Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 172

Chapter 172

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Affan dasu Yusuf sunzo, shine Affan yace inzo in tasheka". A hankali ya buɗe idonshi, Yanayin yadda take ɗan marin gefen fuskarshi da hannunta wanda ke ɗaure da agogo. A hankali ya ɗago hannunshi ya ɗan kan hannunta ya kamoshi ya riƙe, cikin tsoro ta fara kiciniyar kwace hannunta, Sai kuma tayi zuru, jin ya ja hannun da ɗan ƙarfi ya kawoshi dai-dai saitin fuskarshi. Idonshi ya zubawa yatsun hannunta da kullum in ya gansu da jan lalle yake tuna mishi baya. Da sauri tace. "Wash Allah na". Jin ya murɗa hannun ya juyo da fuskar agogon inda zai gani. Ƙarfe biyu da miti arba'in da ɗaya. Du-du baccin 40 minutes yayi tazo ta tasheshi. "Harda zuba min maruka". Ya faɗa a ransa. Ita kuwa kan tattausan suman ta ajiye sinsiyar hannunta. tana jin kanta na sara Especially in ta kalli saitin ƙasan gadonshi." A hankali ya sake hannunta kana ya yunƙura ya juya rigingine, ya fuskanci sama, ita kuma tana zaune tana kallon ƙasa hakanne yasa suna fuskantar juna, cikin wani irin yanayi ya zuba mata ido na wasu sakanni. Shigarta tayi masifar mishi kyau. Kodan tasa kalan kayan da yafi sone. Cikin muryar bacci yace. "Shine harda dukana? Meyasa ne ku mutanen garincan kuke son dukan mutun da kallon jikinsa?". Cikin tura baki tace. "Cinyana, nagaji kanka nauyi". Bai janye idonshi a kantaba ya yunƙura ya tashi zaune tare da juyowa ya fuskanceta. tanƙwashe sawunshi yayi tare da cewa. "Me zaki kalla a jikina? Woto Kin zama kamar ɓarauniya ko? Me kike son gani? Wani abu kike sone?". Cikin tura baki tace. "Nifa tada kai a bacci kawai nayi". Hannunshi yasa ya riƙo hannunta, yatsunta ya zubawa ido, cikin wata murya mai sanyi yace. "Masha Allah, kinyi kyau." Wani irin sanyi taji kalmar tashi tasa mata a ranta, ido ta ɗan ɗago ta kalleshi. Shima ita yake kallo, ido ya lumshe jin sautin zazzaƙar muryarta a hankali tace. "Nagode". Tonƙoshe kansa yayi bisa kafaɗa kana hankali ya sake hannun nata. Fuskarta ya kalla tare da taɓe baki yace. "Waya koya miki irin sa lalle Mammeyyyyy nah!? Dan tafi ko wacce mace iya lalle". Cikin sanyi da nazartar yadda ya kira sunan Mammeyyyyy da yadda lokacin ɗaya idonshi suka fara sheƙin tsastsafo da zafafan hawayen da ba zubowa zasuyiba. Cikin son gano meke cikin zuciyarsa tace. "Ummeyy nah ce ta koya min tun ina ƙaramar". Yatsunta ya jujjuya kana ya miƙe tsaye. A hankali ya juya ya nufi bathroom sabida baya son ta hango wutar ƙunar dake ransa. Ita kuma binshi da ido tayi, tare da langoɓar da kanta tana kallon sharabansa da gargasa yayi musu ƙawanya. A haka ta shiga wani nazarin tana mai maimaita sunan da taji ya kira da cikekken so shaƙuwa ƙauna tausayi rauni shogoba *Mammeyyyyy.* Ta maimaita sunan a fili. Shi kuwa Sheykh Jabeer al'wala yayi kana ya fito. Yayi mamakin ganinta a zaune bata fita ba. Hararanta yayi ganin yadda taketa kallonshi. Jallabiyar shi ya zura, kana yasa al'kyabbar, tare da sa Hiraminshi. Sannan ya fesa turare. Duk inda yayi tana binshi da ido. Wayarshi da yafi yawan riƙewa ya ɗauka ya zura a al'jihunsa. Sannan ya nufi bakin ƙofa inda takalminshi suke yana cewa. "Wannan kallon maitan fa". Da sauri ta janye idonta. Cikin daƙilewa yace. "Kada ki cinyeni da ido fa. Bana son kallo, ko kina bina bashine?." a hankali ta miƙe tare da lumshe ido ta biyu bayanshi. Tana gyara mayafinta tare da cewa. "Ni ban kalleka ba". "Uhummm." yace a taƙaice. Kusan a tare suka fito. Yana gaba tana bayanshi, Suka fito tsakiyar falonshi. Tsayawa ya ɗanyi ya gyara masaƙalin Al'kyabbar tashi. Shiyasa ya zama a jere suke tafiya tana gefen damanshi. A haka suka fito cikin corridor'n. Suka doshi Falon cikin kwarjini da dacewa da juna sai ƙamshi da sheƙi zallan kyau sukeyi. Da Sallama a bakinshi suka kutsa kai cikin falon. Wani irin dariyar jin daɗi Affan da suke can Dinning area yayi, suna cin abinci da Ummi ta matsa suci. Wani irin murmushi Yusuf da Aryan ma sukayi tare da miƙewa suka nufi inda uban gidan nasu ke tsaye da kekyawar tauraruwarshi mai haskawa. Affan kuwa wayarshi ya zaro yana kekkebta musu hoto tare da cewa. "Ga amarya, ga ango, suna carabki da zallan kyau da ƙamshi". Murmushi sukayi dukansu, ita kuwa Shatu tana tsaye gefenshi. A haka su Affan suka iso. Suna Isa Affan ya ruggumeshi shima Sheykh ruggumeshi yayi tare da make ƙeyarsa. Da sauri ya janye kanshi tare da cewa. "Wayyo Allah na yanzu Hamma Jabeer na girma harda yaran nawama ban wuce dukaba". Murmushi yayi tare da, Ruggume Yusuf da Aryan Allah ya sani yana masifar son yaran nan har gobe bashi da ɗalibai sama dasu yana sonsu so na musamman, duk sanda ya gansu yakan tuna ƙuruciyarsu tun suna yan shekara goma sha biyar-biyar yake tare dasu shi ya horas dasu. Yana tura irin tarin ƙalubale da suka fuskanta a gasar Polo da kuma irin nasarorin da suka samu Especially Yusuf nashi yana tuna yadda yaran suke sheƙiyanci in sun haɗu, yana jinsu tamkar su Jamil. Cikin murmushin ya shafa kansu tare da cewa. "Sannunku da zuwa". Cikin jin daɗi sukace to. Bisa kujera ya zauna su kuma suka zauna a ƙasa a gabanshi kan carpet. Ita kuwa Shatu a hankali ta juya ta nufi kitchen ganin Ummi ta nufi can. Hibba kuwa na gefensu tana gayawa su Jalal ga Ya Affan fa. Da gefen idonshi ya bita da kallo. Har ta ɓacewa ganinsa, Allah ya sani yana son abu blue baya iya cire idonshi kan abu mai kalar shiyasa yake jin baya gajiya da ganinta, da zai samu kada tayi nesa dashi, dan tayi mishi kyau sosai farar fatarta ta fito fes kamar balarabiya ji yake tamkar ya bita duk inda tayi. Cikin murmushin ya kalli Aryan yace. "Aryan Ina su Yusuf ƙaramin". "Alhamdulillah suna lfy Malam". Kai ya jinjina tare da cewa. "Masha Allah". Sai ya kuma kalli Yusuf yace. "Ina mai sunana baka zomin da shiba". Murmushi Yusuf yayi tare da cewa. "Malam baka tambayi Aryan ƙaramin ba da yakeso ya zama kamarka sai ka tambayi mai sunanka". Dariya sukayi kana yace. "Ayyah my Aryan, sun kusa tafiya ai in sha Allah Jami'atul Madina zaiyi karatunshi". Da sauri suka juyo suka kalli Jalal da Jamil da suka shigo da sauri. Ruggume Affan sukayi suna cewa. "Oyoyo ya Affan". Hannu ya basu suka tafa kamar sa'ao',insa ne su. Cikin dariya yace. "Tun ɗazu nake kiranku bakwa ɗagawa. Nace waɗannan ana can cikin hayani ". Murmushi Jamil yayi tare da miƙawa Yusuf hannu wanda ke cewa. "Oh wato Affan kawai kuka gani mu ko oho ko". Cikin ɗan sakin fuska Jalal yace. "Afwan Hamma Yusuf ya Aunty Zahra da Mama". "Suna lfy. Sun gaidaku". yace tare da bashi hannun. Kana suka gaisa da Aryan. Sannan suka miƙe sukace bari suje wurin Aunty Mami. Cikin dariya Affan yace. "Eh kujema kuzo da ita taga matar babban yaya". Da sauri Jamil yace. "A a ka kawota da kanka dai". Ya ƙarshe mgnar suna fita. Su kuwa cikin yin ƙasa da kai Yusuf yace. "Uhum dama Malam zamu ɗan shiga wasan daba ne in batsala". Murmushi mai faɗin Sheykh yayi tare da cewa.

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});