Chapter 183
Chapter 183
mai daɗin ji yake fiddawa, ɗan farin siririn Glass irin na manyan Doctors ya manna a fuskarshi kana ya fito. A falonshi ya sameta, tana jera mishi breakfast. Ganin zai wucene ta ɗan biyoshi a hankali ya zama suna tafe a jere. Cikin kallon suman ƙeyarshi tace. "You are breakfast is ready". Bai kulata ba yaci gaba da tafiya. Ita kuma ƙeyanshi ta mannawa harara. A haka suka fito. Ya sallami Ummi da Jamil da tunda suka karya bai tafiba. Da sauri Jamil yabi bayanshi yana cewa. "Uhum Dakta sai yaushe zaka dawo ne?". Juyowa yayi ya kalli Jamil sai kuma yace. "Kanada matsala ne?". Da sauri ya jujjuya kanshi tare da cewa. "No. I'm very fine". yayi mgnar yana jijjiga jikinsa. Kai ya kaɗa ya juya zai fita, Da sauri Jamil ya kuma tambayarsa. "Dakta yaushe zai dawone". Cikin tsuke fuskarsa yace. "Ban sani ba". Daga nan ya fita, shi kuwa Jamil tsalle yayi tare da cewa. "Yesss, Dakta Allah ya kiyaye hanya, a wuni lfy a asibiti". Murmushi Ummi tayi tare da cewa. "Yi maza to ka ɗauki shi". To yace kana ya miƙe ya fita. Sanin cewa yanzu Sheykh yana sashin Hajia Mama ne. Haka yasa ya rigashi fita. Ummi kuwa miƙewa tayi taje ta rufe ƙofar sabida bata son wani yazo ya shigo. Kiran Jamil tayi a waya tace in sun isoma ya kirata a wayane zata buɗe mishi. Tana katse kiran ta juyo ta kalli Shatu dake zaune gefenta tana ce mata. "Yauwa to Ummi muje mu fara aikin kafin ya iso mun kusa cimma aikin." Cikin mamaki tace. "A a keda kikace sai an matsar da gadonshi sannan aikin tono ai bazamu iyaba. Dole sai mazan". Cikin muryar da har yau Ummi ta kasa banbance shi da asalin muryarta tace. "A a ba matsala Ummi muje zamu iya". Ta ƙarishe mgnar tana yin gaba, ganin hakane yasa Ummi Binta a baya. A hankali suka shiga falon. Tana mai cewa Ummi. "A nan ma an mishi wani aikin amman shi bai shiga jikinsa ba, sabida yanada Garkuwar addu'o'in da yakeyi yau da kullum. Shiyasa duk sabbin sihirurruka basa shigarsa. Sai dai waɗanda akayi mishi tun bai gama girma ba." To kawai Ummi ke ce mata sabida jin kamar muryarta na canza mata. A haka ta kuma nuna mata wani wurin. Tare da cewa. "Uhumm Ya Jafar suke nema, su maida majanunin kan bola sai kuma sharrinsu ya zame mishi al'khairi, Tsawon shekaru baya mgn sai ambaton Allah. Bashi ba zunibi sai tarin lada da yake samu na karatun al'ƙur'ani da ya zame mishi abokin hira. To ita kuma me take nema a duniya da zata cutar da baiwar Allah da ahlinta duka haka. In banda lalaci da son duniya na miji ya lalace da bin matsafa yana sawa ana sabauta ɗan uwanshi da yayanshi." Ita dai Ummi binta takeyi da ido da ƙafa har suka isa bedroom ɗin shi. Ɗan lungun da ɗaya Bedside drower'n take ta shiga. Kana ta kalli Ummi fuska a juye tace. "Naɗe min carpet ɗin nan. To Ummi tace da sauri ta fara naɗe carpet ɗin. Bayan ta janyeshi da kyar ne, ita kuma Shatu. A hankali tasa hannun damanta bisa jikin gadon ba tare da ta ɓallashi ba ko, ta cire wani abu a jikinshi ba, ta yunƙura ta tura gadon tare da cewa. "Bismillahirahamanirahim". Da sauri Ummi taja da baya cike da mamaki da tsoron ganin yadda take tura tamfatsetsen gadon mai ɗirkekiyar katifa da ko tura katifar kawai aikine. Guuuuuuh haka sautin tura gadon yake badawa. Saida ta turashi har jikin Waldurob. Kana ta tsaya a tsakiyar inda gadon yake kafin ta turashi. Dai-dai lokacin kiran Jamil ya shigo wayarta. Da sauri taje ta buɗe mushi. Kana suka shigo,. A falon suka bar Ɗalha mai tayis, kana Jamil ya amshi kayan aikin yabi bayan Ummi yana cewa. "Yauwa ɗalha ɗan jirani bari inzo mu isa kaga wurin". To ɗalha yace kana ya fara cin abincin da Ummi ta saka mishi. Suna shiga suka maida ƙofar falon suka rufe. A inda Ummi ta barta a han suka sameta. Da sauri ta miƙawa Jamil hannun tare da cewa. "Bani gudumar da ma'ɓamɓarin." Cikin sauri ya iso tare da ajiye ɗan buhun ya fito da gudumar da Maɓamɓarin yana mai mamakin yadda aka tura gadon yace. "Bari Aunty Shatu nuna min ina zan fasa". Da sauri tace a a, ku ɗan matsa gefe, musamman ma kai koma can". Ta nuna mishi gefe. Sake mata gudumar yayi jin ta fizgeshi. A hankali ya tashi sabida cewa da tayi ya tashi. Ido suka zuba mata, ita kuwa, gudumar tasa ta rinƙa buga tayis ɗin dake wurin saida ta fasa uku lafiyeyyu. Kana ta ture fasassun tasa maɓamɓari tana ɓalle sauran, saida ta ciresu kab. Sannan ta fara fasa fulon simintin dake ƙasan. Da mamaki Ummi ke kallon wurin sabida tasan babu wani fulo da akayi kafin asa tayis ɗin. Fasashi tayi kana ta fara caccaka ƙasan wurin da matonin, tanayi yana fito da ƙasa. Shiru sukayi ganin ramin yayi zurfi kuma ba komai. A haka taci gaba da tono tana kuma faɗaɗa ramin ta ƙasa. Wani irin zabura Jamil da Ummi sukayi lokacin da suka ga wani baƙin hayaƙi yana fitowa cikin ramin. Ita kuwa Shatu da sauri tasa hannun damanta taci gaba da tonon. Tare da yin mgna da sauri tace. "Jamilu buɗe windows da sauri hayaƙin nan ya fita". Cikin rawan jiki yace to. Kana ya fara buɗe wa da sauri sabida, hayaƙin ya fara cika ɗakin. Yana buɗe windows ɗin kuwa hayaƙin ya fara fita. Tonon taci gaba dayi tare da cewa. "Inama da akwai wani yardajjen mu a kusa, bayan ku biyun nan da yabi hayaƙin nan zaigane mana ina zai shiga cikin sashukan mutanen gidannan shaidar aiki ya koma kan wanda ya yishi." Da sauri Jamil yace. "To ko in fitane inbi hayaƙin". Cikin sauri tace. "A a kada ka fita ku tsaya kaida Ummi." Numfashi suka fara sauƙewa, a hankali lokacin da sukaga duk hayaƙin ya gama fita. Sai kuma suka fara takowa suna zuwa inda take ganin yadda hannunta dake cikin ramin yake karkarwa. Ga wata zufa dake keto mata kamar da bakin kwarya. Wani marfin tukunyar ƙasa ta ɗago. Kana a hankali ta ɗago tukunyar. Ta ajiyeta gefe kana ta koma ta jingina tana mai jan numfashin. Cikin sauri Ummi taje ta kunna sauran wutan ɗakin duka, ya zama kamar farin wata. Jamil ne ya fara leƙa cikin tukunyar. Da sauri yace. "Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ummi zo ki gani". Ya ƙarishe mgnar yana sunkuyowa da kai hannunshi zai kama tukunyar ƙasan cikin sauri da ƙarfi Shatu ta buge hannunshi da hannunta na hagu tare da cewa. "Jininka ɗaya da Yah Sheykh in ka taɓa duk abun zai iya dawowa jikinka." Ta ƙarishe mgnar da ɗago hannun ta na dama tasa a ciki. Tukunyar da sauri ta rumtse idanunta sabida wani irin masifeffen tsikara da taji an mata a hannunta. A can ƙasar Cameroon kuwa cikin Rugar Duno dake, kusa da Rugar Malam Babayo. Ba'ana ne zaune bisa buzun aikinshi. Da kasko a gabanshi yana kallon cikin kaskon gaba ɗaya jikinshi rawa yakeyi cikin tashin hankali da fargaba yace. "A'a A a Mata kada
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185