Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 131

Chapter 131

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

duk sashukan gidajen anje anyi sallama dasu an kuma basu daman shiga. Tafiya kaɗan sukayi daga sashin Gimbiya Aminatu, ta gefen hagunshi, suka ɓullo farfajiyar wani babban part, Jakadiyarsu na gaba suna biye da ita a baya, Umaymah na biye dasu. A hankali suke taku cikin ƙasaita hadimai da fadawa na mara musu baya. Suna shiga ciki, suka samuwa wata dattijuwar tsohuwa mai tarin shekaru. Cikin murmushin da muryar tsufa tace. "Malamai magada annabawa, lallai yau inada babban baƙo da babbar baƙuwa." A hankali suke tafiya har zuwa gabanta, inda take zaune bisa tattausan carpet hadimanta na kewaye da ita. wanda biyu daga cikinsu, suka tashi da sauri suka kawo ababen motsa baki suka jera a gabansu. Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya kalli tsohuwar da take matar ga Galadima. Cikin kula yace. "Barka da safiya Innano". Cike da kula tace. "Barka dai Malam Muhammad, mun samu ƙaruwa ko". Kanshi ya gyaɗa mata a hankali haka yasa duk basu ganiba sai ita da yake gabanta. "Cikin muryar tsufa tace. "Allah ya sanya al'khairi. Ya baku zaman lafiya. Yasa matarkace iya rai da mutuwa. Ya azurtaku da zuriya ɗayyiba." Da Sauri Umaymah ta amsa da Amin Amin hakama sauran baki ɗayansu. Ita kuwa Shatu, cikin saisaita nitsuwarta ta ɗan kalli tsohuwar tare da cewa. "Ina kwana". Murmushi tayi tare da kai hannunta ta kamo hannun Shatu, tafin hannunta ta buɗe ta zuba musu ido, na yan wasu ɗakiƙu kana tace. "Lafiya lau, ya baƙu ta?". A hankali tace. "Alhamdulillah". Jakadiyarsu ce ta ɗan rusuna tare da cewa. "Mun barki lfy". Kai ta gyaɗa kana tayiwa hadimanta umarni su miƙo kyautar da take gadon masarautarsun ce farin gyale ne mai kyau da taushi. Umaymah ce ta amsa ta miƙa hadiman dake bayanta. Kana suka miƙe suka fita. Daga nan sashin wani sashin na kusa dashi suka shiga. Wanda yake sashin ƙannen Lamiɗo ne. Saida suka gama da sashukan manyan masarautar. Kana suka nufi sashin Hajia Mama. Tuni tasan da zuwansu. haka yasa ta kimtsa ta tsara komai na tarban surkar tata. A matsayinta na uwar ango. Har can cikin bedroom Ummi ta wuce, su kuma suna biye da ita a baya. Suna shiga suka sameta, zaune bisa kilishi, Batool na gefenta, wacce son ganin amaryar ne, ya hanata tafiya. Hadimanta kuma na zagaye da ita. Suna shigowa ta tashi zaune daga kishingiɗar da tayi. Cikin tsananin baiyana farin cikin ta, ta nunawa Jabeer kusa da ita. a hankali suka iso suka zauna gabanta. Umaymah kuwa gefenta ta zauna. Ummi ko na bayansu hadiman kuma suna can falo. Hannunta tasa ta kamo hannun Jabeer. Cikin fara'a tace. "Alhamdulillah Muhammad Jabeer, Allah ya sanya al'khairi ya baku zaman lfy". To shifa suna ɗaure mishi kai, da tarin addu'o'insu na al'khairi, shi dai ba sonta yakeba ba kuma zama da ita zaiba, to me zai wahal dashi da zaice Amin Amin. Umaymah da Jakadiyarsu ne suka amsa da Amin Amin kamar dai yadda sukayi a sauran wuraren. Batool ce ta kalli Shatu cikin isa tace. "Amarya ki ɗago kanki mana kinga gaban uwar mijine kike". Duk da taji mgnar Batool sai tayi kamar batajiba, Abubuwan ci da sha dake gabansu ne, Hajia Mama ta jawo wani ɗan ƙaramin tray da cups biyu ke kanshi. Gyara zama tayi da kyau, tana murmushi ta kalli Shatu dake mgna a hankali. "Ina kwana Mama". Cikin kula tace. "Lfy lau ɗiyata ya baƙun ta". Alhamdulillah tace, tare da tsurawa madara da zumar da Hajia Mama ta zuba musu cikin kofu nan ido. a hankali ta ɗan muskuta kaɗan tayi baya, tare da ƙara yin ƙasa da kanta. ita kuwa Hajia Mama, kofin ta ɗauka ta miƙa mata. Tare da cewa. "Gashi ɗiyata amshi kisha." Cikin sanyi murya can ƙasa ta girgiza kanta tare da cewa. "Alhamdulillah". cikin nuna kulawa da so Hajia Mama ta ƙara miƙo mata kofin tare da cewa. "A a ɗiyata, amshi kisha, wannan al'adace ta masarautar Joɗa, dole in marabceki dashi." Kai ta kuma girgiza alamun ya isheta. da sauri Umaymah ta matso kusa da ita tare da cewa. "A a Shatu amshi kisha kinji ko?". Cike da mamaki ta ɗan kalli Umaymah ta gefen idonta. jin Umaymah na ƙoƙarin matso da kofin kusa da itane yasa tayi mgna cikin ɗan ɗaga murya tace. "Bana shan madarar". wani irin kallo mai cike da damuwa Hajia Mama tayi mata tare da cewa. "Subahanallahi, bakya sha, kuma, amai yake sakine? Ƙa'idane da dole kishi". Ta ƙarishe mgnar cikin damuwa. Ita dai Shatu shiru tayi idonta na bisa kofunan madarar. Ummi ce ta matsota tare da cewa. "Shatu amshi kisha koda kurɓa ɗaya ne". Cikin rawan murya tace. "Bana sha". Jin alamun rawan murya irinta an takura mutum ne, yasa duk sukayi cirko-cirko suna kallon Madarar. Zuwa can Hajja Mama ta sauƙe wani bahagon ajiyan zuciya, kana ta ɗauki ɗaya kofin ta miƙa Jabeer tare da cewa. "To gashi kai kam kasha naka". Zamanshi ya ɗan gyara tare dasa hannun damansa ya amshi kofin. Wani irin zaro ido Shatu tayi. Kallon kofin takeyi tamkar zata maida kwayar idanunta cikin kofin. duk jikinta tsuma yakeyi, wani irin masifeffen bugawa ƙirjinta yakeyi da ƙarfi. Shi kuwa Sheykh Jabeer zaune yake riƙe da kofin, ya fuskanci Hajia Mama da kyau. Ita kuwa Hajia Mama hannunta tasa ta kamo ɗaya hannun Jabeer da baya riƙe da kofin. Kana ta miƙowa Shatu hannun alamun ta miƙo mata hannunta. Ƙara runsunar da kanta tayi tamkar bata gane me take nufiba. Cikin murmushin Hajia Mama tace. "Kawo hannunki ko ɗiyata". A hankali ta ƙara maida hannunta baya, dai-dai lokacin kuma Jabeer ya ɗago kofin ya kai saitin bakinshi da niyar zai sha. cikin hikima ta muskuta ta ƙara matsowa jikinshi da sauri ta ɗago hannunta kamar zata miƙawa Hajia Mama hannun. sai kuma ta ɗan kaikaice, ta buge c...! Ƙaƙa tsara ƙaƙa By *GARKUWAR FULANI* Ta bugi kofin madarar, ba zato ba tsammani, Jabeer yaji kofin ya tsumbce mishi. ya faɗi gefenshi. Tass ya fashe madarar ta kwaranye a ƙasa. Cikin sauri da tsuƙe fuskarshi ya juyo ya kalleta. Itama ɗin shi take kallo. Ido cikin ido sukayi da ita a karo na forko a rayuwarsa duk da yasan sun taɓa haɗuwa. Kallon kwaɗayye mai irin bakin Junainah, tayi mishi. Sai kuma ta janye ƙwayar idanunta cikin nashi da sauri. Sabida wani irin kallon da taga yanayi manata. Umaymah da Ummi kuwa, kallon junansu sukayi, cikin yanayin son gane ya akayi kofin ya faɗi dan basuga sanda ta ta ɗan buge mishi hannunta. Hajia Mama kuwa cikin tashin hankali da kiɗima ta kalli Umaymah tare da cewa. "Akwai matsala, ita batasha, shi nashi ya kwaɓe." Sai kuma ta maida dubanta ga Shatu cikin alamun damuwa tace kawo hannunki na dama." Still maida hannun nata tayi baya, ba tare da tace komaiba. Ummi ce ta ɗanyi ƙasa da murya tare da cewa. "Miƙa mata hannunki ku gaisa". Murya can ƙasa tace. "Yana ciwo". Ta ƙarishe mgnar da jin haushin kanta da ƙaryar da suka satayi. Batool ce ta kalleta sama da ƙasa kana cikin gyatsine tace. "Umaymah ai wannan ba irin matar Sheykh bac." Sai kuma ta haɗiye ragowar mgnar dan ganin wani irin kallon daya watsa mata na alamun. Ki kama kanki da kiran

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});