin wannan laya tana jikina, to wlh babu wani ƙarfe dake kan doron duniya da zai shiga jikina". Cikin mamaki tace. "Koda bulet ne!?". Kanshi ya gyaɗa mata tare da cewa. "Koda menene, kuwa su wannan sabbin layune, wanda babu makarinsu, sai dai ina na ciresu a jikina, ita wannan da zan saka a ƙafar hagu, layar zanace. Duk sihirin mutun bazai karyashiba, zan iya ɓacewa inje ko ina, makarinta abu ɗaya ne!". A hankali tace. "To menene makarinta?". Cikin sauƙe wani nannauyan numfashi yace. "Idan wata rana dubuna zaicika za'iya kamani, to ammanfa tabbas, zan iya ɓacewa sai dai in ba'a barni na sha ruwaba, amman muddin akabani ruwa nasha zan iya ɓacewa." Da sauri tace. "Ya Ba'ana dubunka ya cika kuma, kamar wani mugu ko maiyin mugun abu". Da sauri ya fizge mgnar da cewa. "Eh to ai yanzu zan fara fataucin nemo. Suya Yaya Giɗi ne, kinga kuwa, sai yadda hali yayi". Ajiyan zuciya ta sauƙe kana tace. "To ita layar ɓatan da ta ƙarfe menene makarinsu?". Kanshi ya ɗan jingina da bakin bukkar ido ya ɗan zuba mata, kana cikin sanyi yace. "Uhum makarinta sai in an samu maza tagwaye, da matar da bata al'ada sunyi tuwon sabon geron da za'a shuka a tsakiyar garken fulanin kana tuwon za'ayishi da garin dakan hannune, kuma maza tagwayen sune zasu tuƙa tuwon kana matar da mijinta ya tara da ita batayi wonkan tsarkiba, ta kwashi tuwon , to su kam in naci, tuwon gaba ɗaya sihirin jikina zai karye, in kuma ba haka sai dai ina an tsaga dundunyar ƙafar tawa an ciresune kafin makami ya iya min illa". Cikin wani irin sanyi tace. "In sha Allah zaka nemosu lfy ka dawo dasu lfy, zanyi ta addu'a Allah ya baiyanasu." Kanshi ya tanƙwasar kana a hankali yace. "Uhum sai daifa Shatu akwai wasu bulalin da aka bani tabbacin zasu worwore duk wani asiri da kafi da nayiwa jikina, Amman duk da haka bazasu worwore waɗannan layunba, sai dai an bani tabbacin, muddinfa aka dakeni da wannan bulalin zan ji azabar dukan, da zai iya ɗauke raina". Cikin mutuwar jiki tace. "Bazama su dakeka ba, Ya Ba'ana". Kanshi ya mirgina kana, yasa hannu ya ɗauki askarnan, kawai sai ya datsata kan dundunyar ƙafar damanshi, Da ƙarfi Shatu tasa salati tare da rufe idonta, gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi murya na rawa tace. "Innalillahi ya Ba'ana zaka kashe kanka". Cikin harshen fillanci yace. "Ai bazanji zafinba Mata, bari yanzu in ɗinkesu, buɗe idonki ki gani." Cike da tsaro tace. "Bazan iyaba, ina tsoro". Jin hakane yasa bai kuma ce ta buɗe idonba, har saida ya gama cusa layun kana yasa ƙayar aduwa ya rinƙa hudawa yana ɗinkawa da zaren, gashin bindin shanu, saida ya gama yace ta buɗe idonta. Cikin tsoron ta zubawa wurin ido, ga jini ya ɓata ko ina, Sai kuma ta ƙurawa ƙafafuwan ido ganin yana shafa musu man shanu sai wani tafasa wurin yakeyi, cikin mintuna uku duk wurin yayi tib-tib kamar ba shiba. Cikin tsoro tace. "Ya Ba'ana, ka dena irin wadannan abubuwa, wallahi shirka ne, tsafine babu kyau! Haramunne." Ganin yadda ya haɗe fuska ne yasa tace. "Kayi haƙuri, shiyasa tun forko ina son ince maka ba kyau bana son kana irin wadannan abubuwan". Murmushi ya ɗanyi kana yace. "In kin sake min mgnar, bulala ɗaya zan ɗauko cikin bulalin shaɗi na, in zaneki da ita sau ɗaya kiji irin zafin da masu gangancin cewa suna sonki, sukeji a jikinsu." Cikin tsoro tace. "Bazan sake bama Ya Ba'ana wadannan, bulalin da kake tsumasu da dafin kunama ai Ni kam na sani bulala ɗaya zakamin zan mutu". Da sauri yace. "Azubillah, Mata kada ki sake cewa zaki mutu, domin duk randa kika mutu nima zan mutu, sai dai batun gsky ko Mata, duk mutumin da kikaga ya iya jure bulalin shaɗi na, har ya kai matakin nasara, to wlh ki sani ki shaida, jarumine, irin jaruman da sunyi ƙaranci a duniya." Hannu tasa ta kange fuska daga wani irin kallo mai cike da so da yake mata, Tabbas Ba'ana ba barbarene, amman yanada wani irin kyau mai ban mmki, a hankali tace. "Ya Ba'ana wai da waye kake kamane?". Cikin murmushin da ya bayyana kyawawan haƙoransa yace. "Ni da kakata Maman babana nake kama, ita kuma ba kanuribace, fulatamare ce ita". Cikin sanyi tace. Murmushi ya ɗanyi kana yace. Cikin sanyi tace. "Haba shiyasa mana kake da kyau sosai". Wani irin kallo ya mata tare da cewa. "Eyeh ashe Ni kekyawan ne Mata, ke dama shine baki taɓa gaya min ba inji daga bakin wacca nafiso fiye da komai a duniya dan inji daɗi, kin bari sai wasu can keta cemin wai ni kekyawan ne". Da sauri ta miƙe tare da cewa. "Sai anjima, Mai kyau ka tashi kaje ka tafi masallacin kaga lokacin sallan jumma'a yazo anata tafiya". Da murmushi ya rakata. Ita kuwa da haka ta tafi gida, sabida tuni wasu masallatan har sun fara huɗuban sallan jumma'a. Tana shiga gida ta samu. Rafi'a, Junainah, Ummiy da Bappa, gaba dayansu a. Cikin Babban birnin Ɓadamaya, a cikin masarautar Joɗa, kuwa. Tuni masallacin Lamiɗo Nuruddee, ya cika yayi maƙil da bani adam tako ina zuwa, akeyi.

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});