Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 60

Chapter 60

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nan gwara ka miƙe kaje ayi da kai tunda kaine sarkin Masarautar Joɗa, Ni nan babu abinda na sani bayan nonon uwata sai al'ƙur'ani da hadisai, sai likitancin da kuka sani na karanta a dole badon raina yasoba, tun ina yaro kullum Ni a cikin sani dole kuke da tsabar rainin hankali, kaje a jibgeka, Ni kuwa nayi al'ƙawarin zan jinyaceka, Lamiɗo Joɗa." Ya ƙarishe mgnar yana amsar wayar da Haroon ke miƙo mishi cikin faɗa yace. "Mitsss wai meye kaketa tura min wannan argar wayar taka ne?". Cikin mamaki Haroon yace. "Kan uba Jabeer wayar tawace ma arga, wayar da kuɗi ta sun kai rabin million To inma argace Umaymah ce bisa layi". Ba tare da ya kara wayar a kunneba yace. "Hello Umaymah". Cikin tausayi Jalal yace. "Hamma Jabeer baka kai wayar kunneba". Lips ɗinsa ya taune tare da cewa. "Au, zama su sani yin abu da yawa". Haroon kuwa mamaki yakeyi domin karo na forko kenan da yaji Jabeer yace Hello a madadin Assalamu alaikum, da shine abinda yakeyi. Ita kuwa Umaymah tana jin ya kara wayar a kunne shi ya kira sunanta cikin rauni. Murya a kausashe tace. "Jabeer". Da mamaki ya amsa dan sama da shekaru goma sha biyu kenan da Jazlaan take kiranshi, cikin sanyi yace. "Na'am Umaymah". Cikin bada umarni tace. "Jabeer ka tashi maza yanzu ka shiga fagen gasar nan ayishi da kai, bana son musu umarnine ba shawara ba". Cikin sauri ya zaro siraran kyawawan idanunshi, Dai-dai lokacin kuma Lamiɗo ya miƙe tsaye cikin tashin hankali da kiɗima da firgici da baƙin cikin dakatar da gasar Shaɗi da akayi a masarautarsu ya sani da anayi da Jabeer bazai ƙalubanceshi ba, cikin sanyi yace. "Zanje za'ayi dani, zan tabbatar da darajar masarautatarmu bata rusheba." Da ido yabi Dottijon kakan nashi wanda a ƙalla ya kai shekaru 91 a duniya. Cikin kauda kai yace. "To Umaymah yadda kikace haka za'ayi amman bari in kira Sheykh Abdulkareem in sanar mishi in ya amince dai zanyi". Da sauri tace. "A a ban yafe ka kirashi ba, wato don kasan in ka kirashi zai kira Sitti da Mai alfarma Jalaluddin da Sarki Nuruddeen ya dakatar da duk abinda za'ayin, tunda na san cemishi zakayi ba addini bane, al'adace, to ban yardaba maza tashi". Ganin Ya Hashim na miƙa masa wayarshi ne yasashi cewa Umaymah. To cikin sanyi. Yana amsa wayar da Ya Hashim ya miƙa mishi yaki Muryar, mahaifinshi cikin sanyi da kuma alamun yana kukane yace. "Jabeer ashe har kayi girman da Lamiɗo zai umarceka da yin abu kaƙi yi mishi mubaya'a, Ashe har na haifi ɗan da zai ja da mahaifina." Cikin sanyi da rauni yake jujjuya kai murya na rawa yake cewa. "A'a Abba, kayi haƙuri kada kayi kuka a kaina." Bai kulashiba yaci gaba da cewa. "Jabeer Ashe zuciyarka har tayi tauri da kangarewar da kanaji kana gani za'a daki mahaifina a gaban idonka, bazaka zame mishi GARKUWA ba, Jabeer wannan shine tukuicin tsantsar son da mahaifina keyi muka, wanda har ya jazamin ƙiyayya a wurin yan uwana sunaga ya fifitaku kan sauran jikokinsa Especially ma kai Jabeer komu daya haifa baya nuna mana son da yake nuna maka, shine zaka bari a dakeshi mutun mai shekaru 91 da ɗaya a duniya kai me shekaru 30 bazaka iya zame mishi GARKUWA ba?". Cikin rauni da ƙunar zuciya, ya miƙe tsaye hannunshi yasa ya kamo na Lamiɗo cikin tarin ƙuna da zafin rai da takaici yace. "Na Amince, zanyi gasar na yarda, ka koma ka zauna". Wani irin farin ciki ne ya ziyarci, zuƙatansu gaba ɗaya, sai dai kowa da irin manufar farin cikinsa. Jin haka yasa fadawan janye labulen da sukayi musu. Shi kuwa Lamiɗo hannunshi yasa ya kamo hannun Jabeer, cikin tsantsar farin ciki da al'fahari da ƙasaita ya fara taku, suna ratsawa cikin taron. Kana fadawansu na biye dasu a baya. Ɗanzagi yana. "Takawarka lfy Sarki mai daraja Lamiɗo ɗan Lamiɗo jikan Joɗa. Gyara kimtsi". A haka har suka isa cikin asalin dandamalin da aka jiƙashi jilak da ruwa, sabida hana ƙura wanzuwa. Gaba ɗaya taron mutanen wurin maza da mata manya da yara, Jabeer suka zubawa ido, sabida duk wanda ya ganshi yaga sahihin Balarabe, mai kamala da nitsuwa, uwa uba kima da haiba, ƙwarjini shi ya cika dukkan idanun magautanshi dake wannan yanki, yayinda masoyanshi ke taraddadin abinda zai faru. A tsakiyar filin suka tsaya, hannunsu dake raƙe dana juna Lamiɗo ya ɗaga tare da fuskantarta gabas, kana ya juya yamma, ya kuma juyawa kudu da Arewa, sannan suka dawo tsakiyar filin, Cikin ƙasaita, yace. "Ga GARKUWAN FULANI, kuma daga Wannan nasarar da zaiyi a gasar nan, Zai tabbatar GARKUWAR Masarautar Joɗa, GARKUWA kuma mai ikon zama inda yaso a cikin fada". Dariya Bukar yayi kana ya ɗaga hannun Ba'ana da yaketa wani abu da ƙirjinshi kamar damisa, Cikin isa da yaƙini da al'fahari yace. "Mu kuma ga namu Garkuwan, da muke da tabbacin bai taɓa gasa ya faɗiba". Sake hannunshi Lamiɗo yayi kana ya juya ya koma ya zauna, cikin rumfar da akayi musu masauƙin. Al'ƙalin gasar ne yazo tsakiyar taro, kamar ko yaushe, hannun Ba'ana ya kamo, ya ɗaga sama, hakan yasa, gaba ɗaya makiɗa da mabusa suka ƙara sautin kiɗe-kiɗen su, wanda Jabeer ke jinsa har tsakiyar kansa, Allah ya sani, baya son hayani koda dai-dai da ƙwayar zarra ne, ga wani masifeffen fargaba da tsinkewar da zuciyarshi keyi, yanaji tamkar yasa hannunshi ya toshe kunnuwanshi. Ɗan wani gajeren tsaki yaja sabida Allah ma ya sani baya son kallo, to kuma yanajin yadda idanun mutane ke yawo a jikinshi. Shi kuwa al'ƙalin gasar, yana sake hannun Ba'ana yazo ya kamo hannun Jabeer, Da sauri ya juyo ya kalleshi sabida kamo hannunshi da yayi sai yaji tamkar hannun jariri ya kamo dam laushi da taushin fatar, hannun sanyi ƙalau, girgiza kanshi yayi cikin tausayawa, sabisa, ya za'ayi ace mai wannan taushin hannun fatarsa ta iya jurar azababbun bulali masu masifar zafi. Ɗaga hannun Jabeer yayi sama. Yana mai nunawa taron mutanen shi a matsayin dashi za'a gwabza. Shi kuwa Sheykh Jabeer, duk abinda akeyi idonshi na cikin ɗan siririn farin galashi mai garai-garai dake liƙe a fuskarshi, Hannunshi kuma riƙe da carɓinshi, kana bakinshi ambaton sunan Allah. Cikin tarin mamaki ya kalli, Al'ƙalin gasar tare dasa hannunshi ya riƙe bakin al'kyabbar jikinshi cikin haɗe fuska yace. "Me hakan!?". Cikin saurin rusunar da kai Al'ƙalin gasar yace. "Za'a cire kayan jikin naka ne!". Cikin tarin mamaki ya zazzaro ido waje, a baiyane yace. "Akan me kenan, suturar da Allah yayi min a matsayin mulmi, in killace kaina, shine zaku yayemin a cikin dubban dubatan mutane?". Cikin dakiya Al'ƙalin ya ɗan kalleshi domin kwarjinin Jabeer ya cika masa fuska cikin sanyi yace. "Allah rene, ƙa'idar gasar ce, ba'ayi da kaya a jikin mutun sai ɗan kamfai, kawai ake bari a jikin mutun". Cikin kufula da harzuƙa yace. "To bada niba, Ni nan Muhammad Jabeer wallahi banyi lalacewar da zan tsaya tsirara a gaban jama'a ba". Yana faɗin haka ya juya a fusashe, zai fita cikin taron. Ganin hakane yasa Galadima, yayi saurin tasowa, kana Ɗan buram na biye dashi a baya, tareshi sukayi tare da kamo hannunshi. Da sauri suka juyo suna. Kallon gungun wasu matasa wanda suka

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});