Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 78

Chapter 78

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tare da jan dogon tsakin da yasa duk suka meda idonsu kanshi. Cikin kula Habibullah yace. "Lfy dai Nasiru?." Wani irin kallo mara daɗin gani ya watsa mishi tare da cewa. "Yes lfy lau, sai dai mu nan duk muna da aiki, ba zauna gari banza, irinka bane, kowa yanada hidimar yi gashi har yanzu, Lamiɗo bai fitoba". Murmushi yayi ba tare da yaji ciwon abinda ya gaya mishibs, a hankali yace. "To Nasiru, ai duk saurinka kayi haƙuri dai ya fito, kaga lfyarsa yaga taka, tunda shi bai gajiya da bincikar lfyarmuba, ai muku wa bazamu gazaba. Domin abune mai wucewa". Wani irin kallo mai cike da tsana da tsoggoma ya mishi tare da kauda kanshi. Basiru ne yayi dariya alamar jin daɗin kallon da ɗan uwanshi yayiwa Babban yayansu da suke ƴan uba. shi kuwa Habibullah Abbansu Sheykh, kauda kai yayi kar bai ganiba. Kusan a tare suka miƙe gaba ɗayansu, tare da haɗa baki wurin cewa. "Barka da fitowa, Mai alfarma Lamiɗon Joɗa." Murmushi yayi tare da kallon ƴaƴan nashi ɗaya bayan ɗaya, a hankali ya ƙarasa fitowa, hannunshi sarƙafe da hannun Jabeer. Wanda baiyanarsa yasa, gaba ɗaya suka zazzaro ido. Cikin tarin mamaki, al'ajabi, firgici, kaɗuwa, gamida tsayawar idanunsu kan ɗan babban yayan nasu, cikin wani irin daskarewa, suka juyo suka fuskaci, junansu wannan ya kalli Wannan wannan ya kalli wancan. Murya a daburce, Nasiru ya nuna Jabeer dake tsaye, cikin wani masifeffen al'kyabbar mai masifar kyau da zadan gaske, cikin ƙafewan yawun baki yace. "Ka gafarceni Lamiɗo, me idonuna ke gani, daga ina ka fito da Jabeer? Me kayi dashi? Meye ma'anar hakan? Mu duk ƴaƴan ka bamu kai ka shiga damu ba sai shi?". Cikin tsare fuska irin ta manyan sarakai dattawan, ya zubawa, Nasiru idanu, wanda dole tasa ya hadiye rahowar maganar tasa. Habibullah kuwa, wani irin rawa da karkarwa jikinsa ya fara. Wani masifeffen tsoro da fargabane ya rufeshi akan ɗan nashi, koda dai baya jinsu a ranshi kamar sauran ƴaƴanshi, hakan bai hanashi tsoro da fargabar abinda zai cutar dasuba. Barrister Kamal kuwa. Wata irinyar madifeffiyar zuface ta keto mishi daga saman kanshi har tsakiyar tafin sawunshi. Lokaci ɗaya yaji wani irin abu ya saki ƙahon zuciyarshi, Maƙoƙoronshi ya bushe ƙamas, duhun daya rufe mishi idone yasashi komawa zaune. Dr Aliyu kuwa, wani irin murmushi yakeyi yana kallon ɗan babban wansun. Shi kuwa Lamiɗo hannun Jabeer ya kuma ja, wanda yake motsa laɓɓansa a hankali yana tasbihi kamar yadda ya saba. Zama yayi kujerarsa ta musamman, kana Jabeer kuwa ya zauna gabanshi. Cikin tattaro yawun baki Barrister Kamal yace. "Barka da safiya. Sarkin Joɗo. Sai ya kuma danne tarin baƙin cikinsa yayi mishi rumfa da fuskarsa ta zahiri kana ya kalli Jabeer da ya ɗan sunkuyar da kanshi tare da gaidashi. Cikin dakiya yace. "Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Joɗa. Yaushe a gari". Kanshi ya ɗan kauda tare da cewa. "Daren jiya". Nasiru ne ya katsesu da cewa. "Lamiɗo, ɗakin sarautar sarakunan Joɗa kuma ya zama kowa zai iya shigane?". Bai kulashi ba, har saida suka gaisa gaba ɗayansu, kana, ya fuskancesu, duka cikin hikima da, kaifin basira yace. "Rigar sarautarsu ta GARKUWAN FULANI, na bashi. Sabida akwai tafiyar gaggawa da zamuyi zuwa, Rugar Bani, da ƙaɓilun wurin suka far musu da kisa." Kai suka gyaɗa alamun gamsuwa, kana duk, ya sallamesu. Duk suka fita kowa da abinda ke cikin ransa, da zuciyarsa. Bayan fitansu ne ya kalli Jabeer cikin, tarin kula yace. "Kaje ka shirya kazo mu tafi". Kanshi ya kuma rusunarwa cikin ladab yace. "Allah saine, mu bari sai bayan sallan, jumma'a ina munyi jam'i anan, mu tafi gudun kada muje bamu dawoba kafin lokacin sallan." Gyara zamanshi yayi tare da gyaɗa kai kana yace. "Haƙƙun kayi, gsky to mu bari sai an sauƙo mutafi, in yaso muyi sallan la'asar a can." Da Wannan shawarar suka bari sai bayan sallan, azahar ɗin su tafi. Sun daɗe suna tattaunawa kafin, ya sallameshi ya tafi, shi kuma ya nufi fada. A falonshi kuwa, yana shigowa duk suka zuba mishi ido, da mamaki cikin zaƙuwa Jamil yace. "Hamma Jabeer wai ta ina kabi ka fitane? Duk bamuga fitankaba". Kanshi ya mirgina, alamun gajiya, kana a fakaice ya kallesu baki ɗayansu, tare da cewa. "Sama". Murmushi sukayi baki ɗayansu, sabida fahimtar amsar daya basu, na nuni basuga sanda ya fita bane. Bisa wata tattausar doguwar kujera ya zauna. Kana ya fuskanci ƙannen nashi da kyau. Jalal ne ya ɗan sunkuyar da kanshi, ganin yadda Hammanshi ya zuba mishi ido, Jamil kuwa, kanshi ya ɗan rausayar tare da katse wayar da yakeyi, ya fuskanci ɗan uwan nasu, Cikin yin fiki-fiki da idanu yace. "Barka da safiya Hamma Jabeer, ya hanya?". Alhamdulillah, yace mushi a taƙaice, kana ya ɗan gyara, hiramin dake bisa kafaɗunshi. Jalal ne ya ɗanyi baya tare da lumshe idonshi cikin saisaita muryar da indai da Hammanshi zaiyi mgna to sai ya nitsu ya gyarata, Domin yakanji yanada rauni duk sanda yake gaban Hammanshi, yana ji tamkar a gaban mahaifinshi yake. Cikin sanyi yace. "Ina kwana? Hamma Jabeer, ka dawo lfy t yasu Sitti?". Ido ya ɗan kauda kana yace . "Alhamdulillah, Jalal ya jikin Ya Jafar?". Kanshi ya ɗan jujjuya kana a hankali yace. "Kalmace dai ta musulmi, koda cuta babu sauƙi ya zame mana ɗa'a muce, da sauƙin, amman a zahirin gsky ciwon Ya Jafar babu sauƙin, komai yaci tura, abubuwan sun yawaita". Ya ƙarishe mgnar tamkar zaiyi kuka, ganin hakane yasa Jabeer ɗan kauda kanshi, Allah yasani, baya son ganin ƙunci ko baƙinci ko wata damu a fuskarsu, sabida ya ɗauka cewa Allah ya barshi da rai da lfy ne a tsakiyarsu, su da akewa kallon marasa lfy ya zame musu Garkuwa. A hankali ya miƙe cikin kula ya kallesu, murya a ɗan macce yace. "Kuzu kuci abinci". To sukace baki ɗayansu, kana duk suka nufi, dinning table ɗin. Wanda yake cike da abinci kala-kala. Juwairiyya ce ta sakawa kowa abinda yake buƙatar ci, Shi kuwa Sheykh sai jujjuya mata kai yayi alamar babu abinda zaici. Ya dai zauna yana kallonsu, Ummi kuwa, tana gefenshi. Kanshi ya ɗan juya ya kalli Haroon dake shan tea kuma still wayarshi na kunne yana, mgna da Jannart, ɗan gajeren tsaki Jabeer ya ja, jin Haroon na cewa. "Ina yin breakfast ne, ke me kikeyi? Bacci? Ko kwaliya? Ko kallo?". hannunshi yasa ya zare wayar kana ya katse kiran tare da mishi nuni yaci abinci kafin ya tsaya yin waya. Cikin haɗe fuska Haroon yace. "Ka ganka ko? Ni shiyasa har tsoron zama kusa da kai nakeyi, sabida tsarabe-tsarabenka nada yawa, yanzu zaka fara jawowa mutum aya da hadisai, kana wani, abu kaza ba laduban kaza bane, in an jika kayi doguwar mgn to an sosa maka wuri biyu, ko ayar Allah, ko wannan mulkin da kake cewa an liƙa maka jaraba". Jamil ne yayi ƴar dariya tare da cewa. "Mulkin nema jaraba a wurin shi ko? Gacan wasu na neman, zaunece sabida Garkuwan da aka bashi". Jalal ne ya ɗan tsuke fuskarsa tare da cewa. "Ni kaina Wannan GARKUWAN bai wani burgeniba, sabida baya cikin, masu iya gadar mulki, sabida shi ai ba jikan sarki ta wurin ƴa mace bane, jikanshi nefa ta wurin ɗa namiji ta yaya zai bashi Garkuwa?". Ummi ce

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});