Chapter 54
Chapter 54
Masallacin ya cika tab tamkar zai fashe, shiru kakeji babu wani amon sautin ɗan adam dake tashi, sai sautin muryarsa. Yana tsayene cas kan ƙafafunshi, Wata dan datsetsiyar, shaddar Super Nour ce a jikinshi wacce take Brown color a ƙalla kuɗinta zai kai dubu ɗari da ashirin, shaddar irin mai mai ɗinnane, Yayi kauri cikin kayan ko dan yanayin suturar da ya sakane, boxes ce fara ƙal yasa a ciki, sai snglet itama fara ƙal, kana sai Rigar half jomfar yaddan dake jikinshi sai wonɗota, wanda sunyi cib-cib da madaidaicin jikinsa, Kana sai watta tattausar doguwar al'kyabbar sa, Golding color, sai wani irin sheƙi takeyi, sai hirami fari daja irin mai ɗigo-ɗigo nan, yayi masa sakin manyan Dattawan bai lonƙosashi, ya barshi a zube bisa kafaɗunshi, sai ta gaban goshinsa da ya ɗan matseshi ya bada ɗan tsini dai-dai kan karan hancinsa, Sai baƙin zagayen daya ɗaura bisa kam hiramin. Kana sai wasu takalman shi dake can bakin ƙofar shuga masallacin ta ƙofar liman, takalman irin na sarauta ne half cover, wanda suma fari da ɗigon jane. Yayi wani irin kyau mai ɗaukar hankali haibarsa da kimarsa da dottakunsa sunyiwa fuskarshi ƙawanya, sajen nan nashi yayi lib-lib tamkar anayi wa koren ciyawa bayi, sai wani irin sassanyan ƙamshin turaren OudKareem ɗin sa, dake tashi a jikinsa. Muryarsace ta cika ko ina na yankin. Shiru mutanen wurin sukayi kowa na jin, wa'azin yana ratsasu. Yana Hudbane akan, wuraren da ya dace namiji ya gani a jikin matar da yake neman aurenta, yana kan hankali, bisa wuce gona da iri da mafiya matasan yanzu keyi, a kan wannan dama da Allah ya basu. Gyara tsayuwarshi yayi, tare da haɗe hannayenshi wuri ɗaya, ya haɗe bakin al'kyabbar jikinshin. Cikin tattausan lafazi mai ratsa kunne da zuciyar duk mai sauraro da imani yaci gaba da cewa. "Aure wata muhimmiyar hanya ce, wanda idan aka ƙullashi zai bawa ma'auta daman saduwa, tsakaninsu, ba tare da wata ƙyama ba, kuma ta hakane ma'autan zasu zama sutura ga junansu. Kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya faɗa, a Suratul Baƙara aya ta , 187:- (HUNNA LIBASUN-LAKUM WA, ANTUM LIBASUN-LAKUM). Ma'ana su mata suturane gareku maza, sannan ku maza suturane garesu (Su Matan)." Gyara zaman al'kyabbar sa yayi tare da kallon tarin dubban al'ummar Annabi dake zaune gabansa, hankalin da nitsuwar kowa na kanshi. Sai ɗan haskem cameras da yake gilmawa ta kanshi da sauran na kusa dashi, shaidar ana naɗar sautin muryarsa nayin huɗuban. Cikin nitsuwa yaci gaba da cewa. "Saboda haka, ya zama dole mutun, ya nitsu ya maida hankali ya zaɓi abokiyar zama ta gari da zata zame mishi sutura ya zame mata sutura, wajibine kuma kayiwa kanka da jikinta iyaka har sai an biya sadaki, an kuma ɗaura aure, shaidu sun shaida sannan zaka samu nitsuwa da ita. Domin shi aure, yana samar da nitsuwa tsakanin ma'auranta. Ɗan Adam bazai samu cikakkiyar nitsuwa a gidansa ba sai in har yanada mata, wacca ya aura. Domin zata ɗebe mishi kewa, ta sa shi ya samu nitsuwar hankalinshi. Saboda zamansu tare, a ƙarƙashin inuwar aure zatayi mishi maganin kaɗaci. Kamar yadda Allah, (A.A.W) ya faɗi a Suratul Rum aya ta 21:- (WA MIN AYATIHI AN KHALAKA LAKUM MIN ANFUSAKUM AZWAJAN LITASKUNUW ILAIHA WA JA'ALA BAINAKUM, MA WADATAN WA RAHMA INNA FII ZALIKA LA AAYAATIN LIKAUMIN YATAFAKKARUN). Yana daga cikin ayoyin da Allah mai girma ya halitta mana mataye daga kawunan mu. (Mataye da muke aure da su) domin su sami nitsuwa junanku, sannan kuma ya sa muku soyayya a tsakanin ku tare da Rahma da tausayawa juna. Lallai a cikin wannan al'amari akwai ayoyi abin lura ga jama'a'an da suke masu tunani". Gaba ɗaya taron al'ummar babu, hayaniya ko motsi shiru kakeji, Baba Nasiru kuwa, yana dai zaune ne cikin sahun da masallacin amman ji yake tamkar ya shaƙo wuyan Jabeer sai ya kaishi ƙiyama, Baba Bashiru ne dake gefenshi, ya ɗan kalleshi tare da yin ƙasa da murya yace. "Ya Nasiru ka nitsu mana ka koyi danne abinda ke ranka". Cikin tarin baƙin ciki yace. "Haba Bashiru ya zanyi in iya danne abinda ke raina, bayan da kai sani dama duk sauran yan uwanmu, mahaifinmu ko sarautar sarkin ƙofa bai bamuba, Tunda ya bawa Ya Muhammad, Galadima, yana rasuwa, madadin a maida sarautar Galadima kaina, ko kan Hashim tunda shi ubanshine Galadima, sai ya ɗauki wannan sarautar ya bawa, Jafar shi ɗan rashin adalci." Murmushi Baba Bashiru yayi tare da cewa. "To ai kuma dai gashi ya haukace ko? Ina dai yanzu sarautar tafi ƙarfinsa, dole dai ya barta". Cikin fusata Baba Nasiru yace. "To ɗaya barta ya haukace ɗin ma, ya maidota ga ƴan ɗakinmu ne, inji, wancan tsohon ya bawa, waishi ya bawa ƙaninshi, ai shima ɗan tsohon sarkine Sannan kana ganin yadda ya kuma ɗaukar sarautar GARKUWA ya bawa Jabeer, sannan babban tashin hankalin kanaga yau tare suka fito ɗakin labbare dashi wannan munafikin yaro, waishi Sheykh ɗan iska anyi asiri anyi tsafi duk baya kamashi yadda mukeso". Barrister Kamal ne dake gefensu, yayi ɗan wani guntun tsaki cikin tsuke fuskarsa, da jin haushin yan uwan nashi yace. "Ya Nasiru kufa, ji tsoron Allah, ku tuna, cikin Masallaci kuke, kuma ba kyau liman na huɗuba ana. Surutu." Wani irin mugun kallo Baba Bashiru ya watsa mishi tare da cewa. "To ɗan masu matacciyar zuciya, wa'azin da yakeyi ai tun kan a haifi uwarshi mun sani". A kufule Barrister Kamal yace. "Ƙaryane, da kun san abunda ya sani wala Allah da zuciyarku ta tsarkaka". Shiru yayi tare da fuskantarta Inda limamin take jin yana cewa. "Halaccin kallon matar da mutun yakeso ya aura. Haƙiƙa munsan matarka abokiyar rayuwarka ce. Kuma gonarka ce da zakayi shuka a cikinta, sannan kuma gareta zaka samu konciyar hankali. Kuma shi manufar yin aure ya hana kallon wata ko wasu matan wanda ba nakaba da dai makamantansu Irin hakan. IN KUWA HAKANE TO LALLAI AKWAI BUƘATAR SAI MUTUN YA ƊARJE! YA ZAƁA. Haka kuwa baya yiwuwa sai ka kalleta sosai da sosai. Saboda mahimmancin haka nema shariyar musulunci ta yardar maka da ka kalli wacce kakeso zaka aura da kyau. Don ka tabbatar da wancan abubuwan da aka ambata a sama. Kuma wannan dama da Shari'a ta bada ta bada shine, a matsayin halasci na wurin mafi yawan malamai, kuma wannan Halascin da akace halasne ya haɗa da cewa. Shin ta yarda ka kalleta, ko bata yardaba, halasne in dai ka kalleta. Kuma wannan hukuncin haka yake a wojen mafiya yawan malamai, sai dai Malikiya, sunce shi hukuncin Halascin ya dogara ne, in ta bashi izinin amma in bata bashi izinin ba to bai halasta ba. Haka kuma shi wannan hukuncin halascin an samo shine daga, hadisin Abu Huraira (Allah ya ƙara masa yarda) yace, wani mutun ya nemi auren wata mata, ƴar Madina, sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa: "Shin ka kalleta kuwa?". Sai mutumin yace, wa Manzon Allah (S.A.W) "A'a ban kalleta ba". Sai Manzon Allah (S.A.W) yace. "Tafi ka kalleta, domin mutanen Madina sunada wata illa a idanunsu." A wata ruwayar kuma da Abu Dauda ya ruwaito. Daga Jabir Bin Abdullahi cewa: Lallai Manzon Allah (S.A.W) yace. "Idan ɗayanku zai nemi aure to idan ya sami ikon kallonta wato kallon abin da zai burgeshi zuwa ga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185