Chapter 72
Chapter 72
bawa fulanin Rugar Kikan tsaro gaggawa, shima yana nan tafe da rundunar sa. Ya bashi umarni mai ƙarfi ya ƙara da cewa, muddin yazo ya samu ba dai-dai ba ta ɓanƙaren tsaro, to akan aikinshi. Wannan abun na umarni daga samane, yasa mugun kafurin nan. Firgita gudun rasa aikinsa, da tonuwar asirinsu da gudun kada a cireshi asa musulmi a kujerarsa, yasa cikin gaggawa ya haɗa kan rundunar sa ya nufi. Cikin Rugar Kikan. Junainah kuwa wani irin karkarwa takeyi wanda, tuni fitsari ke tsiyaya yana bin sawunta. Wani irin ihu tayi, ganin wani kafurin ya kaiwa Junaidun sara a bayanshi. Wani irin juyi Junaidun yayi ya farma kafurin da da wuƙarsa dan kare kansa da Junainah. Duk da su biyar suka zagayesu, basuyi nasara a kanshiba, yana kare kanshi da Junainah, har saida suka tsira daga waɗannan. Sai kuma wasu, mutun takwas suka cimmusu. Da ƙarfi suka banƙaren Junaidun, suka fara kiciniyar zare Junainah da ya ruggumeta da azaban ƙarfi da yayi. Wani irin ihu yasa jin an caka mishi. Wuka a gadon baya. Still bai saketaba, sai yaƙin kareta da ya farayi, da iya ƙarfinshi. Ita kuwa Junainah ganin an caka mishi wuƙane yasa ta sume. Dai-dai lokacin kuma rundunar yan sandan suka iso. Kamar bazasu guduba, dan sun san da bakin hukumar sukeyin aikin, to sai dai ganin musulman cikin yan sandan suna sakin harbine yasa. Suka ari ta kare. Daga nan suka rinƙa gudu sunayiwa yan uwansu fito alamun su gudu. Cikin ƙanƙanin lokaci duk suka gudu. Su kuwa yan sandan, suka shiga cikin Rugar Kikan ɗin. Hankalin musulman cikinsu yayi masifar tashi ganin irin kisan gillar da akayiwa bayin Allah'n nan, kisa na rashin imani. Nan take suka kira motocin asibiti. Suka rinƙa jidon masu sauran rai suna sawa a motar ambulance suna kai cikin Genaral Hospital Numan. Kana suna harhaɗa gawakin kuma a tsakiyar garin. Cikin mintuna talatin rundunar A.S.P ta iso. Tare da yan jaridu. Su Bappa kuwa. Koda suka gama tattaunawa da Maimartaba, sai ya umarci Waziri daya hanasu tafiya a bisa adalcinsa. Yace su tsaya suci abincin rana, kana suyi sallan azahar kafin su tafi. To haka yasa suka zauna. Waziri yasa akayi musu duk ihsanin da Maimartaba ya bada umarnin ayi musu. Sukaci abinci sukasha, Sannan sukayi sallan azahar. Daga nan aka sallesu suka tafi. Tuni cikin gari kuwa gidajen rediyo sun ɗauka, batun faɗan FULANI makiyaya da Ɓachamawa manoma, wanda akaso a juya rahoton da cewa makiyayan ne sukayiwa manomanne ɓarna. Bayan. Tafiyan su Bappa da kamar 30 minutes ne. Labari abinda ya faru ya riski Maimartaba. Nan take yasa Waziri da Galadima da hadimai mutun ashirin suka nufi cikin Numan dan suje su tabbar da abinda akace ɗin. Su Bappa kuwa, sam basuji lbrinba saida suka isa cikin Numan. Ganin garin a hargitse ne yasa Arɗo Bani ya kalli Bappa da Alhaji Haro da suke gefenshi cikin mmki yace. "Lafiya kuwa? Meke faruwane a garin nan?". Cikin kaɗuwa suka haɗa baki wurin cewa. "Allahu alamu". Drivern nasune, ya kallesu a tsorace yace. "Anya kuwa yau ba faɗa akeyiba a garin nan ba". "Kai ba lfy ba kam!". Cewar Alhaji Umaru Shi kuwa Drivern, bakin titi ya ɗan gangara ya tsaya, ya tambayi wasu yan agaji daketa. Shiga cikin wani babban Pharmacy da alamun magunguna suke saya, koda suka mishi bayanin abinda ya faru. Jiki na rawa yazo ya sanarwa su Arɗo Bani. Lokaci ɗaya hankalinsu. Yayi masifar tashi. Nan sukace ya wuce dasu. Asibitin. Koda sukaje hanasu shiga akayi. Hakane yasa, sukace to ya wuce dasu Rugarsu. Suga ko canma akwai uban da zai hanasu zuwa. Nan ya nufi cikin Rugar tasu dasu. Su Wazirima tuni, sun iso. A can cikin masarautar kuwa, Sosai hankalin Maimartaba ya tashi. A can ƙasa mai tsarki kuwa. Sitti ce tsaye gefen Sheykh lokacin da yake mgna da kakanshi. Zama tayi gefenshi, tare da tsareshi da ido. Baibi ta kantaba, ya ci gaba da sarrafa wayarshi. Wata number, ya dannawa kira kana ya kara wayar a kunne, jim kaɗan aka amsa kiran. Bayan sun gaisane, ya ɗan gyara zamanshi tare da ɗan kallon Sitti ta gefen ido Cikin harshen fillanci yace. "A haɗa min zama da Ƙungiyar TABITAL POOLAKU". Sai kuma ya ɗan shaƙi sanyi da ƙamshin ɗauki ido ya lumshe cikin kamala da nitsuwa yaci gaba da cewa. "A kira min Ƙungiyar MIYETTI ALLAH, da gaggawa, ina da zama dasu. Ranar Jumma'a in sha Allah". Hannun damanshi yasa yana shafa sajenshi, tare da sauraron mgmar da. Arɗon Arɗaɓe keyi. "Ranar jumma'a kuma? Ka dawone?". A takaice yace. "Zan dawo!". Cikin gamsuwa da mgnarshi sanin in yace eh, eh ɗince in kuma yace a a, tofa a ance. Muddin kuma yace zaiyi abu to da izinin ubangiji sai yayi shi. Cikin jin daɗi adalci da kulawarshi ga shugabanci da aka bashi yace. "To Allah ya dawo da kai lfy". Yatsun ƙafarshi ya sunkuyar saida suka ɗan bada sautin ƙaras, kana yace. "Amin ya rabbil izzati". Daga nan ya katse kiran. Kamar bata wurin haka ya jawo System ɗinshi ya fara daddannata. Kamar babu kowa kusa dashi haka yaci gaba da aikinshi. A system, ita kuwa Sitti ido ta zuba mishi. Tana kallon yatsun hannunshi da yaketa sassarfa, tamkar shiya haaliccin na'ura. Yanajin idanunta na yawo a sasan jikinshi, hakan yasa, ya ɗan juya kwayar idanunshi, ya ɗan kalleta ta wutsiyar idonshi, murya can ƙasa yace. "Sitti wannan kallonfa, kin san bana son kallo kam ko?". Ajiyar zuciya ta ajiye, kana ta ɗan janye Hiramin kanshi, da sauri yasa hannunshin ya kame hiramin cikin kwaɓe fuska yace. "Sitti ya haka, kinsan Haroon ba kan gadone dashiba, yanzu zai iya shigowa da yaran nan". Ido ta ɗan rufe kana tace. "To su yaran mayune, ko yaushe kana rufe da Al'kyebba da hirami, kasha iska mana, ko nauyi basa makane?". Kanshi ya ɗan juya kana a hankali yaci gaba da aikinshi tare da cewa. "Suturce jiki shine, zaiyiwa ɗan adam nauyi, Sitti, sannan ya za'ayi in bari ko wani Tom and Jerry su kallarmin suman kai, ai shi hula da hirami kamar ɗan kwaline wa mace". Sai ya kuma ɗan juyowa ya kalleta tare da cewa. "Yauwa Sitti, bana son ana sawa Jazrah tana samin abinci, bana so, sai a turrota tazo taita kare min kallo". Fuskarta ta haɗe kana tace. "To yayi kyau, kawai in baka sonta, ka fito fili ka faɗa mana". Kauda mgnar yayi tare da cewa. Ki shirya in sha Allah zuwa ran jumma'a ina son in kasance cikin ƙasata ta haihuwa a jiharmu a kuma masarautarmu". Haroon da yanzu ya shigone ya ɗan kalli ɗan uwan nashi, cikin mmki yace. "Sheykh kawai dan ana mgnar baka matar aure shine kake shirin guduwa zaka bar ƙasar ba?". Bai kalli Haroon ba kuma baice, komai ba, sai rufe system ɗinshi yayi kana ya miƙe a hankali, gaban drower'n gadon ya nufa, buɗewa yayi, wasu E Passport guda biyu ya ɗauko, Kana ya dawo gaban Haroon. Hannun shi ya kamo ya danƙa mishi su, kana yace. "Gasu, ina son zamu bar ƙasar nan ranar al'hamis." Da sauri Sitti tace. "Kaida waye zaku tafi". Ba tare daya kalletaba yace. "Da ke". Kai ta kuma juyawa tace. "A a kam ka koma kai ɗaya, ni
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185